Sashe 46
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 6 min read
Komawa saman gadon tayi, ta kwanta tare da janyo junaid ta rungume shi ajikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci bacci yae awon gaba da ita, Ko da gari ya waye Aneelerh bata sanar da kowa game da mutumin da suka gani acikin gidan Uzair ba, ita kanta tarasa gane dalilin dayasa ta kasa buɗe baki ta faɗa masu cewa wani ya shiga gidan, wata'ƙil ta hanyar hakan asamu wata evidence da zata bayyana ainihin meya faru da su tajo, kuma tun daga ranar bata ƙara gigin zuwa gidan ba, gani take kamar mutumin yana bibiyar rayuwarta, kodan kada ta tona ma shi asiri dole ya bibiyeta, shiyasa take tsoran fallasawa,
Back To prison🌷
A kwana a tashi ba wuya wurin Allah A yau angel ta cika shekara 1 da rabi A gidan KURKUKUN ƘADDARA, tun daga ranar da tayi ma batool tambayoyin nan bata ƙara tambayarta wani abu dangane da gidan kurkukun ba, dalili kuwa shine a duk lokacin da zata tambayi batool game da prison ɗin, Sai wani abu ya faru, wanda zai ɗauke masu hankali, Haka xalika a duk lokacin da ta yi yunƙurin sanar dasu wani abu game da addinin musulunci sai wani abu ya faru wanda zai dakatar da ita, ta ko'ina an toshe mata hanya,
Abu ɗaya ne take kokarin Koyar da su shine yawan ambaton sunan Allah acikin maganarsu, saboda kwata kwata basa furta sunan Allah, zuwan angel cikin rayuwarsu sun fara koyan wasu abubuwan wanda basu iya ba, salon maganarsu ya fara komawa irin na angel, ta zama tamkar malama acikinsu, Idan suka kammala Cin abinci, bata bari su koma bacci, motsa jiki take sanya su suna yi, Ko kuma suyi wasa a tsakaninsu, bakomai yasa suke jin shakkarta ba, face rashin tsoranta, da kuma wannan kalmar ta charman dudu da take yi masu barazana da ita, shiyasa a kullum take Cin galaba a kansu, duk wannan tsawon lokacin da angel ta ɗauka acikin gidan kurkukun ƙaddara, har yau babu jituwa tsakaninta da Haris da kuma mr sound hater wato DANISH, su biyun nan sunƙi yarda da ita, duk da sunfi kowa jin shakkarta, kuma in ta bada umarni dole kowa yabi hada su ɗin,
Zaune suke gaba É—ayansu sun kewaye Kayan abincin da aka kawo masu, giants suna a tsaye sun kasa sun tsare suna jiran su kammala Ci su kwashe Kayan su tafi,
Hanna ce ta ya ye jan kyallen da aka rufe saman trays ɗin, tray na farko fried meat ne, sai faffadan plate me ɗauke da Snacks a tray na ƙarshe kuma jug ɗin ruwa ne, sai kofuna Bayan su kuma sai kwandon dake ɗauke da kayan marmari da ƴar ƙaramar wuƙa, wadda zasu yi amfani da ita su yanka fruits ɗin,
Kowa yakai hannu ya dauki fried meat yana Ci,
Gaba ɗaya hankalin angel na akan wuƙar da aka sako Cikin kwandon kayan marmarinsu Cin naman take yi kamar zata shaƙe, so take ta sace wuƙar batare da sun gani ba, ɗagowa ta ɗanyi tana kallon Su Giants dake a tsaye, abinci ma baza a bar mutun yaci a tsanake ba sai an tsare mutun da ido, a cikin zuciyarta ta yi maganar don tasan suna kallon su,
Cikin ƙankanin lokaci ta cinye nata abincin, miƙa hannu ta yi tana nuna jerin Cups ɗin dake a jiye Javed yace"ruwa zaki sha"? Ta ɗaga mashi kai alamar eh,
Da kanshi ya zuba mata ruwan ya miƙa mata, ta kar6a tana yi mashi godiya, bayan ta shanye ruwan ta ajiye kofin, xama ta yi tana jira sauran su kammala cinye nasu, ko ta samu a zo kan fruit ɗin yadda zata ji daɗin sace wuƙar,
Sun ɗauki tsawon mintuna kafin suka kammala, kowa ya sha ruwa Kafin suka kai hannu suna ɗaukar kayan marmarin, ganin basu yi amfani da wuƙar ba, yasa tace ma batool" ba zasu yanka ba" batool tace mata"A jiyewa zamuyi sai anjima mu sha," yatsina fuska angel ta yi ganin zata rasa damar da take da ita, ta ɗaukar wukar,
Dabara ce ta faɗo mata aranta, miƙewa ta yi tsaye tamkar zata bar wuri, ta ɗan ɗaga kafarta alamar za ta yi tafiya, gaba ɗaya ta yanke jiki ta faɗa saman kayan abincin, aruɗe su hannah suka kewaye ta suna jijjiga jikinta, hankalinsu a tashe suke ambaton sunanta,
Ganin sunyi mata rumfa ta yadda waɗannan Giants ɗin bazasu iya ganin meke wakana ba, a hanzarce ta yi wuf ta zura hannu ta ɗauke wuƙar tare da saƙe ta gefen qugunta, mutun ɗaya ne ya ga lokacin da ta ɗauki wuqar don ta fakaici idon su ne,
Miƙewa ta yi tana faman haki tace su bata ruwa tasha, jiri ne ya kwashe ta,
Da sauri Hibba ta cika mata kofi da ruwa ta miƙa mata, kaɗan tasha ruwan don bata jin ƙishir ruwa duk cikin plan ne,
Ganin sun kammala cin abincin yasa Giants matsowa suka tattara komai da suka yi amfani da shi, har fa sun Kama hanyar fita, danish ya É—aga murya tare da cewa"She took a knife" tashin sense a razane angel ke kallon shi, kafin ta É—aura idonta akan giants gani ta yi sunja burki sun tsaya cak, É—aya daga cikin ne ya jiyo tare da nufar inda suke, tamkar zaki
Saboda tsabar ruɗi tunkafin ya ƙaraso angel ta curo wuƙar ta miƙa mashi yasa hannu ya kar6a, ƙiris ya rage ta fashe da kuka kamar jira take su fita, ta yi wani irin kukan kura ta daka tsalle ta faɗama danish, kokawa ta 6arke a tsakaninsu bugu ta shiga kai mashi, ta yakushe shi da akaifun hannunta, hada cizo ta gartsa mashi gefen wuyan shi,
Su batool suna ta ƙoƙarin rabata da jikin shi, amma ina duk wanda ya yi gigin ta6a ta wurgi take yi da shi, daƙyar haris ya cakumota, rai a 6ace ya yi wurgi da ita gaba ɗaya ta kife ƙasa kanta ya bugu sosai,
Zuƙunnawa su kayi agaban danish dake yashe ƙasa yana fitar da numfashi sama sama, farar fatar wuyan shi tayi jawur ga sahun haƙoran angen nan tamkar an zana su, duk ta 6ata ma shi wuya da yakushi red marks ta ko'ina,
Ran kowannan su sai da ya 6aci, musamman haris, rai a 6ace ya ke faÉ—in
"Dama ae ba sonshi ki ke yi ba, shiyasa ki ke son kashe mana shi, na rasa me danish ya yi maki, bafa shi bane ya yi silar zuwanki prison ɗin nan ba, ballanta na kice xaki ɗauki fansa a kanshi, ki bar ganin ana jin tsoronki, Allah daga yau idan kika kuskura kika ƙara ta6a fatar jikinshi saina karairayaki,
É—agowa angel tayi idanuwanta sunyi jawur, batool da aziza suna a 6angarenta,