← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 179

Sashe 70

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauri ta kalli fuskar mutumin, ya sanya Mask a fuskarshi, Baƙaƙen kaya ne ajikinshi, bakomai ya faɗo mata araiba face mutumin da ya Ɗauke mata baby junaid ɗinta lokacin da taje gidanta, nan take gabanta yyi mugun bugu, A tsananin tsorace ta shiga kiciniyar zuge glass ɗin motar, ganin zata datse mashi hannu yasashi yin saurin zame hannunshi

Key tayi ma motan hannunta na kerma ta ruƙe steering da wani irin speed ta fusgi motar da gudu ta haura saman titi tana ambaton"La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" tarasa ina zata dosa, saboda tsabar ruɗi, Gani take kamar mutumin yana abiye da ita, ashe dama bibiyar rayuwarta yake yi? Tayi tambayar acikin zuciyarta, Marece ne sosai Tana kokarin shan kwana, muryarshi ta ratsa kunnata"Baki bani sadakar ba" a gigice taja burki ta tsayar da motar, idanuwanta azazzare ta ɗago tana kallon shi ta cikin Rear view mirror ɗin motar,

Mutumin Yana a zaune Cikin back seat na motar, a hakimce,

Tayi matuƙar razana ganin shi acikin motarta, taya akai ya shigo bayan ta rufe motar, Anya kuwa mutunne ba aljani ba? muryarta na rawa tace"dan..dan Allah na roƙe ka, kada ka cutar damu, bansan wanene kai ba, ban kuma san laifin da nayi maka ba, ka faɗi kome kake so zanyi maka shi" idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,

"Kome nake so zaki yi mini"? Ya yi tambayar yana kallonta, a tsorace tace"Eh, wlh zanyi"

Ya amsa da "Okey, " hannu taga ya zura cikin aljihun wandon Jikin shi ya lalubo wayarshi, Ya ɗan daddana ta kafin ya miƙa mata wayar"Location ɗin nan zaki bi, " batare da musu ba ta kar6i wayar tashi, idonta akan google map ɗin daya buɗo mata, daga gefenta ta ɗaura wayar, Ta ci gaba da driving tana bin location ɗin, yayin da zufa ke tsastsafo mata, zuciyarta a firgice take da tsoron inda zai kai su, Wayar shi kanta abun tsoro ce saboda ta banbanta da sauran wayoyin da ta saba gani, Babu sunan Company ajikin wayar,

Dogon titi suka Miƙa sham6al har zuwa cikin wata area, Ta jigunannun masu kuɗi, Manya manyan gine gine, Unguwar shiru babu yawaitar mutane acikinta, a bakin wani katafaren Gida ta ƙaraso da motar, yace tayi horn ta danna horn nan take Wagegen gate ɗin gidan Ya zuge awani slow, kutsa motar tayi acikin gidan, har saida ya bata umarnin ta tsayar da motar tukunna ta tsaidata,

BuÉ—e murfin motar yayi tare da fitowa ya zagaya other side É—in da junaid yake a kwance, Ya buÉ—e motar ya zura hannu ya É—auke shi, AruÉ—e aneelerh take kallon shi, ganin ya É—aukar mata yaro,

"Let's go in" yayi maganar yana nuna mata hanyar zuwa cikin gidan, Jiki asanyaye ta buɗe motar ta fito tabi bayanshi, Wa'iya zubilla Ta yi matuƙar girgiza da ganin kyawun gidan ya tsaru iya tsaruwa kai kace ba'a 9ja yake ba, Duk da a tsorace take hakan bai hanata bin ko'ina da kallo ba, suna ƙarasowa bakin glass door ta falon gidan, Muryar na'ura ta karaɗe kunnuwansu, wani abun mamaki daya ɗaure mata kai, na'urar da ta soma magana tana sanar da zuwan su, sai da ta faɗi Cikakken sunan aneelerh, wato Aneelerh muhammad falgore, Ras taji gabanta ya faɗi, a karshe na'urar tace"you're permitted to come in" nan take ƙopar glass ɗin ta zuge,

Mutumin yace mata su shiga Ciki, ta zura kafarta acikin katafaren falon, Tsayawa faÉ—ar irin kyawunshi 6ata baki ne sai wanda ya gani, wani irin sanyin a.c ne ta ko'ina, Komai na Cikin falon White Colour ne atsaftace yadda kasan ba'a ta6a amfani dashi ba, saboda kyawunshi da sabuntakar furniture É—in dake acikin shi,

Miƙa mata Junaid Ya yi, da sauri ta sanya hannu ta kar6eshi, ta rungume shi ajikinta, A saman Sofa 3 seater Ya bata Umarnin ta zauna, xama tayi tana faman baza ido, Jira take taga me za ayi mata, Acikin zuciyarta sai addu'o'in neman tsari take karantowa,

Takun takalma ta soma ji daga can saman twin stairs ɗin dake a falon, a hanzarce takai idanuwanta wurin tana kallonsu, waro ido waje tayi Jikinta ya shiga 6ari ganin Gabza gabzan Mazan dake saukowa saman benan, kowannansu na asanye Cikin shiga ta baƙaƙen kaya, A ƙalla sunkai su takwas, bakwai Suna a left hand na benan, Yayin da mutun ɗaya ke tafiya atsanake ta right hand ɗin stairs ɗin

Kusan atare suka sauko daga saman benan, Aneelerh bata Iya ganin komai na Jikinsu ba, Gaba ɗaya sun rufe kansu daga ƙasa har sama Cikin black dress, Dogayen riguna na maza masu haɗe da huluna kamar alkebba, Guda bakwai ɗin suka Ƙame a tsaye tare da goya hannayensu saman ƙirjinsu, shima wanda ya kawota gidan Yana a tsaye gefen hand sofa ɗin da take a zaune Ya ƙame kamar yadda sauran su ka yi

Mutum ɗayan nan daya rage, shine Ya zauna saman sofa 2 seater, Ya ɗaura ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya, aneelerh fa tasha jinin jikinta, sai faman ƙanƙame junaid ta ke yi ajikinta, Yaro sai bacci yake yi baisan halin da Mommynsa ke ciki ba,

"Ki natsu Ki saurari maganganun da zamu tattauna dake, mintina ƙalilan zamu salleme ki ki tafi" Na gefenta ne yayi maganar, wanda suka zo tare da shi,

Jin haka yasa ta daidaita natsuwarta, ta kasa kunne tana jiran Jin me zasu Ce, wanda take tunanin shine team leader ɗinsu, wanda ke zaune saman Sofa 2 seater akanshi ta tsayar da idanuwanta, wata irin ƙirar ƙarfi ce gare shi, taban al'ajabi, mai matuƙar jan hankali da tsoratarwa, kai daga ganin wannan babu wasa acikin lamuranshi, baƙaƙen kayan sun zauna mashi sosai, sun bayyanar da zazzafar surarshi, tayi tunanin shi zai yi mata magana amma sai taji yayi shiru,

Takun tafiya ta kuma jiyowa ta can 6angaren, Wani ƙaton ne Ya fito sanye da bakaken Kaya, Hannunshi a ruƙe da plate me ɗauke da Glass Cup, ruwan sanyi ne aciki, a saman table ɗin dake a kusa da sofa ɗin da aneelerh ke a zaune ya ɗaura plate ɗin, Cikin girmamawa yace mata"Zata iya sha" ya ambaci hakan tare da juyawa Ya bar falon, duk fa waɗannan Garadan mazan na a kewaye da ita, Da farko taji tsoron tasha kada ace An sanya mata wani abu, amma daga baya saita kai hannu ta ɗauka ta ɗan kur6i ruwan, sanyi gare shi ga daɗi, bayan ta ajiye Glass ɗin, Sai ga wannan katon daya kawo mata ruwa, Ya dawo Cikin falon hannunshi ruƙe da Laptop Tsadaddan gaske, Adai dai gaban aneelerh Ya ajiye laptop ɗin saman table gefen plate ɗin da ya kawo mata ruwa,

Daddana laptop ɗin Ya shiga yi Cikin ƙwarewa, Aneeelrh dai ta zuba ido tana jiran ganin me za'a nuna mata,

Bakomai bane Ya bayyana akan screen ɗin Laptop ɗin nasu, Face Hotonsu da su kayi ranar birthday ɗin Angel, Su Huɗu, Angel ce a tsakiyarsu, Taj yana agefenta ya zuƙunna, Aneelerh da Uzair Suna atsaye fuskokinsu ɗauke da murmushi,

Tsananin mamaki ne ya kama Aneelerh ganin wannan hoton, duk da tasan Zasu Iya samun shi a social media, saboda sunyi share É—inshi a insta da Facebook, twitter da tiktok, hada videos na birthday É—in angel,

"Kin gane su"? Muryar mutumin ce ta katse mata tunaninta, da sauri tace"Eh, ƴan uwana ne," ya nemi ta yi masu bayanin menene alaƙarta da su" da hannu ta nuna mashi hotonta dana uzair tace mijina ne, wannan kuma ɗan uncle ɗin shi ne, Sunan shi Tajuddeen, Ita kuma yarinyar Ɗiyarshi ce, sunanta Unaisa amma muna kiranta da Angel,'

Jinjina kai ya yi tare da cewa"Mu jami'ae ne masu zaman kansu, muna da interest akan case É—in 6acewarsu, that's the reason why muke Bibiyarki, saboda sanin cewa ke kaÉ—aice zaki Iya bamu bayanan da muke so, Zamuyi maki tambayoyi, da zarar kin amsa mana zamu sallame ki ki tafi, kuma bazaki sake ganin mu ba," ta amsa ma shi da toh,

Tambayoyi suka shiga yi mata, tun daga kan alaƙar dake tsakanin su tajuddeen da Uncle abdallah har izuwa kan Alhaji ubaid, da ita kanta hada iyayenta duka saida su ka yi mata tambayoyi a dangane dasu, hatta Benazir sai da suka yi mata tambayoyi akanta, duk ta amsa masu wanda ta sani, abunda ya ɗaure mata kai hada ƙawarta Aisha suka Yi mata tambayoyi akanta, game da yarda akai mahaifinta yayi mata korar kare daga gidan shi, Lamarin ya ɗaure ma aneelerh kai, taya akai suka san kowa da take atare da shi? Su wanene waɗannan jami'an masu Uniform baƙaƙen Kaya, Taso ta tambayesu daga ina suke, amma sai suka ce mata, basu bata iznin tambayar komai agame dasu ba, Sannan suka ce ta sawa ranta cewa a mafarkine Ta haɗu dasu, kada tayi tunaninsu kuma kada ta kuskura ta yi gigin faɗa ma wani agame da su,
Chapter 70 · 0% Book details