← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 179

Sashe 120

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waye xai yanka mana cake ɗin? maji daɗin gado ko kuwa Maji daɗin abinci"? naufal ne yai maganar, parveen uwar zumuɗi tace"Ni xan yanka" Azeeza tace wlh baza abaki ba, indai aka baki sai an bani nima na yanka" harara parveen ta watsa mata tana faɗi"Dallah jibarki can ƙasa, In banda rigima taya za'ae ki iya yanka cake ɗin nan"? Saboda tsabar baƙin cikin kalaman Parveen yasa azeeza ta zuƙunne kasa tana raira musu kuka," rai a6ace angel ta kalli parveen"bansan meyasa kike son kushe halittar mutun ba, Bakisan babu kyau ba, yanzu ita da kike ma gorin halitta, shin ita ta halicci kanta? Ke kanki fa Girma kikayi kika ganki ahaka, Ko ke kika tsara ma kanki halitta ne" ɗaure fuska parveen tayi tuni idanuwanta sun ciko da kwalla, angel tace"ni ban faɗi hakan don na 6ata maki rai ba, kawai inaso kisan cewa ba abu bane mai kyau kushe halittar mutun, cos bashi yai kanshi ba, haka Allah ke son ganin shi, ke kanki, nafi ki tsayi, Ni kuma Danish Yafi ni, so kinga ni kowa Da irin nashi halittar" ganin zasu 6ata masu farin Cikin su yasa haris, Yin saurin dakatar da Angel ta hanyar yi musu magana"its okey, pls maganar ta wuce, indai akan yankar cake ne na yanke shawarar Danish Shine xai fara Yankawa, saboda shiyafi dace wa Daya yanka shi, Idan ma kuka kwantar da hankalin ku kowa ma xai yanka, ba kuga girman Cake ɗin ba? Ai mutun ɗaya bazai iya yanka shi ba, dole sai an haɗa hannu,"

Duƙawa Danish yai tare dakai hannu ya ruƙo Azeexa ya ɗago da ita, gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kanshi ganin ya ɗaurata Saman wuyanshi kamar wata ƙaramar yarinya, nan fa ta fara washe baki ta koma tana yi ma parveen gwalo saboda anyi mata makawuya tsayinta ya zarce na kowa,

"Ku bata knife ɗin, Ita nake so tafara Yankawa" Acewar Danish, da sauri Haris ya ɗauki wuƙar Ya miƙa ma Azeeza dake asaman wuyan Danish, Tasa hannu ta kar6a tana dariya, Ita kanta parveen batasan lokacin data kwashe da dariya ba, ganin yadda Azeeza take alfahari da tsawon da ba nata ba, sai da suka fara ƙirga one two three Kafin Azeeza ta ɗaura wuƙar zata yanka Cake ɗin, sai dai bata kai ga yankawa ba, Suka Ji motsin buɗe ƙopa, a firgice suka kai idanuwansu kan benan,

A matuƙar ruɗe suke kallon ƙafar matashiyar budurwar data fara leƙo wa, wasu matsiyatan Highheels ne a ƙafar masu shegen tsini, Kai daga ganin fatar ƙafar ta rainon madara ce fara tas, saboda tsabar ruɗi azeeza batasan time da ta saki wuƙar yanka cake ɗin dake a hannunta ba, Tabarakallahu ahsanul khalikin, wata irin tafiya yadda kasan bata son taka ƙasa, Daƙyar take taka staircases ɗin, takalmanta har wani sauti suke badawa ƙwas ƙwas! Daga gani ba ita kaɗai bace, akwai sauran dake abayanta, kowannan su sanye Cikin Uniform ɗinshi...........❤

Haƙiƙa Ta yi matuƙar tafiya da hankalinsu, Kyakkyawar matashiyar budurwa, jawur da ita, Uniform ɗin Jikinta Style ɗin yasha banban da nasu, Ita nata gajeran skirt Launin Ja Ko laps ɗinta bai rufe ba, fararen tsala tsalan cinyoyinta sun bayyana a suffarsu kamar ba'indiya, daga sama Coat ce launin Ja, daga Ciki ƴar vest ce, Hannunta na Hagu na ruƙe da igiyar ƙatuwar backpack ɗin data rataya saman shoulder ɗinta.

yarinyar bata da ƙiba ko misƙala zarratin, sai dai wani abu dake da matuƙar jan hankali ajikinta, shi ne ƙirjinta, duk rashin ƙibarta ƙirjinta a cike suke fam, Boobs ɗinta tamkar zasu fasa rigar jikinta, tana da doguwar fuska, dara daran idanuwanta farare ƙal launin ocean blue, Jar sumar kanta anyi mata kitso guda biyu, bata da yawan gashi sai dai akwai tsayi, wutsiyoyin kitson sun sauko ta side by side na shoulders ɗinta, hancinta hada nose ring golden colour, earrings ɗinta na zallar gold ne, gefen wuyanta zanan tattoo ne na bindin ɗawisu, Launika daban daban, A bunka ga farar fata zanan yayi bala'en yi mata kyau, daga gani yarinyar ƴar gidan wani shege ce, mai ji da Naira, sai dai daga ganin fuskarta, ba ƙaramar wayayya bace, zai yi wuya tayi kunya a ido.

Hankulansu Haris gaba ɗaya yana akanta, Har sai da taƙarasa saukowa daga saman benan, ta ɗan dakata da yin tafiyar tana faman wurwuga manyan idanuwanta akan fuskokinsu, Sauran Sabbin Prisoners ɗin dake a bayanta, Daga Cikinsu akwai wani matashin saurayi dogo twins ne shida ƴar uwarshi, wuyansu na sanye da sarƙar cross wanda ke nuni da addininsu, kyawawan gaske, Launin fatarsu kala ce mai tsada wadda ake kira da Chocolote, yadda kasan ɗan wrestling haka ƙirar Jikinshi take, ga wata irin haɗaɗɗiyar sumar kai, Curly har ta gaban goshin kanshi, Uniform dinsu jajayene, Bayansu Akwai wani Ƙaramin yawo da bazai wuci shekara sha biyu ba, Albino ne (Zabiya) Hatta sumar kanshi Fara ce fat kamar hurhura, daga gani baida cikakken hankali don tunda suka faɗo ɗakin ya ke ta tsalle Yana dariya, Bayan su akwai wata Doguwar budurwa yadda kasan fatalwa, Bata da ƙiba ko kaɗan, sai tsawo tubarkalla kamar qugunta zai karye, duk tsayin Danish To ga wadda ta taka shi, gwanin ban tsoro tana tafiya kamar macijiya, launin wankan tarwaɗa ce ta ɗaure guntuwar sumar kanta da ribbom,

Tashin sense, tsabar ruɗu Ya hana su angel cewa komai sai kallon kallo suke yi a tsakaninsu da sabbin prisoners da aka kawo musu, Aranta tace wannan karan Hada Jinsin Aljanu aka bankaɗo mana, Mun shiga ukun mu, Ashe Zaune bata ƙare ba,

Daga Cikin sabbin prisoners ɗin akwai wata ƴar ƙaramar yarinya da bazata wuci 10 years ba, Komai na jikinta sak irin na azeeza, banbancin shine ita azeeza tana da shekaru, girman jiki ke babu, Ita kuma wannan yarinya ce da gaske, Gata kyakkyawa itama, ga wani ƙato mai manyan kumatu, da mazannai, Namiji ne baƙi wulik, yana tafiya tsokokin Jikin shi na motsawa, hatta ƙirjinshi acike yake kamar na mace, tashin hankali akwai gwarama fa,

a hankali Danish Ya sanya hannayen shi biyu ya sauke azeeza daga saman wuyan shi, Ya ajiye ta ƙasa, Yanayin fuskar kowannan su Ya canza, Lokacin da Sabbin prisoners ɗin suka kammala shigowa ciki Su Goma sha takwas ne, Sanye Cikin Uniform jajaye kalar nasu Parveen, A jere suka tsaya cikin ɗakin kamar masu jiran abasu Umarni, Kallon kallo su ke ta yi a tsakanin su dasu Deeja, Kowa Yasha Jinin Jikin shi, A hankali suka soma Jin takun tafiyar mutun daga can saman stair ɗin, Da sauri Su angel suka kai idanuwansu kan Mai shigowa bakowa bace face*TSOHUWA ZAFREEN*cikin shigarta ta jajayen Kaya Ta rufe ko'ina na Jikinta, Idanuwanta kaɗai ne awaje, Yayin da hannayenta ke a ruke da sandar ta, daga bayanta Giants ne kusan su Uku, Gabza gabza, Masu ƙirar Samudawa, suna ƙarasa saukowa Cikin ɗakin, Da sauri Danish Yace masu Parveen su gaishe ta, Atare suka ɗan russina Cikin girmamawa suke gaishe ta, Wani abun mamaki Mutun ɗaya ce bata russina mata ba, Saboda ƙarfin hali irin na angel hada goya hannayenta saman ƙirjinta, Fuskarta babu annuri, don ta gane cewa itace tsohuwa zafreen, Ba ta yi tsammanin zata ankara da ita ba, Sai ji tayi tace"Ke baki Iya gaisuwa bane"? Cikin ƙarfin hali angel tace"Na iya, Ina kwana,"

Al'ajabi ne ya kama Zafreen, Hankalin Danish kuwa idan yai dubu toh ya tashi, da ido yake yi ma angel magana akan ta duƙa ta gaishe da ita, amma ƴar tahalikar nan sai tayi kamar bata gan shi ba, hada ƙoƙarin ɗaure fuska idonta na kallon ƙasa,

Da kakkausar Murya Tsohuwa zafreen tace"Ki gaishe ni kamar yarda sauran ƴan uwanki suka yi mini" Cikin jin fargaba da ƙarfin hali angel tace"wuya na ke ciwo, bazan Iya russina kai na ba, amma ki gafarce ni"

Tsabar mamaki yasa Idon kowa ya koma kan Angel, Hatta Giants dake a bayan Zafreen Acike suke da al'ajabin maganar Angel, Idan ka kalli fuskarta zaka ga ta ɗaure ta tamau, kuma babu alamun wuyan nata na ciwo, ita kanta amma a firgice take, saboda wani irin mugun tsora da take ji, kuma da gangan taƙi russina mata, Saboda ba ta yi Niyya ba ne, don bata ga dalilin da zaisa ta ƙasƙantar da kanta wurin gaishe da tsohuwa Zafreen ba.

Jinjina kai tsohuwa zafreen tayi babu alamun ta fusata, Sai ma ta miƙa mata hannu don su gaisa, a ruɗe angel ta kalli tafin hannun zafreen dake a sanye cikin jar safa, Wani irin fagaba taji

"am happy to see your face, my granddaughter, Ƙwarin gwiwarki ya burge ni, tun da nake a duniyar nan ban ta6a ganin mahalukin da baya jin shakkar Yi min magana irin ki ba, ga ki ƙarama Kamar insa ƙafa in take" Jin wannan magana yasa angel taji hankalinta ya ɗan kwanta, har ta samun damar ɗaura hannunta acikin na tsohuwa tsaffin, Sosai ta ruƙe hannun angel acikin nata, Kafin daga bisani ta sakar mata hannunta,

Cikin ƙasaita Ta Juya baya ta kalli Giants da ta zo dasu, Da hannu ta yi masu magana ba tare da ta furta musu a baki ba, Yatsu Biyar ta watsa musu sau biyu, Gaba ɗaya su angel suka shiga ruɗani sunyi tsammanin wani mugun abun zata yi musu sakamakon Abunda Angel tayi mata, Amma sai suka Giant Sun Kalli Sabbin prisoners da suka zo dasu, Da hannu Suka nuna mutun biyar na farko da suka fara shigowa, su ka yi musu alamar su tsaya a ɗakin, Sauran Goman Cikin su Da hannu su kayi musu alamar su wuce su tafi, A matuƙar ruɗe Su angel suke kallon su Cike da mamakin Ina za'a kai Mutun Goma da Giants suka ware? kenan an fasa ajiye su a ɗakin su? can kuma ta tuna da maganar da Batool ta ta6a faɗa mata na cewa Akwai wasu 6angarorin da prisoners suke rayuwa a gidan kurkukun basu ka ɗai bane, wata'ƙil can za'a kai su.
Chapter 120 · 0% Book details