← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 179

Sashe 51

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nima kiyi mun addu'ar, inaso,"
Angel tace"Toh, ki kwanta kiyi bacci, zanyi maki addu'a," amsa mata tayi da toh , kafin ta kwanta,

Bayan angel ta kammala yin addu'ar ta ta sauko daga saman gadonta, tabi kowani gado ta tottofe su da addu'a, bayan ta kammala ta koma saman nata bed É—in ta kwanta,

Daƙyar ta samu bacci ya yi awon gaba da ita, har mafarkin danish sai da ta yi saboda ta sanya wa ranta shi sosai,

Slowly ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta, dishi dishi ta dinga ganin mutane kewaye da gadonta, sanya cikin baƙaƙen kaya hannunsu zaƙo zaƙo da dogayen akaifu, Kowanne ya ɗaga gudumar dake hannunshi da niyar rotsa mata kanta, A gigice angel ta zabura tana faɗin"Innallallahi wa'inna ilaihirraji'un" sautin dariya taji ta ko'ina acikin kunnanta, hannu tasa ta murza idanuwanta, tare da ware su akan mutanan da take gani, Su batool ne a jere, Sun nannaɗe hannayen rigunansu, Sai faman haki suke yi suna nishi kamar waɗanda suka sha gudu

"angel tun É—azu muke jira ki bamu wani training É—in, duk mun iya wanda kika koya mana" rubina ce tayi maganar,

Nauyayyiyar ajiyar Zuciya angel ta sauke, Ashe idanuwanta badai dai suke nuna mata ba, tayi tunanin wasu shaiÉ—anun aljanune suka kawo mata ziyara,

"Ki tashi Muje mu motsa jikin mu atare" Acewar batool,
Muryarta a disashe tace"Kun takuramun, ba haka ake ta shin mutun daga bacci ba, duk kun tsoratar dani" taƙarasa maganar tana jifarsu da harara hada murguɗa masu baki, gaba ɗaya suka tuntsire da dariya,

Muryar javed taji yana faÉ—in"Zata taso ko sai munzo mun cuccu6eta"? ya yi maganar yana naÉ—e hannun rigarshi, É—aya bayan É—aya take kallon fuskokinsu, zufa sai tsastsafowa take yi daga jikin su,

Ba ƙaramin burgeta su kayi ba, fuskarta ɗauke da murmushi tace"me yayi zafi javed, yanzu zan taso amma fa saina fara shiga toilet, "

Har suna haɗa baki wurin cewa"To kiyi sauri ki fito, muna jiran ki," ƙarasa janye bargon Jikinta tayi tare da saukowa daga saman gadon, Suka matsa mata hanya tabi ta wuce,

Walking slowly ta nufi ƙopar shiga makewayinsu, Harta ruƙe handle ɗin ƙopar da niyar ta buɗe sai kuma ta ɗan dakata tare da juyawa tana kallon Haris dake kwance daman gadonshi, idanuwanshi na fuskantar ceilling, da alamun damu atattare dashi, tasan bakomai ya jawo hakan ba, face rashin ɗan uwanshi danish don ta lura ba ƙaramin ƙaunarsa yake yi ba, Yau ce rana ta farka da tafara Jin tausayin haris, duk yabi ya ƙuntata kan shi saboda rashin danish, Allah sarki danish kowa Jikin nashi yake"?

Janye idanuwanta tayi daga kan haris ta mayar dasu kansu Parveen dake a tsastsaye, Tace"Har yanzu ba wani labari game da dawowar danish"?

Jinjina kai su kayi"eh, mu ma munyi expecting É—in idan muka farka daga bacci zamu same shi kwance a cikin mu, ashe ba'a dawo mana da shi ba"

In brittle voice Azeeza tace"nadamu da rashin É—an uwanmu, Jiya har mafarkin danish nayi, Allah yasa su dawo mana da shi, idan ba haka ba ni ko abinci bazan Iya ci ba" muryarta tamkar zata fashe da kuka,

Mubeen yace"nikaina daurewa kawai nake yi amma gaba ɗaya zuciyata a raunace take da rashin danish" yana rufe baki, Naufal yace"idan har jikin danish baiyi sauƙi ba, Zaiyi wuya su dawo mana da shi yau" zuciyarshi a karaye yae maganar,

"Ni abunda nake jima tsoro ma, kada a ƙi dawo mana dashi, kamar yarda ake yi mana a lokacin baya" Da sauri angel ta kalli fuskar batool da ta yi maganar, a yanayi na jin farga ba, tunawa tayi da tattaunawarsu da ita jiya a cikin toilet area, Inda batool take faɗa mata cewa"A lokacin baya duk wanda aka ɗauko acikinsu ba'a dawo dashi, He has gone forever," da sauri ta shiga girgiza kai tana faɗin"that's impossible, danish must be back, ku kwantar da hankalinku, babu abunda zai same shi, bana so inji kuna xancen cewa ba lallai danish ya dawo cikin mu ba, ' a harzuƙe takai ƙarshen maganar tare da buɗe ƙopar ta shige ciki, Koda ta shiga cikin toilet ɗin a jikin bango ta jingina bayanta, Idonta akan windown nan data kwallafawa ran son fasa ta,

"Da ace xan iya samun damar rotsa gilashin nan, dana yi ƙoƙarin binciko inda treatment room ɗin nan yake, kodan saboda inga danish, bawan Allah, ni tsorona ma kada ya rasa ranshi batare da ya kar6i kalmatusshahada ba, banaso ɗaya daga cikin su ya rasa ranshi batare da na musuluntar da shi ba, idan har hakan ta faru i won't forgive my self, tabbas zanyi asarar jinkirin da nayi,' cikin shessheƙar ku ka tayi maganar tuni hawaye sun soma sintiri akan fuskarta, ta ɗauki tsawn lokaci a tsaye batare da ta ta6uka komai ba, Har sai da tajiyo muryar Batul daga waje tana kwala mata kira"Angel! Angel! Kixo mu yi breakfast giants sun zo, ke kaɗai muke jira" Daƙyar ta iya ɗaga murya tace"Kada ku jira ni, ku fara kawai,"

Takai ƙarshen maganar tare da sanya hannayenta biyu Ta tu6e kayan jikinta asaman igiya ta ɗaura su, wanka ta samu tayi bayan takammmala ta mayar da kayan Jikinta,

Lokacin da ta fito daga Cikin toilet É—in, A zazzaune ta same su saman red Carpet, a tsakiyarsu wooden trays ne na kayan abincinsu, kowa ya hallara banda mutun biyu ita da kuma Haris dake kwance yana kallon ceilling, yadda tabarshi haka ta same shi,

Ba irin lallashin da batool ba tayi mashi ba akan ya taso yaci abinci amma ya kafe akan sai an dawo mashi da ɗan uwanshi, a dole suka ƙyale shi,

A hankali angel ta ɗaura idanuwanta akan su giants dake a tsaye kamar gumaka sun goya hannayensu saman ƙirjinsu,

Maimakon taje ta zauna taci abincin, sai gani su kayi ta nufi Inda su giants suke a tsaye, A ruɗe batool ta shiga kiran sunanta tana faɗin"Angel where are u goinig? Ki zo muyi breakfast" ko kallon inda batool take ba tayi ba, Tana ƙarasawa gaban giants, taci burki ta tsaya tana ƙare masu kallo, ga tsoronsu tana ji haka nan ta daure ta cije, ganin kanta take yi wata ƴar ƙaramar halitta agabansu, saboda a Halittar jikinsu, Gabza gabza ne ga ƙirar jiki mai matuƙar razanarwa,

"Pls angel kada kija mana muna zaman lpy, ki dawo ki zauna acikin mu muci abinci" hanna ce tayi maganar,

Yasmin ma tace"Angel, giants basa ji basa gani, Kada ki ce zaki tanka masu, suna iya yi maki illa" Kowa yasha Jinin Jikin shi, duk tana sauraron magiyar da suke Yi mata, amma taƙi koda juyawa ta kalle su, hatta haris dake acan kwance saman gadonshi, Ganin angel agaban giants Yasa shi yin zumbur ya miƙe zaune yana kallon Ikon Allah, Azeeza har ta fara kuka saboda tsabar tsoron kada su cutar da angel,

Sai da angel ta gama kalle su daga ƙasa har sama, Kafin tace"Ko dabba idan a ka yi mata magana tana responding ballanta kuma ku da kuke Jinsin bil'adama, Meyasa a koda yaushe Kuke yin 6adda kama idan zaku zo wurin mu? Why? u can't even talk to us? Saboda rashin gaskiya wato kuna tsoron muga fuskokin ku saboda gudun kada mu tona maku asiri nan gaba idan Allah ya ku6utar damu ko? Tayi tambayar cike da tuhuma tana kallon su, Ko motsi wannan ba suyi ba, Balle ma ta gane cewa suna sauraronta,

"Ko gunki bazai nuna maku yadda ake tsayuwa ba, agoya hannu saman ƙirji, ku dai ga ku nan wasu hamagawa da ku, to kodai ba mutane bane ku? Nafi zargin cewa ku ɗin Robot ne, wato sarrafa ku akeyi daga Can sama, ta yadda baku iya furta komai sai an baku izni koba haka ba"? Tayi tambayar a harzuƙe tana kallonsu,

Su batool sai faman lalla6a angel suke yi akan ta daina yi masu magana tazo suci abinci, amma Æ´ar tahalikar nan ko kallon inda su ke ba ta yi ba, sai ma cewa tayi"Su rabu da ita, Suci abincin su, Yau sai taga abunda ya turewa buzu naÉ—i, a tsakanin da giants dole suyi mata magana,

Atsiwace tace"Ba zakuyi mun magana ba? wlh duk ranar da wani ya kuskura acikin ku, Ya furta koda kalmar A ce, zan gano ko wanene shi koda bansan shi ba, idan har naji muryarshi awani wuri zan shaida shi ne, saboda Allah yayi mun baiwar tantance muryar mutane," A zafafe takai karshen maganar, ga yunwa tana ji amma taƙi zuwa taje taci abinci,

Ruƙe qugu tayi"meyasa baku dawo mana da danish ɗin mu ba? ina kuka kai mana ɗan uwan mu? Tsohuwa tace kune kuka zo kuka ɗauke shi"? Tayi maganar tana faman haɗiyar yawu,

Aiki fa ya ga angel , ita kaÉ—ai sai sambatu take yi kamar wata zautacciya,

Ganin taƙi zuwa taci abinci Yasa batool taje ƙarƙashin gadonta, ta ɗauko kwandonta, ta kwashe ragowar sauran abincin da suka Ci, da niyar ta ajiye ma angel da haris,

"Giants we are done," Javed ne ya sanar dasu, yayi hakan ne don su samu su tafi, kafin angel takaiga ƙure su, don in suka fusata, komai zasu iya aikatawa,

Ta gefen angel suka bi suka wuce, Tattara kayan Abincin su kayi a jera suka nufi benan, Ganin zasu tafi basu bata amsar tambayarta ba, yasa ta watsa da gudu ta riga su hayewa saman benen, a jikin ƙofar ta jingina bayanta tare da ware hannyenta, wato ta toshe masu hanyar sa zasu bi su fuce,

Tsayawa su ka yi a tsaye saman matattakalar benan, tunda suke aiki a prison É—in, basu ta6a ganin hatsabibiyar yarinya irin wannan da take agabansu ba, da ace tasan irin hatsarin dake gare su da bata yi gigin shiga huruminsu ba,

Kallon kallon aka soma Yi atsakaninta angel dasu giants, Hankalin su Batool yayi matuƙar tashi, duk suna a tsaye bakin benan sai roƙon angel su ke yi akan ta matsa ta basu hanya su wuce, ba iri magiyar da basuyi mata ba, amma angel ta maƙe kafaɗa akan bazata matsa ta basu hanya ba, Ita so take taga ikon Allah Shin giants zasu Yi mata magana akan ta basu hanya su wuce ko kuwa"?
Chapter 51 · 0% Book details