← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 179

Sashe 73

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsakiyar ɗakin Angel Ta tsaya tana bin Ɗakin tsohuwa da kallo, Abun mamaki abun al'ajabi, Bakomai bane aciki face Shufke sufken fulawowi,Ta ko'ina tamkar ɗan garde, Sai wasu tsoffin Kujeru guda Biyu suna fuskantar Juna, tsakiyarsu table ne mai ɗauke da Tea pot, da ƙananun Kofina guda Biyu, bayansu babu wani abu na furniture, Gado ko katifa,

Bayan ta kammala Kallon Cikin ɗakin na tsohuwa, Ta wurga idanuwanta kan tsohuwa dake yunƙurin zama saman ɗaya daga Cikin kujerun guda biyu dake fuskantar juna,

Muryarta angel ce ta katse mata hanzarinta da cewa"ina kayan É—akin suke? Naga babu gado ko katifa? A ina kike kwana"?

Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa tasaki, Mai matuƙar sautin gaske, Angel tuni tasha jinin jikinta, Muryar tsohuwa ashaƙe tace"Ƴar nan Badai Iya tambaya ba, Dama ganin kwakwaf kika zo Yi mini acikin ɗakin nawa? Keda kika ce Magana zamuyi ae kamata Yayi ki zo ki zauna ga kujera har ma da shayinmu na tsoffi in zuba maki musha don muji daɗin tattaunawa" Takai ƙarshen maganar tana nunawa angel kujerar da hannunta,

Jikinta tamkar na wadda aka zarewa Laka haka Taci gaba da tafiya Ta nufi kujerun Ta shiga Ciki ta zauna, tana Bin tsohuwa da kallon Ban yarda dake ba,

Ƙarasa xama saman kujerar tsohuwa Tayi, a yayin da suke fuskantar Juna ita da angel, Ido cikin ido suke Kallon juna,

"Ina sauraronki wata magana ce kikeson tattaunawa dani"? Ta yi tambayar a ƙagare da son ji,

Angel da ƙarfin hali tace"Tambayoyi ne nake son Yi maki, Ina fata zaki amsa mani" Wani irin kallo tsohuwa ta jefa mata, da mitsi mitsin idanuwanta,

Cigaba da magana angel tayi"Badan Hali na ba, Alfarmace nake nema awurinki, duk da nasan zaiyi wuya ki amsa mini tambayoyina, bansani ba ko yin hakan ya sa6awa dokar Prison"

Gajeren murmushi tsohuwa ta saki, kafin tace"A dokar gidan kurkukun ƙaddara, Ba'a ba mu damar Yin magana da prisoner ba dangane da abunda ya shafi Kurkukun, Yin hakan babban laifina wanda hukuncinsa mutuwa ne.........." aruɗe angel ta ɗan zaro ido tana kallonta, Tsohuwa tace"Kinga kuwa babu ta yadda za'ai In iya amsa maki tambayoyinki kodan saboda in tsira da raina"

Angel tace"Amma ae babu mai ganin mu, Daga Ni sai ke ne acikin ɗakin nan, Babu wanda zai san anyi" Cikin sigar wayau angel ta yi maganar, hakan ba ƙaramin dariya yaba tsohuwa ba, ganin ƙaramar yarinya na neman raina mata hankali, su da suka ga jiya suka yau

"Mu sha Tea mana, " tayi maganar tare da kai hannu ta É—auki tea pot, tana tsirara musu ruwan tea Acikin Cups,

"Ko kin zuba bazan Sha ba," acewar angel, kallonta tsohuwa tayi"saboda me"?
"Ban yarda da duk wani abu da zai fito daga gare ki ba,"
"Amma meyasa Æ´ar nan"?

"Saboda Ina kokwanto Akan shayin da da zaki bani, Shekaran Jiya da kika ba su batool apples Sunyi bacci Na tsawon yini guda batare da sun farka ba, Har safiya tayi, ina da tabbacin cewa silar apples ɗin da kika basu ne, Shiyasa nake tsoron in sha tea ɗin nan, wata'ƙil kinsa Poison aciki,"

Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace"Da ace naso kashe ki da tuni na aiwatar da hakan, kada ki manta kina acikin ɗakina ke kaɗai, Koda sandar hannu zan Iya cutar dake, ƴan uwanki kuma dana bawa Apples Taimakonsu Nayi saboda bani da ikon da zansa Giants su dawo masu da abinci, Shiyasa na baku Apples ɗinmu na gidan kurkukun ƙaddara, Domin kuyi bacci Har gobe Ta yi saurin zagayowa ko kun samu Ku ci abinci" dariya angel ta ɗanyi Tare da cewa"Hakan Yayi kyau, yanzu dai tun da bakyaso In tambayeki agame da kurkukun ƙaddara, Inaso Nayi maki tambaya biyu bata Cikin kurkukun bace...."tsohuwa tace "ina sauraronki"

"Gidan Kurkukun ƙaddara A Cikin Nigeria Yake? Sa'an nan kince Mutum baya ta6a kasance Acikin kurkukun nan dole sai in na Jininsa ne Ya sadaukar da shi, Abunda da nake so In sani, Na jinin naka daya sadaukar dakai Kamar wa kenan"?

"Kin manta abunda na faÉ—a maki kenan? kiyi mini ko wace irin tambaya amma kada Ki tambayeni game da gidan kurkukun nan....." tunkan takai karshen maganar angel ta katse ta da cewa"Amma ae ba'a Cikin kurkukun Nayi maki tambayar ba, Kawai ni inaso insan a wace nahiya Yake, Sannan Na jininka da zai Iya sadaukar dakai Kamar wa kenan"?

Tsohuwa bata amsa mata tambayarta ba, sai da ta fara miƙa hannu ta ɗauki kofin da ta zuba shayi acikin shi, takai bakinta tana kur6arshi kusan sau uku, Angel dai ta zuba mata ido, bayan ta Ajiye kofin saman table ɗin, Tana faman mulmula baki tace"Shayin da daɗi, Ki jaraba sha mana" girgiza kai angel tayi"Na ƙoshi, ni dai kawai ki amsa mini tambayata" dariya tsohuwa tayi"Ban ta6a ganin yarinya mai wayau da kaifin basira ba irin naki, Gaskiya Iyayenki Sun Iya haihuwa gaki Kyakkyawa Kamar ke kika ƙera Kyanki,.." ɗaure fuska angel tayi ganin tsohuwa Na ƙoƙarin Kaucewa Tambayarta, ta hanyar canza wani zancen,

Rai a6ace tace"ba wannan na tambayeki ba, Ki bani amsar tambayarta,"

Jinjina kai tsohuwa Ta yi idonta acikin na angel tace"idan na baki amsar tambayarki, Ni kuma me xaki bani? Kinsan ance gwammanti bata aikin banza" kallon rainin wayau angel tayi mata"Amma ae kinsan bani da abunda zan Iya biyanki da shi ko?, Ni dai kawai ki amsa mini tambayata"

Tea pot tsohuwa Ta ɗauka ta ƙara tsirara ruwan tea ɗin acikin cup ɗin gabanta, kafin ta ajiye pot ɗin ta ɗauki kofin takai baki tana sha" Sai da ta kur6e shi duka ta sauke kofin saman table, Tukunna tace"Tambaya ta farko, Gidan kurkukun ƙaddara Ni kaina bansan awace Nahiya yake ba, Abunda na sani shi ne ba'a Cikin kowace ƙasa Yake ba, mashin ko mota bazasu Iya kawo ki cikin kurkukun nan ba"

aruÉ—e angel ke kallonta, sai da takai karshen maganarta angel tace"Amma Ni lokacin da za'a kawo ni acikin mota aka É—auko Ni, idan har zan Iya tunawa" dariya tsohuwa Ta saki,

"iya saninki kenan, A mota aka Cafko ki, Amma Bayan nan bazaki Iya tuna Ta Cikin ina aka ƙaraso dake nan ba," shiru angel ta yi Zuciyarta cike da was wasin maganar tsohuwa, Gani take kamar ƙarya take Yi mata,

Muryar tsohuwa ce ta katse mata Zancen nata da cewa"Tambaya ta biyu, Na jinin ka da zai Iya sadaukar dakai, Mafi rinjayen sadaukarwa Iyayene waÉ—anda suka Yi silar zuwan ka duniya sune suke sacrificing É—in É—ansu, Uwa Ko Uba, Bayansu Kuma sai Cikin Blood relatives É—inka, Domin kuwa Bare bazai ta6a Iya sadaukar dakai ba"

A matuƙar kiɗime angel ke kallon tsohuwa, Muryarta har rawa take yi wurin furta"Iyayen mutun? uwa ko Uba? Anya kuwa zan Iya yarda da maganarki? Duk irin ƙaunar dake a tsakanin Iyaye da ɗansu Zasu Iya sadaukar dashi zuwa ga wannan ƙuntatacciyar rayuwar? To Meyasa zasu Yi hakan?

Fuskar tsohuwa É—auke da murmushi tace"Kina mamaki ne?, dama nasan zaiyi wuya ki yarda da magana ta, Yanzu dai Ina sauraronki, Idan akwai tambayar da kike da ita, Ki faÉ—a mini kafin in tafi"

Angel dai ta jinjina maganar tsohuwa abun Ya tsaya mata arai, ya cunkushe kwakwalwarta, Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Tambaya Ta ƙarshe da nake so Inyi maki, Mu prisoners dake rayuwa a gidan Kurkukun ƙaddara, Jinsi ɗaya ne? Dukanmu ƴan nigeria ne? Naga da yawan mu kamar fararen fata ne,

Tsohuwa tace"meyasa Ki kece haka"?

Angel tace"saboda Sam babu kamanceceniyar Jinsin baƙar fata atare da mafi rinjayenmu, Misali Kamar danish da Parveen da Javed Sun fi kama da ƴan ƴankin Asia, Azeeza Kuma kamanninta sak da European, Ita kuma batool tafi kama da Jinsin Larabawa, idan muka koma 6angaren Hanna da Hibba, sun fi kama da buzaye Ƴan ƙasar niger....." ɗaya bayan ɗaya saida angel ta korawa tsohuwa Bayani adangane da Jinsin da kowannan su take hasashen yana kama da shi, takai ƙarshen maganar, a ƙagare da son jin amsar da tsohuwa zata bata,

"Lokacin da kina atare da Iyayenki, Mutane da wani jinsi suke kwatantaki"? Tsohuwace ta jefa mata tambayar yayin da take sakin murmushi,

Yatsina fuska angel ta yi tare da cewa"Sun fi tsammanin Ni balarabiyace wasu kuma baturiya, amma asalin mahaifiyata half cast ce, auntyna ce ta faɗa mini cewa kakata mace balarabiyar ƙasar egypt ce"

Tsohuwa tace"Kinyi kyan kai, Wannan tambayar da kikayi mini, Kina da amsarta ahannunki, ina fata zaki tashi ki tafi Cikin ƴan uwanki tunda na amsa miki tambayoyinki," maƙe kafaɗa Angel tayi alamar bazata tafi ba

"Korata kike Yi daga ɗakin ki? Tsohuwa tace"a'a kawai dai Akwai inda nake son xuwa ne" Mamaki akan fuskar angel tace"ta ina xaki bi ki fita daga Cikin ɗakin nan naki bayan naga babu ƙopa, Koda yake ba abun mamaki bane, ae naga kafin ma in shigo Ciki, Kincanzawa ɗakin suffarshi duk don kada In yi maki leƙen asiri" tuntsirewa tsohuwa tayi da dariya, Itama angel ɗin dariyar tayi, sai da suka kammala shan dariyarsu kamar wasu ta6a66u, bayan sun tsagaita da yin dariyar angel tace

"Na jima inaso in tambayeki, Ya akai kika san Tarihin rayuwata? Kinsan komai dangane dani, Bayan haka kuma inaso insan asalin sunanki, Daga kin amsa mini waÉ—an nan tambayoyin xan Tashi intafi Cikin Æ´an uwana"

Tsohuwa bata amsa tambayar ba, har sai da ta ɗauki tea pot ta ƙara zuba ruwan shayi a kofi ta kur6a sau biyu, Sannan ta ajiye kofin ta soma magana atsanake,

"Amsar tambaya ta farko, Duk yaron da aka sadaukar agidan kurkukun ƙaddara, Muna bibiyar rayuwarshi ne tun Yana acikin Cikin mahaifiyarshi, Har zuwa lokacin da zata haife shi, zamuyita bibiyar rayuwarshi da zarar yakai shekarun da muƙe buƙatarsa To babu makawa xamu ɗauke shi ne...."
Chapter 73 · 0% Book details