Sashe 121
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
A jere mutun Goman nan suka nufi saman Benan zasu koma, Christian ɗin nan Namiji Ya fasa wata irin ƙara da taja hankalinsu, da gudu yabi bayan waɗanda aka tafi dasu, Sai dai bai kai ga ƙarasawa ba, Giants suka Damƙo hannun shi, sosai idanuwanshi suke fitar da hawaye Yayin da yake miƙa hannu yana nuna ƴar uwarshi mace, Yana faɗin"My twin sister pls kada ku raba ni da ita, bazan iya rayuwa babu ita ba, " Fashewa da kuka ƴar uwar tashi ta yi kamar ranta zai fita, da gudu ta dawo ta faɗa jikinshi ta ƙanƙameta, Kamar zai maida ta Cikinsa, wani irin tausayin su ne ya kama su angel, azeeza tuni ta fara yi musu kuka saboda sun yi matuƙar ta6a mata zuciyarta, bayin Allah Kamanninsu sak iri ɗaya, Daga gani suna matuƙar ƙaunar junan su, saboda rashin Imani na Giants suka sa ƙarfi wurin raba su da juna, Su ka tasa ƙeyar macen gaba suka haura saman benan, Sai kuka take tana faɗin"My twin bro, Ka kula min da kan ka, Duk inda za'a kai ni zan dawo wurin ka," shima yana kuka yana kiran sunanta, Ahaka har aka fuce da ita" Bayan fitar su ɗakin yai tsit Ya rage Saura Su Angel da tsohuwa Zafreen sai mutun biyar da aka Bar musu cikin sabbin prisoners, Haƙika Tagwayen sunyi matuƙar ta6a Zuciyoyin su, Namijin sai share kwalla yake yi, idanuwanshi sun yi jawur dasu, ga wata irin zufa dake tsastsafo mishi, Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi, An raba shi da twin sister ɗinshi, Giant sun yi yankan ƙauna.
Gyaran murya tsohuwa zafreen ta yi musu kowa Ya shiga natsuwarshi, Cikin harshen turanci ta soma Yi musu magana
"Ina fata tsohuwa Tamira ta yi maku bayanin komai a dangane dani, ba sai na maimaita ba," Har suna haÉ—a baki wurin ce mata eh,
Jinjina kai tayi Yayin da take kallonsu É—aya bayan É—aya, kafin ta tsaida Tsoffin idanuwanta kan fuskar angel,
"Sai dai ga dukkan alamu akwai waÉ—anda basu san wacece ni ba, Amma asannu zasu fahimta"
Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta kalli Sabbin prisoners da aka Bar musu tace"Ya rage naku, Ku zauna lafiya ko akasin hakan, Bata shafe ni ba, zan dinga zuwa akai akai ina duba ku, A koda yaushe ku kasance Cikin shiri"
A hankali ta soma ja da baya Still idonta akan Angel, Kafin ta ɗauke su tare da juyawa ta nufi stairs ta haye, Giants su ka take musu baya, Suna jiyo datse ƙopar ɗakin, Nan fa kowannan su Ya shiga sauke ajiyar zuciya, don ba ƙaramin shakkarta suke ji ba,
Sai lokacin su Haris suka samu damar yin magana
"Wannan wani irin rashin imani ne? Don me za'a raba shi da Æ´ar uwarshi? Bayan akwai sauran gadajen da kowannan su zai samu wurin kwana, Ni bansan me ke damun waÉ—annan mutanan ba, tsabar zalunci ne kawai" Haris ne yae magana yana mai jan tsoki, Azeeza tace ni wlh tausayi suka bani bayin Allah, hakanan an raba su"
Angel ta shiga ruÉ—ani, Ita damuwarta ina za'a kai sauran toh? Ga kuma gadajen su A ajiye, Allah dai yasa ba wani mugun abun za'ayi musu ba, bakowa tafi jima tausayi ba face christian É—in nan, Ya yi tsaye hawaye ta ko'ina akan fuskarsa.
Danish ne yai ƙoƙarin zuwa wurin shi Ya janyo shi tare da rungume shi yana lallashinsa, Cikin shessheƙar kuka yake faɗa mishi cewa ƴar uwarshi, tun da suka taso atare suke rayuwa komai atare suke yi, basu ta6a rabuwa ba, Amma yau An raba shi da ita," daƙyar Danish ya samu Ya lallashe shi, Har ya daina kukan, Tukunna Ya raba jikin su,
Tun da suka shigo ɗakin Yaron nan da aka bar musu zabiya, Sai tsalle Yake Yi yana dariya, babu wanda ya lura dashi saboda Halin da suka shiga, Ya haye saman gadajensu Yana ta ɗaukar fululluka yana watsar dasu ƙasa Hada bargunansu.
"Hey, y'all! my name is Unaiza, and i'm excited to get to know u all."
Da sauri suka kalli bakin mai magana, wata irin zazzaƙar murya mai cike da kwarkwasa da duniyanci, Bakowa bace face Ƴar madarar nan, da alama taji sunyi tsit basu tarbesu ba, Shiyasa tayi fara yi musu magana, ae daga ganinta wayayyiya ce, Murmushin yaƙe kowannansu ya sakar mata, Batare da sunce komai ba, ta kuma cewa
"It seems like we're not welcome at all" Jin wannan maganar yasa Danish Yin ƙoƙarin yi mata magana
"it's not like that, We welcome you with open arms. We are excited to have you here and look forward to getting to know you. You are highly welcome here"
Fuskar shi ɗauke da murmushi ya ƙarasa maganar, Yana yi musu nuni da gadajen su, don su shugo ciki su zauna.
shu'umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, irin na tatattun ƴan iska, Ba zato ba tsammani, su angel suka ga ta nufi Danish Tana ƙarasawa gabanshi Ta sanya hannu biyu Tayi hugging ɗinshi ajikinta, Cikin harshen turancin dake nuni da ƙwarewar ta ta furta"Tayi matuƙar jin daɗin haɗuwa da shi, tana fata za'a kar6e su hannu bibbiyu,"
Ran angel ya 6aci da sauri ta nufi inda suke atsaye, Suma sauran suka bi bayanta, Tana ƙarasawa gabansu ta sanya hannu Ta ruƙo damtsen hannun Danish Ta janye shi daga Jikin yarinyar, ta dinga jefa mata harara, Amma ko ajikinta sai ma ta sakar mata ƙayataccen murmushi tare da miƙa mata hannu don su gaisa
"Hi, Am unaizah ƴar gidan daddy, can i know u"? Ta jefa ma angel tambayar, Yatsina fuska angel ta yi, Kamar bazata tanka mata ba, Sai kuma tace"My name is Unaisah, Amma daddyna Yana kira na Angel, shine sunan da kowa Yake kira na" Dariya su ka ga ta saki tare da cewa"Wow, sunan mu yae shige dana juna, banbancin kawai harafin ƙarshe ne, ina fata zamu zama abokai" Da hausa tayi maganar amma sai ka rantse da Allah da turanci tayi ta, Saboda Yadda take furta ta, daga gani baturiyace amma ta iya hausa ba laifi,'
Murmushin yaƙe angel ta sakar mata tare da cewa"why not, tun da zama ya haɗu mu wuri ɗaya" murmushi ta kuma saki tana kallon fuskokin su Tace Idan ba damu tana son su gabatar mata da kansu, batare da sun Yi mata musu ba, ɗaya bayan ɗaya Kowannan su Ya gabatar mata da kanshi, koda a kazo kan Danish Yana yi mata bayani dangane dashi har wani lumshe ido take yi tana kallonshi, ran angel ya gama 6aci gani take kamar an kawo musu annoba ne, saboda babu natsuwa atare da yarinyar, bayan sun gama da kansu, Haris ya kalli sauran sabbin prisoners ɗin yace"saura ku ya rage ku faɗa mana sunayen ku, sannan muna son musan daga ina ku ke"_
Ƙaramar yarinyar nan ce ta fara Yi musu magana tace sunanta *JAMIMAH* Itama Prisoner ce a gidan kurkukun ta taso shekararta Goma cuf aduniya," Bayan Jamima Ta kammala gabatar musu da kanta, Wannan Doguwar mai zubin Taliyar indomi Ta faɗa musu cewa"ita Sunanta *SARAH* shekararta, Sha bakwai, Itama rainon kurkukun ƙaddara ce" Jinjina kai su kayi yayin da suka maida dubansu ga kirista ɗin nan suka ce mashi Ya faɗa musu wanene shi, Cikin sanyin murya yace musu Sunan shi*GABRIEL* twin sister ɗin shi kuma sunanta *GABRIELA* shekararsu goma sha bakwai," su angel sun yi mamakin jin shekarun su ashe duk Yara ne, Girman Jikine kawai, Naufal yace"rainon kurkukune ku ma Ko kuwa daga waje aka kawo ku"? Gabriel yace mishi bazai iya tuna komai dangane da rayuwarsu ta baya ba, shi dai kawai a bunda zai iya tunawa twins ne su, yana matuƙar ƙaunar ƴar uwarshi itama tana son shi, tare suka taso basu ta6a rabuwa ba"
Maganar shi ta ɗaurewa Angel kai, ga dukkan alamu suma tagwayen ba rainon kurkuku bane, daga waje aka zo su, Saboda babu addini agidan kurkukun ƙaddara, Su kuma Akwai sarƙar cross a wuyansu, hakan na nufin An canza musu tunaninsu ne,
Gaba ɗaya sun manta da mutun ɗaya daya rage basu su tambayi wanene shi ba, Kowa ya shafa'a da ɗan ta halikin nan, Sai da Parveen ta tuna da Abincinsu, Da sauri ta waiwaya baya don ta kalli Kayan abinci, Ras taji gaban ta ya faɗi ganin Mahaukacin yaron nan zuƙunne gaban faranti Ya ɗauki Chicken shawarma Yana turawa abaki, rabi na shiga rabi na zubewa ƙasa duk ya cakalkala ta, ga kuma Bargunansu daya wurgo ƙasa da fululluka, Da ƙarfi Ta ambaci"Innalallahi! " gaba ɗaya suka kalle ta, Ganin Tana kallon saitin dining carpet ɗinsu Yasa suma suka kalli wurin, Da gudun gaske parveen ta nufi yaron ta shaƙo wuyan rigarshi Ta wurgar dashi gefe ɗaya, Ya faɗi ƙasa kanshi ya bugu, Maimakon yayi kuka sai ya kama Dariya Yana Wuntsila ƙafafuwanshi, Rai a6ace Parveen ta shaƙo wuyanshi tana faɗin"Wanene kai?daga zuwa yau zaka fara Yi mana hauka? kana da hankali Kuwa....." bata kai ƙarshen maganar ba, sakamakon jin saukar Yawun daya watsa mata akan fuskarta, tsabar fusata yasa ta kikkifa mishi maru ka, ya dinga dariya ba ƙaƙƙautawa, daga gani jaki ne bai jin bugu.
Hankalinsu yae matuƙar tashi, saboda sun fahimci cewa Yaron yana da ta6in hankali, Mahaukaci ne aka kawo musu,
"Parveen ki daina bugun shi, Baki ga yaro bane"? Azeeza ce tai mata magana, Rai a6ace tace"Babu ruwana da yaro ne, Ubanshi zanci, har ni zai watsa wa miyau a fuska"? Da alama ta fusata, Rigarshi ta damƙo ta goge miyan daya watsa mata a face ɗinta, duk da haka bata ƙyale shi ba, sai da ta sanya hannu ta dunguri kanshi, Kafin ta miƙe ta nufi toilet don ta wanke fuskarta, badajimawa ba Sai ga parveen ta dawo Cikin ɗakin fuskarta ɗauke da lemar ruwa, Sai Jifar yaron take yi da harara kamar ƙwayar idon zasu faɗo ƙasa.
Deeja tace"Mun shiga uku, tamu ta same mu, Yanzu haka zamu rayu da wannan Ta6a66an? Naufal yace"Bazamu zuba mishi ido ba, Dole mu koya mishi hankali," tsoki haris yaja batare daya ce komai ba,