Sashe 60
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gallery ta shiga, ta lalubo tsoffin hotunansu tana kallo, Wani hoto ta buɗo wanda suka yi su uku, Ranar graduation ɗinsu akayi masu hoton a University of Hagen, dake a ƙasar germany, su uku su kayi hoton kowannasu yana asanye Cikin Graduation gown sunyi matuƙar yin kyau, Allah yayi halitta ta farko Aneelerh ce, A tsakiyarsu Benazir ce kyakkyawar balarabiya, Ta ƙarshe kuma wata aminiyarsu ce masha Allah, Matar akwai diri kamar ita ta ƙera kanta, kowacce da irin baiwar kyan da Allah yayi masu, sai dai kash gaba ɗayansu a halin yanzu ƙaddarar rayuwa tayi silar tarwatsewarsu,
A tsanake take kallon hotunan nasu, tayi matuƙar yin kewar aminnanta, bazata ta6a manta irin shaƙuwar da su kayi da juna ba, runtse idanuwanta tayi tana tuna wasu maganganun da suka jima suna yi mata yawo acikin kanta, ɗaya daga Cikin aminnan nata ne ta furta su a cikin text message da ta ta6a tura mata lokacin da take Cikin tashin hankali tace"Aneelerh bazan Iya jurewa ba, ko gaisuwata bai amsawa, bansan shi wani irin uba bane, ni dai banyi dacen iyaye ba, Yanzu haka da nake rubuta maki text ɗin nan, Ina akan hanyar zuwa airport wlh idan nabar ƙasar nan bazan sake dawowa Cikinta ba, tun da yace baison gani na, aneelerh agaban kowa Yaci mutunci na, agaban maids ɗin gidanmu, yayi mun korar kare hada tsine mun yayi kamar wani jahili shi baisan ƙaddara ba ne? Idan har na biyewa zuciya zansha poison ne in mutu........"
Sosai aneelerh ta fashe da kuka, lokacin da ta kammala tariyo abunda ya faru, A fili tace"Allah sarki Aisha! Bansan A ina zan ƙara ganinta ba, Allah ya kare ki aduk inda kike, ni shaida ce akanki, Ke mutuniyar kirkice, bana fata, ƙaddarar rayuwa tayi silar canzaki daga yadda nasanki, '
Cikin shessheƙar kuka aneelerh tace"Narasa Aisha saboda korar karan da mahaifinta yayi mata, na kuma zo narasa Benazir, duk da ita don san ranta ta gudu, daga baya kuma Narasa Mutun uku masu mahimmanci acikin rayuwata, " jefar da wayarta tayi saman mattress, Ta kifa kanta Jikin pillow, junaid tuni ya jima da komawa bacci,
Tasha kuka kafin bacci yayi awon gaba da ita, Wuraren ƙarfe 9 na safe, Mami ta shigo ɗakin Jikinta sanye da atampa , murmushi ta saki ganin yadda uwa da ɗanta suke ta sharar bacci, Girgiza kai ta ɗanyi "Jikana mai abun ban mamaki, dama nasan bai wuci nan ka gudo ba, wurin mommyn taka, bayan ka sace mun rigar mijina, Allah dai ya shirya mun kai,' Takai ƙarshen maganar, tare da ƙarasawa Cikin ɗakin agaban gadon aneeleerh ta tsaya tare dakai hannu tana ɗan bubbuga kafarta" Daughter baccin ya isa haka, Ki tashi muje muyi breakfast,"
Buɗe ido aneelerh tayi sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, koda ganin busassun hawaye akan fuskarta, sai mami ta ɗaure fuska"aneelerh when zaki daina kuka? Sai kace wata ƙaramar yarinya? Abu kaɗan sai kuka duk kin maida kanki wata sauna," rai aɗan 6ace tayi maganar, yayin da take zama gefen gadon idonta akan fuskar aneelerh,
Miƙewa zaune aneelerh ta yi, batare da tace komai ba,
"Fada mun me kuma ya saki kuka"? Muryarta a disashe tace"Mami kiyi hakuri idan kukana ya 6ata maki rai, nasan bakya son ganin zubar hawaye na, nima ba so nake yi ba, sai dai wani abunne ko nayi kokarin na danne saina kasa, idan ba hawayen na zubar ba, bana jin daɗi," yanayin yadda tayi maganar ba ƙaramin kashe ma mami jiki tayi ba ,
Ruƙo hannayen aneelerh tayi acikin nata"Aneelerh, kodai zaki ɗauki shawarar mahaifinki ne, ki koma abuja gidan Uncle ɗinki da zama? ina ganin kamar in kina acan zaki fi samun sauƙi acikin zuciyarki, amma zamanki anan sam babu cigaba," girgiza kai aneelerh tayi yi"Mami dan Allah kudaina yi mun maganar komawa gidan uncle da zama, ya kuke so nayi da rai na? A halin da nake Ciki, ku kaɗai nake gani inji sanyi acikin raina, indai nayi nesa da ku, bazan ta6a samun natsuwa ba" takai karshen maganar fuskarta a yamutse,
Mami ta fahimci halin da aneelerh take Ciki, dama tasan zaiyi wuya ta amince tayi nesa da su,
"Shikenan, bazan ƙara yi maki zancen komawa can ɗin ba, ina fata hakan yayi maki" jinjina kai aneelerh tayi alamar eh,
"Yanzu ki tashi ki shiga toilet ki wanke fuskarki sarkin kuka, Allah idan baki daina ba sai yaronki ya raina ki, ga shi nan yanzu shima ya fara zama irin ki, ko kallon banza mutun yayi mashi sai ya fara ta6e baki zaiyi ma mutane kuka," murmushi gefen fuska aneelerh ta saki, tare da juyawa tana kallon junaid dake kwance, har lokacin wuyanshi na sanye da cazbaharta daya sanya,
Dariya mami tayi don ita sai lokacin ta lura da cazbahar da ke sanye a wuyan junaid,
"Wayaga É—an Sarkin malamai," dariya sukayi atare, gwanin ban sha'awa,
Miƙewa mommy tayi"xan koma dining ki same ni acan ina jiranku,"
Amsa mata tayi da toh mami, kafin ta sauko daga saman gadon ta shige toilet, after some minutes ta fito tana gyara doguwar rigar material É—in dake ajikinta,'
Har lokacin Junaid Bai farka ba, tasan dole yana jin yunwa, hannu takai tare da ɗauko shi, aikuwa kamar ta tsunkule shi, Yaita kuka yana fadin shi bai gaji da baccin ba, tana dariya tace"Am sorry My baby Boy, breakfast zamuyi da zarar mun kammala, Sai ka koma baccin ka, daƙyar ta samu ta shawo kanshi Ya daina kuka, Toilet ta shiga da shi, ta yi mashi wanka, ta fito dashi sa6e saman kafaɗarta, ta nado shi Cikin towel, Gyara mashi Jikin shi tayi kafin ta sanya mashi riga da wando, rungume dashi ta fito ta nufi dining table, Mami ta hango a zaune tana Shan tea, Kujera taja ta zauna suna fuskantar juna da mami tace"ɗazu ban gaishe ki ba, My first love, Ina kwana mamina, ina fata kin tashi cikin koshin lpy," fuskar mami dauke da murmushi ta amsa mata da cewa"Alhamdulillah, my lovely daughter, Ya grand son ɗin nawa naga yana ta tur6une fuska uwa alkubus, halan tashinsa ki kayi daga bacci"? Takai ƙarshen maganar idonta akan junaid, dake zaune saman cinyar mommynsa, sai shan mur yake yi, yana hura hanci, Shi an takura mashi,
"Mami saboda fa ya ci abinci na tada shi, amma da yake shi baisan abun arziki ba, shine yake ta hura mun hanci,"
Mami tace"kwantar da hankalin ki, ae da zarar yayi arba da noodles zai wartsake" hannu mami takai tare da ruƙo plate ɗin dake shaƙe da noodles ta tura ma aneelerh agabanta,
Hannunshi har kerma yake yi wurin kokarin tsoma shi Cikin taliyar, da sauri aneeleerh ta damƙi hannun nashi tare da cewa"Baka ga akwai zafi ba? So kake bakin ka ya ƙone"? ta6e baki ya soma yi alamar zaiyi kuka, lallashin shi ta shiga yi"haba my baby boy, Fushi ba naka bane bari na baka da hannu na" hannu ta sanya ta soma ɗibowa tana bashi abaki yana Ci,
"Mami Ina abie? Ko har sun tafi"? Jinjina kai mamie tayi"tun yaushe kuma, tun bayan sallar asuba yace mun bazai dawo gida ba, daga can zasu wuce, "
"Shi ne ko ya jira muyi sallama dashi" rai adan 6ace tayi maganar, mami tace"sauri yake yi ne, idan mun kammala cin abinci sai ki kira shi awaya ki yi mashi Allah ya kiyaye hanya," amsa mata tayi da toh, daga haka suka Cigaba da cin abincin su,
*south korea🌹*
Seoul City,
Hajiya adama ce zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, A cikin katafaren Palourn gidansu, jikinta na sanye da doguwar cord lace milk colour, idanuwanta na a manne da farin glass medicated, Ta natsuwa tana daddana laptop É—inta dake asaman Table É—in gabanta, da alama Komai ya daidaita don yanayinta bai nuna tana acikin damuwa ba,
Gaba É—aya ta tattara kwandon hankalinta akan aikin da take yi acikin laptop É—inta,
Sautin Dirar motoci ta juyo acikin Apartment din nasu, dakatawa ta ɗanyi da daddana laptop din ta ɗago tana kallon bakin kofar shigowa falon, duk da tasan ba lallai In baƙin su bane tun da basu kaɗai bane akwai sauran mutanan dake Haya Acikin Ginin,
*â¤â¤â¤PRISONERSâ¤â¤â¤*
Uncel abdallah ne Ya shigo Falon, Hannun shi ruƙe da key ɗin motarshi, Suit ne ajikin shi, Miƙe wa Hajiya adama tayi fuskarta asake tace "Welcome back dear, I heard the sound of cars Coming in ko munyi baƙi ne"? sai da ya samu wuri ya zauna tukunna ya kalle ta fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Ni ne baƙon ae, fatan na same ki lafiya, Yau naga walwala atattare dake, Ga shi kin ɗau wanka kinyi kyau abunki,"
Ta6e baki ta yi "Ae tun da kayi mun albishir game da komawarmu gida, Nake ta sakin fara'a ni kaɗai abuna, Yanzu haka ma da kaganni a zaune, Ina duba kayayyakin da zan siyane na tsaraba da zanyiwa mutanan gida," takai ƙarshen maganar tare da kama hanyar zuwa kitchen tace"Bari na kawo maka Ruwa mai sanyi kasha"
"Da kanki Hajiyata? Ina mai aikin gidan take ne"? A sukwane ta Juyo tana bin shi da kallon bansan rainin wayau,
"Oh kamanta irin Korar da kayi ma Ajumma daga gidan nan, Saboda laifin da ba nata ba, Æ´ar baiwar Allah, dama burinka kaga ina shiga kitchen da girmana, ae yanzu hankalin ka ya kwanta, Hajiya adama ta zama kukun mijinta" Dariya Uncle abdalla Yayi"Matar nan kina sani nishaÉ—i, Abun alfahari ne mace ta girka ma mijinta abinci da hannunta yaci ya sanya mata albarka, Ta samu lada, Ni ae naga Cigaba sosai, da na kori wannan tsohuwar matar, Tun barinta gidan, kika daina shan Soju, gashi yanzu kin samu natsuwa kin dawo Hajiya adamar dana sani,"
Hararar wasa ta jefa mashi daga inda take a tsaye" korar ajumma da kayi ba shi ne yasa na daina shaye shaye ba, Da naso zan fita inje in siyo da kaina ne, Allah ne yayi silar shiryuwata, dama ba halina bane, tsautsayine da ƙaddara, da kuma damuwar da na shiga na rashin mutun uku masu mahimmanci acikin rayuwata.........." muryarta a karye takai ƙarshen maganar, da sauri tajuya ta shige Cikin kitchen,