Sashe 177
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sauran tambayoyin da kikayi mini bazan iya amsa maki ba saboda babu isasshen lokaci, zasu iya riskar mu, Abu ɗaya da nake so kiyi mini alƙawari shine kiyi ƙoƙarin ganin kinbi duk wasu sharuɗɗa da zan faɗa maki don ku tsira daga Cikin kurkukun nan, Mun ɗaura buri akan ki Unaiserh, saboda ta hanyarki ne kaɗai zaki iya tona asirin matsafan da ke ruƙe da kurkukun ƙaddara! Muna so duniya tasan da zaman su, A san me ake aikatawa a gidan kurkukun, yin hakan da zakiyi shi zai janyo hankalin mutanan duniya daga nan za'a samu waɗanda zasu Iya kawo masu farmaki, Inaso ki ɗaurawa kan ki nauyin yin hakan ko dan saboda rayukan dake rayuwa acikin kurkukun nan cikin mawuyacin hali! Akwai ire iren ku da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba, An kulle su an hanasu sakat, Kullum ne sai an rasa rayuka agidan kurkukun nan, kashe mutane suke yi tamkar kyankyasai, Idan har bamu kawo ƙarshen kurkukun nan ba to kuwa zasu cigaba da aikata 6arnar da babu ranar dainawa, Muna matuƙar jin tausayin yaran da ke rayuwa a kurkukun nan, Dan Allah Unaiserh ki taimaki rayuwar su! Ki daure ki jure wurin ganin kun tona asirin abun da ake aikata......" hannayenta Ya ruƙo a cikin nashi ya dinga yi mata magiya sautin muryar shi kamar zai fashe da kuka, Ga dukkan alamu sun gaji da ganin Zaluncin da ake aikatawa agidan kurkukun ƙaddara
Tun tana yin kuka har muryarta ta disashe da ƙyar ta samu ta tsagaita tana kallon shi tace "NAYI MAKA ALƘAWARI Idan Allah ya bani damar fita daga kurkukun nan zan tona asirin su harma mu bada gudunmawa wurin ganin an kawo ƙarshen su, Bi'iznillahi,
Ajiyar zuciya ya shiga saukewa kafin ya daidaita natsuwar shi yaci gaba da cewa "Silar sabunta ginin da aka yi ƙofar ta 6ace mana, amma muna hasashen tana a cikin ɗaya daga cikin waɗannan makewayin naku guda uku, akwai wata tukunyar fulawa da ke ajiye Cikin toilet ɗinku Mahafiyata ce ta ajiyeta saboda bayan an sabunta ginin shafen dake a ƙasan wurin bai zauna da kyau ba, kuma bakomai ya jawo hakan ba face silar zaman da mahaifina yayi awurin na tsawon kwana biyu yana ibada, to duk wani abu da ke da sihiri idan ya ta6a wurin bazai zauna ba sai ya nuna alama, gudun kada ta manta da ƙofar yasa ta ajiye wannan tukunyar fulawar, Idan kuna so shafen dake akan ƙopar Ya 6a66ako batare da kun sha wahala ba, Ku yi amfani da ruwan zafin da ake kawo maku a matsayin ruwan shan ku, da zarar kun yayyafa shi asaman wurin zai tsastsage daga nan ƙofar zata bayyana, amma fa sai kun yi takatsantsan, kada farin cikin ganin ƙopar yasa ku fasa ihu wanda zai janyo hankalin su........."
Wani irin Farin ciki ne ya lullu6e Angel, Bakinta yaƙi rufuwa
"Kada ku sanyawa ranku cewa dukkan ku zaku tsira, ba abune mai sauƙi ba, dole ku fuskanci tarin ƙalubale wurin ku6uta, musamman Makullin nan ɗaya da baya a cikin ku wato Danish dole ku dawo da shi saboda shi kaɗai ne zai Iya Cire murfin ƙarfen da ke a jikin ƙofar cikin sauƙi ba tare da kun sha wahala ba.
Cikin shessheƙar kuka tace"Taya zamu iya gano Danish har mu iya dawo dashi Cikin hayyacin shi"? bai amsa mata tambayar ta ba, ganin ya miƙe tsaye yasa itama ta miƙe tana kallon shi,
"Akwai ruwan zam zam da mahaifina yake yawo dashi cikin aljihun rigar shi, ya mallake shine a wurin wani hamshaƙin malamin addini wanda ake kira da Shaykh al-ikhlass ɗan ƙasar Madina, shi ya yi mashi kyautar jarkar ruwan zam zam ɗin duk mutumin da ya kur6i ruwan abakin shi ya haɗiya to zaiyi wuya Sihiri yayi tasiri a jikin shi, sannan waraka ne ga kowace irin lalura da izinin ubangiji, Dubarar da mahaifina yayi sai ya dinga ɗibar ruwan xam xam din yana ɗura shi cikin ƙananun robobi, duk in zai fita a cikin aljihun shi yake ɗauka ya tura, saboda tsaro baisan ko Allah zai haɗa shi da mai buƙatar taimakon wata lalura dake damun shi, shiyasa Yake yawo da robobin ruwan cikin aljihun shi, to aranar da matsafa suka farmake mu tsakar dare suka kawo mu kurkukun nan akwai kingin roba ɗaya da ta rage a cikin aljihun jallabiyar shi, Kafin ya rasu ya damƙa ma mahaifiyata ita mun 6oyeta wurin da babu wanda ya sani daga ita sai ni, Robar ruwan zam zam ɗin tana a cikin ɗakinta inda ku ke rayuwa, da zarar kun dafa jikin bangon ƙofar zata buɗe da kanta, Sai ku shiga ku ɗauko ta.
Ke za ki nemo Danish a gidan kurkukun nan saboda ke kaɗaice zaki iya sarrafa tunanin shi amma fa sai kinci baƙar wahala domin kuwa baisan wacece ke ba a yanzu, Har kashe ki zai Iya yi, komai zai iya aikata maki, duk runtsi duk wuya karki bari tsoron shi yasa ki kasa watsa mashi ruwan a cikin bakin shi, ki tabbatar ya haɗiye shi.
Sannan Giant basa jin Bugu, Wuƙa bata iya tsaga jikinsu, haka zalika harsashin bindiga bai iya tsaga fatar su, Mutane ne masu hatsarin gaske, ƙarfin shaiɗanun aljanun da ke a jikin su ya rinjayi halittar su ta ɗan adam, Giant's heart ba irin zuciyar mutun bace, ta shaiɗanin aljani ce, Ko da ace kinyi nasarar sanya mashi ruwan abakin shi zai dawo hayyacin shi na ɗan lokaci ƙanƙani amma duk lokacin da Giant's heart ɗin shi ta motsa zaku ci baƙar wahala, Shiyasa ni ke so ki dage dayi mashi addu'a saboda ku samu ya fitar daku daga Cikin kurkukun nan, In yaso daga baya idan kuka faɗa cikin mutane zan baki Address ɗin gidan mu da mahaifiyata ta rubutamin don in baki, idan ku ka duba zaku iya samun sauran robobin ruwan zamzam na mahaifina daya ajiye a ƙarƙashin gadon shi, da shi zaku dinga yin amfani wurin shawo kan Danish a duk lokacin da Giant's heart ɗinshi ta motsa. Ki kula da rayuwar shi Angel Ki ɗauka cewa amanar Danish na baki, ki ruƙe mini shi hannu bibbiyu, kada ki kuskura ki bari yayi nesa dake, ku kasance atare domin mu samu muyi nasara agidan kurkukun nan, Danish yasan komai fiye da tunanin ki, mun riga shi zuwa kurkukun nan amma yafi mu sanin komai, shi kaɗai yasan hanyar da za'a iya ruguza su, Matsalar shi ɗaya mugun miskili ne kuma yana da taurin kai, zaku ci wahala kafin ku samu Ya baku haɗin kai.........." Yana kai ƙarshen maganar shi da sauri ya zura hannu cikin ajihun baƙin wandon dake ajikin shi ya zaro takardar dake a ninke ya miƙa mata, Address din gidanmu ne dake a Kaduna state, Daga yau ba zaki sake gani na ba, duk wani taimako daya dace inyi maku na riga nayi, yanzu saura ku ya rage ku fara naku, Zamu jira har zuwa lokacin da zaku dawo mana da kyakkyawan sakamako, Sai dai bamu da tabbacin zamu kai lokacin a raye nida mahaifiyata ko kuwa....." bai ƙarasa Maganar ba Angel ta faɗa jikin shi ta rungume shi sosai ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hannayen shi biyu ya ɗaura a saman bayanta ya ƙanƙame ta sosai tamkar ƴar cikin shi, Sun ɗauki tsawon lokaci rungume da juna, kafin daga bisani taji kanta ya fara sara mata, nan ta ke idanuwan ta suka lumshe bacci mai nauyi yai awon gaba da ita.........
â¤PRISONERSâ¤
Tsawon lokaci da su Batul su ke ta faman bubbuga ƙofar toilet, Angel tana aciki tana bacci kanta jingine da bango, Salsabeel ne Ya dawo da ita tun da jimawa, tasha uban baccin ta hankalinta akwance yayin da ƴan uwanta su ka shiga matsananciyar damuwa na rashinta.
Ba ta tashi farkawa ba, Sai da dare Ya tsala Lokacin Sun yi nisa acikin baccin su, A hankali ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta, Yayin da la66anta ke ambaton Sunan Allah, Wata irin kasala ta ke ji a jikinta sam babu kuzari, duk yinin yau bata ci abinci ba, Ko ruwa bai gifta maƙoshinta, azababbiyar yunwa ce ta addabe ta, daƙyar ta samu ta yunƙura ta miƙe tsaye Tana ƙarewa toilet ɗin nasu kallo, kamar ranar ta fara ganin shi, Hasken filitar da su ka ajiye acikin shi ce ta gaure ko'ina, Bakomai ne ya faɗo mata acikin ranta ba, Fa ce maganganun da Salsabeel Ya faɗa mata, tamkar a mafarki ta ke tariyo komai da ya faru a tsakanin su, kwokwanto ta soma yi a cikin zuciyarta Anya da gaske ne Haɗuwar su da shi? Gani ta ke yi kamar haduwarta mafarki ce, da sauri ta juya tare da ɗaura kyawawan idanuwanta kan tukunyar fulawar nan da ke ajiye saman floor, Walking slowly ta nufi tukunyar, zuƙunnawa ta yi agabanta idanuwanta akan furen Danish, A tsanake ta ke tariyo duk wani abu da Salsabeel Ya faɗa mata dangane da shi, ba za ta Iya misalta irin ƙaunarshi da ta ke ji ba, Taji takaicin mayar dashi Giant da su ka Yi, zuciyarta ba ƙaramin tafarfasa ta ke yi ba duk in ta tuna cewa yanzu Danish ɗinta Giant ne mai haɗarin gaske, Tayaya zata Iya tunkarar shi? Ba tare da ta samu matsala ba, ' runtse idanuwanta tayi sosai hawaye na cigaba da wanke fuskarta, idanuwanta sun canza launin, ciwon kanta ya tsananta sosai.
"GENIE!" Ras ta ji gabanta Ya faɗi jin muryar Jamimah, A hanzarce ta miƙe tare da sanya tafin hannunta ta share hawayen da ke tsastsafo mata saman kuncin ta, sai da ta fara zuwa gaban Fanfo ta wanke fuskarta sosai, har ta nufi ƙofa zata buɗe sai kuma ta fasa tunawa da Uniform ɗin Jamimah da bata wanke mata ba, kamar yarda tabar su saman Igiyar shanya haka tayi tozali da su, Matsawa tayi gaban Igiyar ta janyo uniform ɗin, kafin ta zame jam lock ɗin da ke a jikin ƙofar, zuciyarta acike fal da tunanin amsar da zata basu idan suka tambayeta Ina taje?