← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 179

Sashe 10

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

Karo na farko da jikinta ya fara ta6a namijin da ba muharraminta ba, shi kan shi bai yi tsammani hakan zata faru ba, saboda ba ita yayi niyar Janyo ba, Angel da ke a hannunta Yaso Ya damƙo, hatta mayafin da aneelerh ta rufe kanta dashi ya warware sumar kanta mai tarin yawa ta sauka har saman kafadarta, wani irin yanayi mara misaltuwa ne ya ziyarci kowan nan su, ƙoƙarin miƙewa aneelerh ta yi sai dai ina wani magnet ne ya ruketa, Runtse idanuwanta tayi da karfi ta soma ambaton a'uzubillahi minasshaiɗanirrajim, tun da ta ambaci hakan sai ga shi ta samu ƙwarin guiwar Raba jikinta daga Na taj, aikuwa A gaggauce ta hanzarta sauka daga saman gadon, ko mayafin ta bata tsaya ɗauka ba ta watsa da gudu tabar ɗakin,
A hankali taj ya lumshe idanuwan shi, ya yin da hancin shi ke shaƙar mashi ƙamshin turaren Jikin aneelerh daya gauraye Jikinshi, bakomai Ya tuna ba face Matarshi da ta gudu tabar shi, maca ce mai matuƙar son ƙamshi, shima kuma ma'abocinsa ne, baisan Ya akai ba Ya tsinci kanshi da tariyo yarda Aneelerh ta faɗo saman ƙirjinshi, da kuma yadda yalwataccen gashin kanta Ya zubo har a jikinshi,da kuma daddaɗan ƙamshin turaren ta,

Ganin Zuciyar shi na ƙokarin Zayyana irin kyawun surarta ne yasa shi saurin Ambaton A uzu billahi minasshaiɗanirrajim, Astagfurullah Ya Allah,

Miƙe wa Ya yi zaune Duk kasala Ta rufe shi, saukowa yayi daga saman gadon ya fito palour, babu kowa Hakan ya tabbatar mashi da cewa Neelerh ta gudu, frigde ya buɗe ya dauko Swan Mai sanyi ya dawo bedroom din shi, daga gefen gadon Ya zauna, buɗe murfin yayi ya tarfa ruwan a hannunshi Ya watsa ma angel asaman fuskarta, nan take Taja dogon numshi,

Slowly ta buÉ—e idanuwanta akan fuskar shi, Suna hada ido ta fashe da matsanancin kuka,

Natsuwa yayi yana kallonta ko kusa baiji tausayin kukan nata ba, tun da ya lura Ba son shi take Yi ba,

Cikin shessheƙar kuka tace "You want to kill me because you don't love me, yanzu da na mutu Allah zai kamani, so kake in shiga wuta ko? ta yi tambayar tana kallonshi, har lokacin idanuwanshi na akanta baice uffan ba,
"Kana Jina ka share ni ko"

Gyaran murya ya É—anyi can kasan makoshin shi ya furta"Dama kina tsoran Mutuwa"!
A tsiwace tace "Eh mana,malamin mu ya karanta mana wani hadithi wanda ke magana akan mai munana ma iyayensa ba zai shiga aljanna ba, A wuta za'a babbaka shi......"

Ƙiris Ya rage taj ya ɗan murmusa"So you know that but u keep hurting me ko"?

Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan, Ganin tasha Jinin jikinta sosai yasa shi kwantowa Yayi mata rumfa da faffadan kirjinshi, cikin sanyin murya ya soma magana Yayin da idanuwan su ke kallon Cikin na Juna,

"Angel, zan sanar dake wani abun da baki sani ba ba ki da wanda yafi ni a duniyar nan, ba ki ta6a tambayata mahaifiyarki ba, Bansani ba ko kina tunanin Namiji yana iya haihuwa ne, Shiyasa kike ganin kamar ni na haife ki, Baki da abun wulaƙantawa Irin mahaifin ki," shiru ya ɗanyi yana nazarin wani abu, ita kuwa ta kasa kunne tana sauraronshi,

Cigaba da magana yayi"Angel, mahaifiyarki a wulakance ta haife ki, Cikin bathtub tabar min ke, Cikin Jini kina ta kuka, Ni ina bacci kukan ki ne Ya tashe ni haka naje na sameki, Na ɗauke ki na rungume ki ajikina, duk da jinin da ke ajikin ki, Ni ban gudu nabar ki ba, kuma ban bari kin wulaƙanta ba, Sai da na tsaya akan ki angel da taimakon Allah har kika kai wannan lokacin, Tun da ki ke ƙuntatamun dai dai da na rana ɗaya ban ta6a Tunanin na tafi nabarki ba, kuma ban ta6a tunanin in sanya hannuna wurin ta6a lafiyar jikin ba amma angel......"kasa ƙarasa maganar Ya yi jin yadda ta rushe da kuka kamar ranta zai fita, ɗagowa Ya yi zaune yana kallonta.

Hannu ta ɗaura akai tana faɗin "Wayyo Allah na nashiga Uku,Na bani Na lalace!" hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,njin yadda babyn shi take Kuka,

Lallashinta ya soma ƙokarin"Am really sorry daughter, I don't mean to hurt u darling, Na faɗa maki ne don ki ɗauke ni da muhimmanci, don ki san cewa Ina sonki, kuma ina buƙatar tausayawa daga gare ki," bata tsaya sauraronshi ba, Ta sauko daga saman Gadon da gudu ta nufi toilet ta shige taja ƙopar ta rufe,

A hanzarce Ya sauko daga saman godon cike da fargabar karta kashe kanta, tura ƙopar yayi ya ji tayi Locking dinta,

Bubbuga ƙopar ya shiga yi yana ambaton sunanta"My angel am sorry, kada hakan Ya ta6a zuciyarki, kinsan ina sonki, banason zubar hawayen ki"

Daga Cikin toilet É—in yajiyo muryarta Cikin shesshekar kuka tana faÉ—in"I hate my self daddy, cikin toilet aka haife ni, kuma ta gudu tabar ni saboda bata sona......"
Runtse idanuwan shi Yayi tare da É—an Cizon lips É—inshi Calmly ya kira sunanta"Angel pls forget about it, Tunda kina da ni don me zaki damu kanki? Ni ne mom dinki kuma daddyn ki,
Zuƙunnawa Yayi agaban ƙopar, yana ji aran shi cewa tana zaune a gaban ƙopar, tsit ya ji ta daina kukan
"Pls say something to me, ko naji sanyi acikin zuciyata"
Shiru bata tanka mashi ba,
"Ki buɗa mun ƙopar"
Sai Lokacin yajiyo muryarta can ƙasa ƙasa"daddy inaso na mutu, kodan saboda nadaina 6ata maka rai"
Cikin matsananciyar damuwa Yace"idan kika mutu angel shi ne zan shiga Damuwa wadda zatayi silar mutuwata nima, saboda kece Oxygen ɗin da nake shaƙa,"

Yakai ƙarshen maganar tare da kwantar da kanshi jikin door ɗin, don Yaji daɗin Jin muryarta

"I made a mistake daddy, I won't hurt you anymore,"

Saboda tsabar Mamakin Jin abunda tace har saida Ya É—an dago da kanshi, yana kwalkwale kunnanshi wai koda Ya samu matsalar hearing ne,
"I love u daddy" ya kuma Jin ta furta mashi aruÉ—e yace"Repeat it pls"
"I love u daddy"
"sake maimaita mun naji"fuskar shi É—auke da murmushi Ya yi maganar,
Sake maimaitawa ta yi kamar yarda ya nuna yana son ta yi ma shi,

"I love U daddy, Bani da tamkarka a duniyar nan"
Wani irin ihu ya saki, Irin wanda Ƴan kwallo ke yi idan sunci nasara akan wasan su,

A ƙagare Yace"Come out pls, ina so naji ɗumin ki a jikina"

Yana jiyo alamun tana buɗe ƙopar kamar jira yake yi, tana ƙarasa buɗe wa Ya janyo ta Jikin shi yayi hugging ɗinta very tight, hannun shi na acikin sumarta, Wani irin farin Ciki ne Ya lullu6e shi kamar wanda a ka yi ma Albishir da gidan Aljanna,' dole Taj ya yi farin ciki cos this is the first time da angel Ta fara furta mashi kalmar tana son shi a mtsayina mahaifinta, Ya ji tausayinta sosai, bai ta6a tunanin akwai lagwanta ba sai yau, da ta ji cewa mahaifiyar ta ta gudu ta barta, Jikinta ya yi sanyi, da yasan da haka da tuni ya faɗa mata, da duk wannan abun bai faru ba,
daukarta Yayi asaman bayanshi, yakaita Cikin motarshi, atare da ita suka je masallaci, Ya barta acikin mota, Bayan ya kammala sallar, ya dawo Ya shiga motar yayi driving ɗinsu zuwa Restaurant, komai take so shiyasa aka kawo masu, sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Suka dawo gida, A palour suka zauna saman Sofa tana rungume ajikin shi, Suna kallon tashar Mbs 3, dama best channel ɗinta ce saboda suna sanya Cartoon, tafi sha'awar kallon Cartoon da kuma zombie,

Tuni bacci ya dauketa ajikinshi, asaman kafaÉ—ar shi ya É—auke ta Ya nufi bedroom dinsu, don ya kwantar da ita, a hankali Ya tura kopar É—akin Ya shige, A saman gado Ya kwantar da ita, Sai da ya fara daukar wayar shi dake ajiye agaban mirror, Tukunna Ya haye saman gadon ya janyo ta a jikinshi, Yana shafa sumar kanta, cikin magagin bacci ya ji tana fadin"I luv u daddy" murmushi ya É—an saki, Tare da manna mata kiss a gefen fuskarta
"Luv u too My own daughter"

Number Uzair Ya kira, tana fara ringing Uzair ya É—auka,
"Aminina Yanzu nake shirin zuwa duba jikin ka"
"Na hutasshe ka ba sai kazo ba, Jiki ya yi sauƙi Alhamdulillah"
"Naji labarin abun kunyar da kaso ka aikata na kashe Æ´arka, Ae ni har na yi shirin zuwa É—aukar rahoto"
Fashewa Taj yayi da dariya"Ta
6atamin raine, ni kaina bansan nayi wannan yunkurin ba,"
"Yanzu Ina virus ɗin taka take"?a cewar uzair, don tun ranar da ta Sa ƴan sanda su ka kama su akan ƙazafin da ta yi masu na cewa su ƴan yankar kai ne, tun daga ranar Yake kiran ta da Virus,
Murmushi Taj yayi, tare da kai hannu ya shafa sumar kan angel, Virus ta yi bacci, Mutumina ka ta ya ni farin Ciki,"
Uzair yace"Meya faru"?
Nan Taj ya kwashe duk abunda Ya faru tsakanin shi da angel ya sanar mashi,"
Yana jiyo sautin dariyar farin cikin da uzair Yake yi,
"Ja'irar taji ƙamshin mutuwa, Allah yasa ƙarshen wahalarmu ce tazo, Amma fa nayi farin Ciki,
Chapter 10 · 0% Book details