Sashe 105
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lokacin da kuna bacci, Giants suka shigo da su, hada new metal beds da boxes guda biyu, ina expecting din sabbin prisoners xa'a kawo mana" Danish ne ya kora mata bayani, Ganin yadda take bin ko'ina na toilet din da kallo yasan dole ta buƙaci jin daga ina aka same su,
Ko kaɗan bata yi farin Ciki da ganinsu ba, Ita fa a halin yanzu komai na kurkukun ta tsane shi, abu ɗaya ne idan aka daina Yi musu xata so shi harma ta haƙura ta rungumi ƙaddararta, su cigaba da yin rayuwarsu Har Illah masha Allahu, shine a daina ɗaukar ƴan uwansu ana lalata rayuwarsu, sai dai tasan abune mai wuya, wannan dalilin ne ma yasa zata cigaba da neman hanyar da zata ku6utar dasu, domin kuwa babu fashi, Shiga Cikin kurkuku yanzu ta fara, Babu gudu babu ja da baya! ba'a halicce ta don ta zama raguwa ba, ita ɗin Jinin jarumai ce, masu dakakkiyar zuciya, waɗanda suka Yi imani da Allah batare da was wasi ba! duk da abunda ya faru da ita jiya, hakan baisa zuciyarta ta karaya ba, Sai ma taji kamar ana ƙara encouraging ɗinta akan taci gaba da bibiyarsu, a mutu ko ae rai, Kuma taci alwashin daga rana irin ta yau bazata ƙara sakin baki tayi bacci ba, Zata dinga raba dare biyu, kodan ta dinga kai kukanta wurin Allah, akan halin da suke aciki da kuma ƴar uwarsu batool!........" Ya jima yana kallonta ganin yadda numfashinta ke fita, ta ciccije la66anta, bakomai yajawo hakan ba face zancen zucin da take Yi, daga cikin zuciyarta,
"Angel!!" Firgigit tayi Jin muryarshi acikin kunnuwanta, wani irin kallo ta jefa mishi, da sauri yace"Ki É—an jira ni, Yanzu xan dawo" Bata amsa mishi ba, dama bai sanya ran zata tanka mishi ba, don ya lura yau mulki take ji.
Miƙewa Yayi da sauri Ya juya ya fuce daga Cikin toilet ɗin, badajimawa ba sai gashi Ya shigo ciki hannun shi ruƙe da robar ruwan daya yayyafa mata afuskarta ɗazu Cikin ɗaki, Bin shi da kallo tayi har ya ƙarasa gaban fanfo. ya zuƙunna Ya kunna shi, ruwa ya shiga kwararowa ya tarba robar, saida taci ka tukunna ya miƙe da azama ya dawo inda take zaune jikin bango, Ya zuƙunna agaban tukunyar fulawar,
ya ɗan saci kallonta ta wutsiyar idanuwanshi, harara yaga tana jefa mishi, ƙayataccen murmushi ya saki tare da cewa"Idanuwanki basu gajiya da yin harara"? Murguɗa mashi ƙaramin bakinta ta yi, tana faman hura hanci tace
"Bai shafe ka ba" Yace "its ok am sorry, abunda zan nuna maki ayanzu, sharaɗin shine, Koda ace zuciyarki ta ƙaryata hakan to kada ki amince just ki yarda kawai da duk wani abu da zan faɗi batare da kokwanto ba," bata amsa mishi ba, sai ma ta juya mishi ƙeya,
Bai damu ba, yaci gaba da cewa"yanzu inaso ki rufe idanuwanki", rai a6ace tace"saboda me xan rufe idanuwana"? Yatsina fuska yayi don tafara hayaƙa shi da tsiwarta,
"Kiyi kawai abunda nace miki, asannu zaki fahimce ni" Sai da taja guntun tsoki mai sauti, kafin ta runtse idanuwa nta, tana faman murga baki,
Bai san ya akai ya tsinci kanshi da kallon kyakkyawar fuskarta ba, sai yaga tafi yi mishi kyau a haka, duk da raunin dake akan fuskarta, sai ma suka ƙara mata kyau especially heart shaped lips ɗinta da suke abushe sun faffashe, kamar ta shafa musu jan baki pink, bakomai ya ƙara ƙawata fuskarta ba face gashin jagirarta masu tsayi dark brown dasu.
Jin shiru Danish baice ta buɗe idanuwanta ba, yasa ta harzuƙa ta yunƙuro zata wage baki ta zazzaga mishi masifa, Yai saurin cewa"Saura kaɗan" ajiyar zuciya ta ɗan sauke Cikin ƙagara da son jin me zai ce next,
"Ki buɗe idanuwanki a hankali," mutsu mutsu ta soma yi cikin wani irin yanayi ta ɗan waresu ta ƙara buɗesu kafin ta zarosu tana ƙarewa tukunyar fulawar kallo, abun mamaki abun al'ajabi, yauƙanannun fulawowin dake acikinta waɗanda sun jima da bushewa duk sun yagalgale sun lafe cikin ƙasar dake acikinta, ɗaya daga Cikinsu tagani ta miƙe ta bubbuɗe ganyayyakin jikinta sun wawware tayi matuƙar ɗaukar hankalinta, musamman launin Jikinta Ja da ya ciza, tsabar mamaki ya hana ta rufe bakinta, Idan ta kalli furan sai kuma ta kalli fuskar Danish,
Har dai tagaza jurewa tace"taya akai kayi hakan? Kamar a mafarki,"
"Ba shi yakamata ki tambayeni ba, wannan furen da kika gani ki ɗauka cewa ran mutun ne mai numfashi a jikin shi " Ya ƙarasa maganar tare dakai hannu ya shafa ganyen shi tare da cewa"Batool ɗinki ce, Our lovely sister, idan kika kalli furan da kyau, zaki ga yana da cikakkiyar lafiya ajikinshi, Launin shi ya ciza, hakan na nufin batul aduk inda take a yanzu tana acikin ƙoshin lafiya, Idan kuma ki gaka ganyen jikin furan Yana fitar da ruwa kamar zufa batare da an yayyafa mashi ruwa ba, that mean batool kuka take yi tana kewan ƴan uwanta, idan kuma ganyen ya kwanta jikin ƙasar dake acikin fulawar, to batool bacci take yi........" tunda ya soma kora bata jawabi, take kallonshi babu wasa a fuskarshi, Yadda kasan irin malamin duban nan, sai da yakai ƙarshen maganarshi tukunna tace"to idan furan ya mutu fa me hakan yake nufi? Maimakon ya bata amsa sai ya sadda kanshi ƙasa, tuni ta gane me hakan ke nufi wato mamallakin furan ya mutu kenan,
"Baka amsa mini tambayata ba," ɗagowa yai da kanshi ya ɗaura idanuwanshi akan fuskarta yace"idan ganyen dake ajikin furan Ya bushe ƙamas Ya tsotse ko ya fiffige, Hakan yana nufin mamallakinsa yana acikin mawuyacin hali, Idan kuma ganyen furan ya mutu, ko ansa mishi ruwa bazai tashi ba, ma'anar hakan mamallakinsa ya mutu baya araye" duk da bata gasgata maganarshi ba, amma sai da taji gabanta ya faɗi ras, muryarta na ɗan rawa tace"Shi...shi fa daddyna? Ina nashi furan yake? Taya za'ae in iya gane cewa yana a raye ko ya mutu?" aruɗe take jera mashi tambayoyin,
Kwantar mata da hankali yayi, "Ki natsu yanzu xan duba maki na daddyn ki amma kafin nan Kiyi mini alƙawarin cewa komai ki ka gani ba zaki yi kuka ba, idan kuma muka yi nasarar ganin furan daddynki Cikin ƙoshin lafiya, zaki bani abinci abaki. Nima in baki, a karo na ƙarshe kafin mu ƙauracewa juna,"
da yake a ƙagare take da son gani, da sauri tace mashi eh ta amince, yace to ta rufe idanuwanta, Bayan ta rufe su, Na ɗan wani lokaci, Yace ta buɗesu a hankali, Kamar wata sakarya haka take bin umarninshi, tunkafin ta ƙarasa buɗe idanuwanta ta soma hango fure Launin Kore, a gaggauce ta zare eyes ɗinta akan furan har zata fara Farin ciki sai kuma ta lura da naƙasar dake a ƙasan furen ya ɗan lanƙwashe alamar ba lafiya atattare da shi.
Wasu irin zafafan hawayene suka wanke fuskarta, Har wani zazza6i taji ajikinta, muryarta adabarbarce take faɗin" Danish Ya mutu ko? Naga ganyen kamar ya karye, Dan Allah ka faɗa mini, zuciyata zata Iya bugawa...." tsananin tausayinta ne ya kama shi ganin yadda tabi ta ruɗe, bakomai yake tunani ba face Iyayen shi, Shi da bai rayu dasu ba, kuma ba shi da tabbacin Suna araye ko sun mutu, shin dagaske sune suka sadaukar dashi? Anya kuwa shima yana da iyaye kamar kowa? A lokacin baya kafin zuwan angel bai ta6a tunanin wasu iyaye ba, gani suke Yi kamar tsohuwa itace komai na rayuwarsu, zuwan angel ne yasa suka fara tunanin suma ina iyayen su suke? Idan tana basu labarin irin ƙaunar da daddynta yake yi mata sai suji inama ace suma sunyi rayuwa da nasu Iyayen........."
Sautin kukan angel daya ƙaru ne yasa shi Barin yin zancen zucin nashi ya ɗago ya kalleta, ta wage baki sai kuka take Yi, baisan time daya saki murmushi ba, bai ta6a ganin ƙuruciyarta ba sai yau, da ta gasgata abunda shi kanshi baida tabbaci akanshi, kawai yana nuna mata ne don ya samu ya kwantar mata da hankalinta,
Ahankali ya sanya hannayenshi biyu Ya tallabo fuskarta, Yana ƙare mata kallo, hawaye ta ko'ina, Cikin sanyin murya yace"kin manta bayanin da nayi maki? Idan har furan bai bushe ba ko ya fiffige ya mutu, to mamallakinsa yana araye," Cikin shessheƙar kuka tace"Am...amma ae ya naƙasa, kai ba ka ga Ciwo a jikin iccen shi ba" Da lumsassun idanuwanshi ya ɗan kalli furan kafin yace"na gani, sai dai ba hakan yana nufin mamallakinsa ya mutu ba, sai dai ko karyewa ƙafarshi tayi sakamakon wani rauni daya ji, ko kuma wani ciwonne na daban ya same shi a ƙafar shi, kinji ma'anar raunin dake ajikin furen" hannu tasa tana share hawayenta hankalinta har ya ɗan kwanta,
"Kuma Allah idan har na gane cewa ƙarya kake Yi mini, to ka sani har bada babu ni babu kai, kuma kullum xan dinga zuwa ina duba furennin ina basu ruwa akai akai. Kodan kada su mutu, hakan kuma ba yana nufin na yarda da maganganun ka bane kawai dai zanyi amfani dasu ne" ƙiris ya rage ya saki dariya, jin wautarta, Ta wani 6angaren kuma yaji daɗi sosai, koba komai yasanyata farin Ciki, ya kuma bata aikin yi, duk da shima yana jin fargabar ranar da zata gane cewa ƙarya yake yi mata,
Taso ta tambaye shi furan aunty aneelerh kodan tasan awani hali take aciki, amma sai ta fasa don ta gaji da zama Acikin toilet ɗin, Gashi tana buƙatar Yin wanka sai dai tasan bazata Iya ba saboda ga6o6in jikinta dake yi mata ciwo,
"Muje mu ci abinci, Ko xaki yi wanka in taimaka maki"? Sakin baki tayi tana kallon shi jin abunda yace,
"Yanzu idan nace ka taimaka min inyi wanka? Kuma saika amince"? Fuskarta a É—aure tayi mishi maganar, baisan sadda ya furta"ae naga komai jiya so ba wani abu bane, nima ae kin ta6a gani na naked, bai kamata ki damu ba, har wankan ma sai mu yi atare,"
ras taji gabanta Ya faÉ—i, Ta zazzare gray eyes dinta tana kallonshi, Da sauri ya sanya tafin hannayenshi biyu ya toshe kunnuwanshi, saboda gudun tsiwar da zatayi mashi, shi kanshi baisan Ya furta maganar ba, su6ul da baka yai,