Sashe 119
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya yi matuƙar yin kyau, kusan hawa bakwai ne ajikin cake ɗin, A tsakiyar ɗakin Giant mai ɗauke da table ɗin Ya sauke shi, Sauran dake ruƙe da wooden trays suka sauke farantan saman dining Carpet ɗinsu, basu tsaya jiran su farka ba, a tare suka juya tare da fuce wa daga cikin ɗakin, "
ƙarar rufe ƙopar ne Ya farkar da Azeeza daga bacci, abun ka ga ruɗaɗɗa. A firgice ta ware Idanuwanta, Hannunta dafe da saitin zuciyarta, dake ta faman harbawa, Tayi tsammanin ko zuwa za'ae a ɗauki wani daga Cikin su, jikinta na kerma ta ɗan yunƙura ta miƙe zaune don taga su wanene, A tsorace take kallon Cikin ɗakin, Karaf idanuwanta suka sauka akan Ƙaton cake ɗin, mai matuƙar ɗaukar ido, Mamaki ne Ya kamata, Ta zaro ido tamkar ƙwayar zasu ƙundumo ƙasa, Jiki na 6ari ta sauko daga saman gadon ta nufi Cake din, Saboda tsabar girman shi, da kuma tsayin table din dake dauke shi, sun kere mata, bata iya ganin ƙarshen cake ɗin idan tana a kusa dashi, Kamar wata baƙauyar Daji haka ta dinga zagaye Cake din har saida kanta Ya fara juyawa tukunna ta ɗan dakata, Hannunta ruƙe da qugunta, Sai faman Jinjina kai take yi, alamar mamaki, ta wutsiyar idonta, ta hango kamar kayan abincinsu, Da sauri Ta juya ta 6angare da Daning Carpet ɗinsu yake, waro ido tayi, badan tana mamakin Abincin da aka kawo musu ba, face Sabbin farantan da aka canza musu masu tsayi.
Wani irin ihun farin Ciki ta saki, kai tsaye sautin ihun ya daki dodon kunnan masu bacci, Saboda tsabar firgitar da su ka Yi, kusan atare suka Yaye bargunan da suka lullu6a dasu, Kowannan su Ya miƙe xaune, wasu suna hamma wasu suna Yin miƙa, hada masu miyan bacci abaki irin su parveen da mubeen, At same time suka kai idanuwansu kan Azeeza Kafin suyi yunƙurin Yi mata magana tai saurin Nuna masu ƙaton Cake ɗin da hannunta,"
Zallar mamaki da al'ajabi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Nan take baccin da bai ƙarasa sakin su ba, ya washe, ɗaya bayan ɗaya suka dinga saukowa daga saman gadajensu suna tunkarar ƙaton Cake ɗin, a wani irin kasalance, Danish ne kaɗai bai sauko daga saman bed dinshi ba, Yana zaune daga bakin gadon idonshi akan cake ɗin, Ga dukkan alamu baccin bai ishe shi ba, katse mashi shi akayi, sai faman lumshe eyes ɗinshi yake yi,
A jere Suka kewaye Cake ɗin, Kowa Ya baza na mazurinsa, Ko ƙyaftawa ba su yi, parveen ce tai ƙoƙarin kai hannu don ta ta6a shi da sauri Javed Ya ka6e mata hannu tare da cewa"Uwar Hankali, Daga ganin cake kinsan Wanda Ya ajiye shi ne?
Azeeza ce ta bashi amsa da cewa"Ina tunanin Giants Ne suka kawo shi, tare da breakfast ɗinmu," ta ƙarasa maganar tare da Juyawa tana nuna mashi Dining Carpet ɗinsu, atare Su naufal suka kai idanuwansu kan abunda take ƙoƙarin nuna musu, mamakine Ya ƙara kama su ganin an canza musu farantan abincin su, don suna sane da Irin trays din da ake kawo musu abinci cikinsu, To yau an canza musu wasu sabbin farantai, masu tsayi,
Angel dai ta rasa bakin magana, tarasa gane wannan sabon salon na Kurkukun ƙaddara, abubuwa suna ta canzawa, Anya wannan farin Cikin bana ƙarshe bane acikin xamansu Prison? Na farko an canza musu kayan amfani na toilets da sabbin uniforms duk da tsohuwa tace musu itace ta buƙaci abasu akayan don ta faranta mu su,
Tsawon kwanaki tunda aka tafi da batool ba'a ƙara ɗaukar wani acikinsu ba, duk da bata ga wani ya ƙara yin menstruation ba, wata'ƙil shiyasa ba'a zo an ƙara ɗaukar wani ba,
ta yi zurfi Acikin tunaninta, muryar Naufal ce ta dawo da ita Cikin hayyacinta
"Nifa ina tunanin Sabbin prisoners za'a kawo mana Yau, yakamata muyi wani abu akai, Mu gyara musu gadajensu, sannan muje muyi wanka mu sanya sabbin uniform É—in mu kada suxo su ganmu kaca kaca suce xasu raina mana wayau,"
Naufal na kai ƙarshen maganar tashi, Yasmin tace"Nima nayi tunanin hakan, idan ku ka lura da rubutun dake akan cake ɗin, Kamar Ana yi ma wasu barka da zuwa ne," eve tace"in dai haka ne kuwa nayi mamaki, daga gani waɗanda za'a kawo mana ƴan gata ne, don ko time da aka kawo Angel ba'a shirya mata cake ba" Mubeen ne ya bata amsa da cewa"ae ita angel ita kaɗai aka kawo daga waje, su kuma waɗannan ina hasashen dukansu ba acikin prison suke ba, Sannan kuma ki duba da kyau Ajikin Cake ɗin an rubuta Prisoner's Day, that mean an shirya shi ne domin mu kan mu muyi enjoying ɗin ranar mu ta prisoners," Da mamaki akan fuskar Hanna tace"Abun da ɗaure kai, Har wani prisoner's day gare Mu," ta6e baki Haris yae, yama rasa ta cewa, kwata kwata baiyi farin ciki da ganin cake ɗin ba, acewarshi maimakon adawo musu da ƴar uwarsu batool, An dage sai faranta musu akeyi, gani yake kamar ana ƙoƙarin ɗauke musu hankali ne daga tunaninta,' a fili Yaja guntun tsoki, fuskarshi amurtuke babu walwala, Deeja ta lura da yanayin fuskarshi, tunaninsu yazo ɗaya, itama abunda take hasashe kenan acikin zuciyarta, sai dai basu fito sun faɗa ma sauran ƴan uwan nasu ba, kodan gudun kada su tarwatsa musu farin Cikin da suke ci. Ganin yadda suke ta zagaye cake ɗin, Cikin Jin daɗi,
"Muje mu yi wanka, mu canza kaya, kafin Mu zo mu yanka Cake" Rubina ce tai maganar, da gudu suka nufi sashen toilets, suna ƴar rige rigen shiga, Mutun uku ne suka fara shiga, sauran suka tsaya suna jiran su fito suma su shiga, Waɗanda suka rage Acikin ɗakin Danish dake zaune gefen gadonshi, Sai angel da haris and deeja da kuma naufal dake tsaye gaban ƙaton Cake ɗin, daga bisani ne Angel ta koma gefen Danish ta zauna, tare da kallon fuskarshi tace"Ka tashi lafiya"? Ya mutsa fuska yae muryarshi adisashe yace"A'a, baccin bai ishe ni ba, azeeza ne ta farkar dani,"
"Ka kwanta mana, ka yi bacci, amma idan kana jin yunwa ka bari mu fara cin abinci, in yaso daga bisani sai ka koma baccin" girgixa mata kai yae tare da cewa"na haƙura da komawa baccin, tun da kin farka ƙwara nima na kasance a farke" Yaƙarasa magnar yana faman lumshe idanuwashi akan fuskarta,
"Ko zamuje muyi wanka ne"? amsa mashi tae da toh," Ya ruƙo hannunta acikin nashi, suka nufi toilet, a lokacin su Parveen sun kammala nasu wankan sun fito daga sashen toilet ɗin, Sai da suka je bakin ƙopar toilet ɗin Taga yaki sakin hannunta, tace"Ka shiga mana" ni sai na shiga ɗayan toilet ɗin" da buɗar bakinshi sai cewa"why bazamu shiga atare ba? Ni inaso na taimaka maki ne wurin yin wankan" fuskarshi a yamutse yai maganar, ita ko ta saki baki tana kallon shi, Mamaki Ya hanata magana,' har saida yaja hannunta da niyar su shiga ciki, da sauri ta fusge tana faɗin"Kai fa ba cikakken hankali ne da kai ba, na faɗa maka babu kyau ka daina cewa mu shiga toilet ɗaya, hakan bazai ta6a yiwuwa ba, Kana namiji ina mace kuma ka ce zaka yi mini wanka" ta ƙarasa maganar tana jifar shi da harara, ta lura haryan zu Danish baida linzami, shi dai burin shi yayi mata wanka, sai kace wata ƴar tsana,
"Angel ba wani abu bane fa, kafin zuwanki prison ɗin nan, munayin wanka dasu Batool, so wannan ba wani matsala bane....."daƙyar ya ƙarasa maganar saboda kallon da take watsa mishi,
"Ba ka ji me ka ce ba? Kafin zuwana kurkuku, That's mean lokacin kuna a jahiliya period! bayan nazo Kuma saina zo maku da tsarkakakken addini, da ya hana mace da namiji su ke6e awuri ɗaya, sannan babu kyau kallon tsiraici, baida amfani ma mutun ya dinga kallon tsirai cin shi balle ya kalli na wani kuma, fatan Ka fahimce ni" ta yi maganar tare da yi mashi gwalo, tana dariya ta fada toilet taja ƙopa ta datse, bayan ta shiga ciki, ta sanya hannu ta dafe ƙirjinta, tana faman sauke ajiyar zuciya, lamarin Danish yafi ƙarfinta, Dole sai tana taka mishi burki, idan ba haka ba, wata rana zaifi ƙarfinta ne ya ɗauketa yakai ta toilet da sunan zai mata wanka,
Saboda ta ɗauke su tamkar Ciki ɗaya suka fito, shiyasa ma take bari suna ruƙe juna, don Lokacin da take tare da daddynta, babu namijin daya isa Ya ruƙe mata hannu tun tana ƴar ƙaramarta, bayan shi sai Uncle abdallah sai kuma Uzair, saboda ta tsani Namiji ya ta6a jikin ta, akwai ranar da wani malaminsu na makarantar boko yayi gigin Shafa la66anta, ya gansu pink sun burgeshi, aikuwa ta daddage ta gartsa mashi cizo, ɗan tahalikin nan jinya har gadon asibiti, saboda cizonta tamkar dafi gare shi, zai yi wuya ta ciji mutun batare da zazza6i ya rufar mashi ba, kamar dai yadda ta yi ma danish a kwanakin baya kafin su fara shiri daya tona mata asirin ta ɗauki wuƙa, ta yakushe shi tare da gartsa mashi cizo, zazza6i ya rufe shi har giant suka tafi dashi,"
tana Jiyo alamun buɗe ƙopor ɗayan toilet ɗin dake a jikin wanda take Ciki, murmushi tasaki saboda ta gane shine Ya shiga, aranta tace"ɗan rainin wayau, saboda kawai ka ganmin budurcina shine zaka sa naci akan sai ka yi mini wanka," ta ƙarasa maganar tana faman Cizon la66a,
Kafin wani lokaci gaba ɗayansu su kayi wanka, Kowa Ya cire tsaffin uniform ɗinshi suka maida sababbin ajikinsu, Wani irin kyaune ya bayyana akan fuskokin kowannan su, Farin Ciki ta ko'ina, Sun kewaye Cake ɗin suna ƙare mashi kallon kafin suyi tunanin Yanka shi, Angel tace su jira ta fara yi musu addu'a,
Suka amsa mata da to, Kowa Ya natsu A yayin da take karanto musu addu'o'in ta tofa ma Cake ɗin, Haris yace"kin fake da addu'a kina watsa mana yawu akan cake ɗin mu" Da zolaya yayi maganar yana hararanta, gaba ɗaya suka sanya dariya, fararen haƙoransu kamar gonar auduga,