Sashe 35
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read
Dawowa batool ta yi wurin angel don taji idan ta yi bacci, a gefen gadonta ta zauna, Cikin sanyin murya tace"sister kinyi bacci"
Hannu angel tasa ta yaye bargon da ta lullu6e kanta da shi, fuskar nan tayi jawur ta kumbura, daƙyar take iya kallon fuskar batool,
Hannu batool takai tare da shafa fuskarta, Cikin sanyin murya ta soma magana" i know we don't know each other that well, but i'm still worried about you, nasan irin raɗaɗin da kike ji acikin zuciyar ki, bazan iya yaye maki shi ba, amma abu ɗaya nake so in tunasar da ke, duk abunda haƙuri bai baka ba, to rashin haƙuri bazai ta6a baka shi ba, tsohuwa ce ta ta6a faɗa mana haka," shiru ta ɗanyi na wani lokaci, angel na sauraronta kafin taci gaba da cewa" yau kika tsinci kanki acikin kurkukun nan ni kuwa tun ban mallaki hankali na ba nake acikinsa, bansan kowa nawa ba abun da nasani kawai tsohuwa ce ta raine mu........" bata kai ƙarshen maganar ba, cikin shessheƙar kuka angel tace"bazan iya jure zama acikinsa ba, cewa fa ta yi daddy na ya mutu, yanzu ni marainiya ce amma ae ina da dangi masu ƙaunata aunty aneelerh tana so, mommyna adama tana so na, don me za'a kawo ni gidan marayu"? daƙyar take magana saboda yanayin da take ciki,
"bazan iya amsa tambayarki ba, amma shawarar da zan ba ki shi ne ki bi komai a sannu, idan kika ce zaki bi ta ƙarfi da yaji don ki bar cikinsa to kuwa kece a wuya domin kuwa ni tun da na taso a cikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA yau tsawon shekara da shekaru banta6a ganin hanyar fita daga cikinsa ba, babu wanda yasan ta hanyar da aka shigo da shi, balle kuma yasan hanyar da zai fita daga cikin sa, sa'annan duk wani motsin mu a tafin hannunsu yake suna kallon mu, kewaye ne kaɗai idan kika shiga basa iya ganin ki........"
Cikin rashin fahimta angel tace"Idan har dagaske orphanage home ne meyasa xasu ƙuntata rayuwar mutun babu shige babu fuce kenan ko makaranta mutun baida ikon zuwa? Gaskiya bazan ta6a yarda da gidan nan ba......."
Batool tace"bana son muja zancan nan da tsayi, kamar yadda ba zaki fahimce ni ba, nima bazan iya fahimtar ki ba, saboda dukkan mu cikin ruɗani mu ke, abu ɗaya zan sanar dake GIDAN KURKUKUN ƘADDARA ba gidan cutarwa bane, saboda ni tunda na taso a cikinsa ba'a ta6a cutar dani ba kuma banga an cutar da wani ba, sai dai abu ɗaya ne da ya ke ci mun tuwo a kwarya shi ne kullan da a ke yi mana, ba ko'ina bane muke da ikon taka ƙafarmu ba acikinsa, najima ina tunanin ya wajen sa yake? Saboda ni ban ta6a fita daga cikinsa ba,"
Shiru angel ta yi batare da ta kuma cewa wani abu ba, saboda har yanzu tana ɗan jin jikinta ba daɗi, amma tabbas tana da tambayoyi dayawa da suka cunkushe zuciyarta, Dama gidan marayu bibiyar rayuwar mutun suke yi idan suka ga iyayen shi sun mutu sai su sato shi zuwa cikinsu? Meyasa batool tace sau ɗaya ake basu abinci a rana kamar yadda ta faɗa mata ɗazu! Meyasa za'a haɗa maza da mata a ɗaki ɗaya? Meyasa mutanan dake kawo masu abinci su ka yi 6adda kama!? Meyasa ba'a shige da fuce acikinsa? saboda me a ka yi masu iyaka da komai na cikinsa? Tabbas kuwa akwai wata maƙarƙashiya da ake shiryawa acikinsa, kodan saboda wannan tambayoyin da suka toshe kwakwalwarta, dole ta sanya nutsuwa don ta gano komai dake wakana,
"Zanje na kwanta, Amma kafin nan i naso ki faɗa mun sunan ki, duk da naji ɗazu kamar tsohuwa ta ambace shi, sai dai ban ruƙe ba," muryar batool ce ta katse mata zancen zucin nata,
Ajiyar zuciya angel ta sauke kafin tace"Sunana ANGEL ke fa?" batool ta bata amsa da cewa"Ni sunana BATOOL inaso ki É—auke ni tamkar Æ´ar uwarki, kuma ina so ki saki jikin ki acikin mu, ta hakanne zaki samu duk abunda ki ke so,"
"Kin wahaltu sosai yau, ki samu ki yi bacci, takai ƙarshen maganar tare da jan bargo ta lullu6e fuskar angel da shi,
"Sleep well my lovely sister" ƙasa ƙasa da murya angel ta furta mata"thank u, Sister" murmu shi batool tasaki ba ƙaramin daɗi taji ba, da angel ta kira sunanta da sister, wuce wa tayi zuwa nata gadon ta kwanta, kamar daga sama ta jiyo muryar hannah"kin gama kula da jinjirar ta ki? Tsoki batool taja" mind ur own business" tana faɗin hakan bata ƙara tanka mata ba,
Kowa ya runtsa a daren ranar banda mutun ɗaya! Dama taya zata iya bacci? ya yin da zuciyarta ke a cunkushe a ƙuntace da rashin mahaifinta, duk da har yanzu bata gasgata kalaman dattijuwar nan ba, ita dai tana ji aranta daddyn ta he's still alive! kuma taci alwashin duk runtsi duk wuya sai ta nemi hanyar guduwa daga cikin kurkukun ƙaddara, ni dai nace Allah ya ba mai rabo sa'a,
Ataƙaice cikin ƴan kwanakin nan ba irin haukan da angel ba ta yi masu ba akan su fitar da ita daga cikin kurkukun amma duk a banza, babu mai saurarenta acikinsu batool ce kaɗai ke lallashinta, duk ta bushe ta rame dama ba ƙiba gare ta ba, yadda kasan ɗiyar roba haka ta koma cikin sati ɗaya kawai, duk ta fita hayyaci kuma taƙi sakin jiki da su, musamman mazan haushin su take ji, saboda wannan Danish ɗin da basa jituwa da shi, ta tsane shi kamar mutuwarta shima haka ya tsaneta ko kallon arziƙi bai haɗa ta da shi, ko fira suke yi ta sanya masu baki to ya gama magana, ita kallan ɗan iska ta ke yi ma shi saboda doguwar sumar dake akan shi ita a ganinta ta ya yana namiji xai tara suma? tsayin sumar shi har ya kusa taddo nata, gaba ɗaya dai haushin mazan take ji saboda an haɗa su rayuwa a wuri ɗaya sam bata so ko kallonta su na yi ae ita a wurinta iskanci ne hakan, abunda bata sani kwata kwata basu da feelings a tare da su, suna ɗaukar kansu tamkar jinsi ɗaya da matan, ita ce kawai ta sanyawa ranta hakan, bakomai ya ƙara ɗaure mata kai ba fa ce rashin barin su yin ibada, batool ta sanar da ita cewa basu da addini, duk wanda ke rayuwa acikin kurkukun ƙaddara baida addini, rayuwa kawai suke yi tamkar arnaku ko sunan Allah basu ambato acikin maganar su, ba sallah ba sallati, bama su san yadda akeyin ta ba, dokar prison ɗin ce ba'a ibada acikinsa, wani irin kurman kurkuku ne, baka sanin lokaci dare ne kaɗai idan ya yi suke ankara saboda hasken ɗakinsu da ake ɗaukewa sai kuma idan safiya ta yi sun ta shi daga bacci, ita kanta angel ɗin ta ta6a gigin yin sallah, duk da basu da hijabi, ranar da tayi alwala ta yafa bargon lullu6arta da sunan za ta yi sallah, zagaye ta su ka yi suna kallonta da mamaki don basu san menene take yi ba, da zarar ta ɗaura niyya zata kabbara, sai ta dinga jin kukan mahaifinta, idanuwanta su dinga nuna mata fuskar tajuddeen wuta na ƙone jikin shi, gaba ɗaya take rikicewa ta gigice ta dinga kuka ire iren irin wannan gane gane da take yi yasa ta daina yunƙurin yin sallar, abun yana affecting ɗin ta
Yanzu dai ta zubawa sarautar Allah ido, ta daina haukan guduwa daga cikinsa tun da ta ga babu hanya, amma fa bawai hakan yana nufin ta haƙura ba, tana nan akan bakanta! ta lura cewa idan har zata cigaba da borin haukan da take yi masu tofa bazata ta6a samun nasara ba, wannan dalilin ne yasa ta nema ma kanta maslaha, tayin rayuwa cikin salama don ta samu damar yin bincike ta gano ainihin sarƙaƙiyar dake acikin Kurkukun ƙaddara, don tun daga kan ma'anar Sunan kurkukun fassara ce me zaman kanta, Kuma kullum tana cikin yin azhkar na safe dana mare ce, wanda daddynta ya koya mata, har tsakar dare bata runtsawa xama take yi tsakiyar gadonta, ta ɗaga hannayenta sama tana jera addu'o'i akan Allah ya kawo mata mafita acikin rayuwarta,
*Boss Batureâœï¸ðŸ’‹*
*After some weeks*