Sashe 22
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuba masu ido aneelerh tayi tana kallonsu batare da kiftawa ba, tasan aikin mahaifinta ne, mutunne mai É—aukar abu da mahimmanci babu wasa a lamarinshi, Sam ba ta yi tsammanin zai yi report din case din wurin Æ´an sanda ba, Sai gashi É—ungurugum ya taho dasu Gidan,
Ganin ta yi tsaye tana kallonsu yasa Shi yi mata gyaran murya yace"Daughter Kece kika koma haka"? jin haka yasa ta nufe shi da sauri, tunkafin ta ƙaraso ya buɗe mata hannayen shi ta faɗa a kirjin shi, ta fashe ma shi da kuka, duk jikinsu yayi sanyi, Hannu yasa yana shafa bayanta cikin sigar lallashi, kafin ya kalli uncle din nata yace dashi Bismillah su zauna"wuri suka samu kowa ya zauna saman sofa, Bayan ya raba jikinshi daga na aneelerh yace itama ta zauna, atare dashi suka zauna,
Uncle Bash ƙusa yace"Aneelerh Why tun daren jiya daya fita baki sanar damu ba"?
Cikin shessheƙar tace"Ae nayi tunanin zai dawo kafin da safe"
Jinjina kai yayi"okey, yanzu ki natsu ki faÉ—a mana taya akai yabar gidan without your knowledge"?
Ƙoƙarin buɗe baki tayi donta kora masu jawabi kamar yadda suka buƙata, nan take Wani irin yunƙurin amai yazo mata, da sauri ta miƙe daga saman sofa din ta watsa aguje zuwa bedroom ɗinta,
Dco ya kalli Ramlat Jami'ar binciken da suka zo da ita yace da ita tabi bayan aneelerh, amsa mashi tayi da Okey sir, Kafin ta miƙe ta bi bayan aneelerh cikin bedroom ɗinta,
Tana shiga tajiyo Sautin ƙaƙarin aman da aneelerh keyi acikin toilet, kaitsaye ta taka izuwa cikin toilet ɗin, Agaban Sink ta samu aneelerh tana ta kwara amai tamkar ƴar hanjin cikinta zasu fito waje,
Ƙarasawa tayi har zuwa bayanta, ta sanya hannunta tana ɗan bubbuga bayanta, Tana yi mata sannu,
Bayan ta kammala yin aman, Ramlat ta kunna mata fanfo, ta wanke bakinta tass, Takai hannu jikin tissue holder ta yago kaɗan ta miƙa ma aneelerh ta goge mouth ɗinta, daga haka ta ruƙo hannunta suka fito daga Cikin toilet ɗinta
"Sorry dear ki kwantar da hankalinki, in sha Allah we will try our very best wurin ganin mun gano inda mijinki ya ke,"acewar Jami'ar binciken,
Aneelerh dake ta faman fitar da numfashi mai É—umi tace"Bana jin daÉ—in jikina, tun jiya banci komai ba, kuma bana jin zan iya cin wani abu,"
Ramlat tace"Ki daure kici, lafiyar ki muke buƙata, domin kuwa idan ba lafiya atare dake taya zamu iya samun haɗin kanki wurin yin investigation ɗinmu"?
Takai ƙarshen maganar a lokacin sun dawo Cikin falon, Hankalin Dco da na sauran jami'an ya dawo kansu, mahaifinta kuwa jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba, ganin yadda ɗiyar shi ta rame, tamkar ba neelerh ɗinsa ba,
A gefen abie ta zauna tare da kwantar da kanta saman kafaÉ—ar shi, Ramlat Ta kalli dco tace"Sir, bata da koshin lpy, kuma ta sanar dani cewa tun jiya bata Ci komai ba,"
Uncle bash yace"Idan har bata ci abinci ba, ba zamu iya samun bayanan da muke bukata ba awurinta," Yayi maganar eyes dinshi akan Abie, kafin ya mayar dasu kan Ramlat yace"ki duba frigde nasan baza a rasa abunsha ba, Ki É—auko mata tare da ruwa me sanyi"Amsa mashi tayi"okey sir" kafin ta juya ta nufi fridge É—in dake A falon"
Hanmu tasa ta buɗe frigde din, Lemuka ne a jere masu sanyi, hada fura da youghurt, fresh milk ta dauko mata tare da ruwa"ta ruƙo bottles din a hannunta ta dawo ta ɗaura su asaman C table din dake agaban sofa din da aneelerh take,
Uncle bash yace"Aneelerh ta shi kisha,"batare da musu ba, Aneelerh ta mike zaune, Takai hannu ta É—auki milk É—in ta buÉ—e ta kwafa abakinta, ta shiga É—aÉ—É—akarta, makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat!!
Abie yace"Ki sha a hankali, kada ki shaƙe" janye bottle din tayi daga bakinta tana faman sauke ajiyar zuciya, lallai ba ƙaramar yunwa take ji ba, bayan ta ajiye milk din Abie ya dauki bottle water me sanyi ya mika mata, hannunta na kerma ta buɗe mufin ta kwafa abakinta, A hankali take shan ruwan harta kammala, Sai gashi ta ɗan samu natsuwa,
Uncle bash yace"Aneelerh kiyi mana bayanin yadda komai ya faru a daren jiya, muna sauraronki"
Ganin yadda zufa ke keto mata, abie yace ta cire hijabinta"hannu tasa ta É—ebe hijabin, dama akwai Kallabin data É—aure kanta da shi,
A tsanake ta soma Yi masu Bayani tiryan tiryan
"Ji wuraren ƙarfe tara, nafarka ban samu uzair a saman gado ba, nayi tsammanin ko ya shiga toilet ne amma ko da na duba baya a ciki, na yanke shawarar zuwa na tambayi megadi,koda naje wurinshi yace mun Yaga lokacin da Uzair ya fita acikin motarshi, kuma har magana sunyi da shi kafin tafiyar shi, koda jin haka na dawo cikin gida na ɗauki wayata na kira layin uzair tana ringing amma uzair bai ɗaga ba, a ruɗe na ajiye wayar na fito na nufi gidan taj, ina zuwa na shiga gidan, A falo nayi mashi sallama, ya fito daga ɗakin shi, harma yayi shirin kwaciya, nake faɗa mashi Game da tafiyar uzair ƙarfe 9 na dare na farka banganshi ba, Nayi tunanin ko ya kirashi awaya, saboda kusancinsu dana sani, Uzair zai iya 6oye mun abun amma bazai iya 6oyema Taj ba, Shiyasa na tambaye shi,A wannan lokacin taj yace na jirashi ,Zaije room dinshi ya kira shi awaya, na tsaya ina jiranshi, koda ya dawo na tambaye shi ya kirashi,yace mun in kwantar da hankalina duk inda yake ayanzu yasan yana akan hanyar dawowa ne, ba don na yadda da kalamanshi ba, na dawo gida zuciyata duk a harmutse na kwanta, Ko a daren sai da taj ya kira layina, ya ƙara kwantar mun da hankalina, a wannan yanayin bacci yayi awon gaba dani,
Shiru ta ɗanyi tana mayar da numfashi, kafin taci gaba da cewa"da safe na farka wuraren ƙarfe tara, still uzair bai dawo ba, Nan ma hankalina ya ƙara tashi, Na yanke shawarar zuwa Wurin taj don inji idan sunyi waya da uzair, koda ace ya kirashi tsakar daren jiya, Ina fita daga gida na nufi gidan taj, tunkafin ma naƙarasa naga baba maigadin gidan atsaye ya jingina bayanshi jikin Gate din gidan fuskarshi da alamun damuwa atattare da ita..............."Komai daya faru saida aneelerh ta sanar dasu, lokacin da aneelerh ta kammala zayyana masu komai, Lamarin yayi matuƙar girgizasu, ipo Yace"akwai matsala, Uzair ya fita gida ƙarfe 9 na dare, Shi kuma taj ya fita tare da ƴarshi ƙarfe ɗaya da rabi nadare? tabbas wani Babban al'amarine ya afku"
Ramlat tace"Kuma dukansu atare da wayoyinsu suka fita"?
Aneelerh tace"Shi uzair da wayarshi ya fita, Amma shi Taj banda masaniya akan hakan"
Dco yace"Aneelerh zaki yi mana jagora zuwa gidan Taj don mu fara gudanar da binciken mu"Amsa mashi tayi"toh" kafin suka miƙe gaba ɗayansu suka ɗunguma zuwa gidan Tajuddeen, A bakin gate Dco Yace ma malam Garba yabi bayansu, Don shima zasu buƙaci jin ƙarin bayani awurin shi, Lokacin da suka ƙaraso bakin gate ɗin gidan Tajo, Baba maigadi Na zaune saman benci cikin zullumi, Dco yace shima Yabiyosu Cikin gidan,Ya miƙe yabi bayansu,
A falon Gida Taj, Abie ya zauna, baba maigadi da malam garba suka zauna saman Carpet suna jiran tambayoyin da za'ayi masu,
Aneelerh ce ta yi masu jagora zuwa bedroom É—in taj, A bude suka samu É—akin, Da sallama tashiga ciki, Dco da ic da ipo suka mara mata baya,
A tsakiyar Dakin suka tsaya suna bin ko'ina da kallo, Karaf idanuwan Aneeleeh suka sauka akan wayar Taj dake yashe ƙasan tiles, A ruɗe tace"Uncle ga wayar shi anan" A tare police men din suka kai idanuwansu kan abunda aneelerh ke nuna masu,
Hanky Ic ya curo daga cikin aljihun shi, a hankali ya taka zuwa inda wayar take a ƙasan tiles,ya zuƙunna tare da ɗaukota,Ya dago da ita ya juyo da ita, Screeen ɗin wayar ya fashe, sakamakon Bugun tiles da Tayi,
Juyowa Yayi tare da kallon Dco yace"Sir, A hasashe na, Jiya Bayan aneelerh tabar gidan nan, Tajo Ya dawo Ya kwanta har bacci ya ɗauko shi, Wuraren ƙarfe ɗaya da rabi na dare, An kira wayar shi, kuma ya ɗaga kiran, tabbas an gaya mashi wani abu daya ɗaga mashi hankali, wanda yayi matuƙar razanar da shi, har baisan lokacin da yayi wurgi da wayarshi ba, Ya fito daga ɗakinshi Yaje ya ɗauki ɗiyarshi ya gudu da ita,tabbas anyi mashi barazanane, kuma zai iyayiyuwa anyi amfani da uzair wajen razanar da shi"
Jinjina kai dco yayi"tabbas akwai wani 6oyayyen Al'amari, daya faru a daren Jiya, taya za'ae mu gano ainihin meya faru?
Ipo yace"Abu na farko daya kamata muyi shine, mu fara tambayar masu gadin gidajensu A wani yanayi sukayi rabuwar ƙarshe dasu, sannan Wayar taj, Yakamata A gyarata, kodan mu samu damar bincikar last Call da yayi recieving awannan daren! Sannan zamu duba messages ɗin wayarshi, koda ace sun tattauna game da wani sirri dake atsakaninsu shida uzair"
Gaba ɗaya sunyi amanna da maganar ipo, aneelerh dae Jikin ta ƙaura yayi la'asar,Tunda taji hasashen Ic gabanta Ya dinga faɗuwa rass rasss! Daurewa kawai take yi,
Cikin falon suka dawo Kowa ya zauna, Ipo Ya kalli ɗan ladi baba maigadi na gidan tajo, yace"lokacin da taj zai fita A daren Jiya! Kaine ka buɗe mashi gate"Da sauri baba maigadi ya girgiza kai"a'a yalla6ai, Wlh ni bansan ma Ya fita ba, Kwatsam Ina Cikin Bacci sama sama Naji alamun buɗe gate, kafin inyi wani yunƙuri in miƙe inzo in duba,Tuni Ya fuce, Babu shi babu alamar shi, har waje na leƙa banga komai ba, na dawo cikin don in duba wurin ajiye motocin shi anan naga ya fita da ɗaya daga cikin su, Bayan haka kuma na shiga cikin gidan don inga ko ƴar shi angela na nan, sai naga babu ita, nan na gane cewa da ita ya tafi, Wannan shine iya abunda nasani,
Jinjina kai Ipo ya yi kafin Ya mayar da idanuwanshi kan Malam garba me gadin gidan Uzairu,Yace"kaifa?Me ka sani game da tafiyar Uzair"?