Sashe 28
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ganinsu rungume da juna ita da junaid, yasa ta saki murmushi, baƙaramin ƙaunar yaron take ji ba, ita kanta mamin saboda sunan yaron yaci Sunan marigayi mahaifinta Alhaji Junaid Shuwa, tun lokacin da mami ta auri Mahaifin Aneelerh Alhaji Muhammad falgore ta ƙwallafa rai akan ta samu ɗa namiji don ta sanya ma shi sunan mahaifinta, Allah bai nufa ba, ƴa ta samu mace kuma daga ita bata ƙara haihuwa ba, Aneelerh tasan da wannan burin na mahaifiyarta, shiyasa ta sanyawa yaron Suna Junaid, kuma aka amince mata da sunan, ko lokacin da su Uncle abdallah suka zo Nigeria don su ga jikan su, basu yi gaddama ba da aka faɗa masu sunan yaron, saima farin Ciki da su kayi An haifa masu ɗan kyakkyawan Saurayi.
Ƙarasawa gaban gadon tayi ta kira sunanta"Aneelerh wake up, lokacin yin breakfast ya yi, abie na son magana dake,"
BuÉ—e ido aneelerh tayi akan mami, biji biji take ganinta kafin idon ya washe,
"Mami," ta ambaci sunanta muryarta da alamun bacci,
"Muna jiran ki a dining area," mami ce ta yi maganar, tare da juyawa ta fuce daga É—akin,
A lalace Aneelerh ta miƙe ta sauko daga saman gadon, toilet ta nufe ta shige, bayan ta fito daga wankan, bata canza jallabiyar jikinta ba, mayafi kaɗai ta dauko cikin closet, tayi rolling ɗin shi a saman kanta,
Fitowa daga É—akin tayi ta nufi dining area, A saman dining chairs ta iske su zaune su biyu, sai Ana mai aikin gidan Aneelerh dake tsaye tana yin serving É—insu,
Tana ƙarasowa Ana ta soma gaishe da ita cikin girmamawa"good morning madam, how was ur night" murmushi Aneelerh ta sakar mata"Alhamdulillah, ina fata kema haka," jinjina mata kai ta yi alamar eh,
Mayar da idanuwanta tayi kan iyayen nata, gaba É—aya ita suke kallo, da sauri ta gaishe da su, su ka amsa mata fuskokin su a sake,
Kujera taja ta zauna, Ana tace" me zan zuba maki"?
"Cup of tea, ki haÉ—a mun da noodles," amsa mata tayi da toh, ta É—auki serving spoon da plate ta soma zuba mata noodles É—in, bayan ta gama haÉ—a mata ta tura mata gabanta, tare da kofin tea,
Har ta É—auki fork zata fara cin abincin ta É—ago ta saci kallon iyayen nata, da yake suna fuskantar juna,
Ganin suna kallonta yasa ta sunnar dakai ƙasa, murmushi su ka sakar mata, mami tace" Ina kika baro mana baby junaid ɗin mu"?
"Bacci yake yi,"
"Ya cika bacci anya kuwa lafiya"?
Abie yace"lafiyar ce ta kawo haka ae, yaron fa É—an hutu ne, " da zolaya ya yi maganar, murmushin gefen fuska aneelerh tasaki"mami ae ya farka É—azu, daga baya ne ya koma bacci" mami tace"Okey, ki ci abincin ki, yana huce wa" kallon abie ta yi tare da cewa"abie da gaske ne uncel abdallah ya kira akan zasu kar6i baby junaid"? yanayin yadda tayi maganar a É—an tsorace take da jin amsar da zai bata,
"Dagaske na, Amma ki kwantar da
hankalin ki, bawan da zai raba ki da babynki, mutu ka raba takalmin kaza" dariyar farin ciki ta saki, hatta Ana dake a tsaye saida ta murmusa,
"Ci ki ƙoshi daughter, farin cikinki ae shi ne namu," yakai karshen maganar tare da kallon Ana dake a tsaye"Nayi magana da drivern da zai kai ki garin ku, ki kasance a cikin shiri a kowani lokaci zai iya zuwa ku tafi" jin wannan maganar yasa yanayin fuskarta ya canza ta shiga yarfa hannu, cike da mamaki suke kallonta, tattara skirt ɗin jikinta tayi tare da zuƙunnawa saman guiwowinta, tana faɗin
"Allaji ayi haƙuri abarni anan tunda har nakai wannan lokacin, wlh kona koma ƙauyanmu wahala zanci, Noman doya za'a sanya ni, dan Allah Alaji a taimaka, ƴan uwana duk suna a cikin garin nan suna aiki, dama mu uku ne marayu iyayen mu sun rasu," tuni hawaye sun wanke fuskarta, kallon aneelerh tayi a marairaice tace"madan ki taimaka, abarni anan wlh noman doya da wahala", duk wannan ƙibar da nayi idan har na kuskura na koma ƙauyan mu, Cikin kwana uku zan sace," mami dai dariya ce ke son kufce mata, amma ta gumtse ta cikin baki, shi kanshi abie taso ta ba shi dariya, musamman hausarta da bata fita sosai,
"Abie, tunda tana taimaka ma Inna hauwa wurin yin girki, da aikace aikacen gida ni ina ganin barta kawai,"
Mami ma tace"Nima na goyi bayan haka, saboda ta nuna bata son noman doya....."takai ƙarshen maganar tana ƴar dariya,
"Yanzu ina Æ´an uwan naki"? Abie ne yae mata tambatar,
Hannu tasa tana matse ƙwallar dake akan fuskarta,
"Esther tana aiki a restaurant itace take aiki gidan Iyayen Sir uzair, Tun bayan barin su ƙasar ta koma restaurant da aiki, ita kuma janet, tun lokacin da madam Benazir ta koreta, ta samu aiki a hotel,"
Ajiyar zuciya abie ya sauke, kafin yace"Shikenan zaki zauna anan, amma fa zan sa maki ido, duk ranar da kika aikata badaidai ba, zan turo ki ƙauyan ku, aje can ayi noman doya,"
Gaba ɗaya suka saki dariya, miƙewa tayi muryar na rawa ta shiga faɗin"thank u sir, thank u madam ngde ngde," tsantsar farin ciki ne akan fuskarta,
"Ki koma wurin Inna hauwa, ku yi breakfast É—in ku," mami ce ta yi mata maganar, da sauri ta juya ta nufi part É—insu,
A tsanake suka cigaba da yin breakfast É—insu, sai da suka kusa kammalawa, aneelerh ta mike mami tace ina zuwa,
"Inaji araina kamar Junaid ya farka, bari naje na duba shi," da sauri ta wuce É—akinta,
Kallon Juna abie da mami su kayi,
"Namanta ban faÉ—a maki ba, Munyi waya da É—an Iya, wai yana so Aneelerh ta koma hannun shi da zama, Zai sama mata aiki a Asibitin *CHIEF OBINNA* " rass Mami taji gabanta ya faÉ—i, can kuma ta É—an saki murmushi,
"Ka daina yarda da maganar ɗan Iya, kasan halin shi, Ya iya shirga ƙarya in banda abunka taya za'ae ya iya sama mata aiki A wannan katafaren asibitin wanda ma'aikatan cikinsa ma fa, ɗai ɗai ku ne ƴan ƙasar nan, amma fa in ta samu aiki acan zan fi kowa mafarin ciki, don naji ance ƙaramin ma'aikaci na asibitin just cleaner kawai albashin shi yakai Dubu ɗari da hamsin,
Abie yace"nima nayi mamaki da yace haka amma kuma kinsan shi, mutunne na jama'a, duk wani politician daya shahara yasan shi, to ba abun mamaki bane don yace zai iya sama mata aiki acan, Ni abunda yasa ma na yi mata sha'awarar zama can abujan, zata fi samun kwanciya hankali akan nan, yau fa tsawon shekara biyu da watanni, rabon aneelerh da taje aiki, badan Dr Aisha ta kar6i ragamar kula da asibitin ba, da yanzu komai ya durƙushe"
Shiru mami tayi na wani lokaci, aranta ta ayyana cewa in kuwa har Aneelerh ta samu aiki a asibitin *CHIEF OBINNA* tabbas cikin ƙankanin Lokaci zata zama hamshaƙiyar mai kuɗi, kuma zata ji daɗin rayuwa agidan ɗan Iya, saboda barkwancin shi dana matar shi, ƴan sharholiya ne ana shan drama a gidansu, sai dai kafin Ashawo kan Aneeelerh ta zauna acan ɗin shine abu mai wuya, kuma suma kansu baza su so tayi nesa da su ba, duk da shima abie Suna hasashen zai samu ƙarin matsayi a wurin aikin shi, nan badajimawa ba za'ayi mashi transfer zuwa Ministry of finance dake abuja,
Sun jima suna tattaunawa da abie kafin Yayi mata sallama, Ya tafi zuwa wurin aikin shi, ita kuma Mami ta koma falo, a lokacin aneelerh ta dawo falon hannunta É—auke da juanid, fira suka zauna sunayi yayin da plasma tv ke a kunne suna kallon tashar arewa 24,
*To fa😳Su Angel An yi gudun gara An faɗo gidan zago, ko ina ne Wurin nan? Lamarin ya ɗaure mun kaina, To dai mu haɗu a next page gobe in Allah yakainu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya, kada ku manta friday da weekend ba posting, Amma zanyi ƙoƙari in dinga yi maku Long pages, Ga waɗan da suka shirya yin payment ƙopa a buɗe take su yi mun magana (08103884440)**💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
*Boss Bature âœï¸*
dedicated to Aunty kubraâ¤
*E10*
_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faÉ—akarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaÉ—antarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba.âœï¸_
GargarÉ—i
_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube don already na siyar da littafin, Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_
*South Korea*
Seoul City-Gangnam-Gu
Hamshaƙiyar Unguwace ta Attajiran masu kuɗi dake zaune a Seoul, Babban birnin korea ta kudu, babban birni ne mai manyan-manyan gine-ginen gargajiya dana zama ni masu matuƙar ƙayatarwa, ga manyan hanyoyin jiragen karkashin kasa da kuma Wuraren shaƙatawa, masu matuƙar jan hankali, A ɗaya daga Cikin jerin Modern apartments din dake a Gangnam-Gu Haɗaɗɗen masaukin Uncle abdallah ya ke, inda suke sauka duk in suka zo ƙasar.