← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 179

Sashe 74

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"hakan na nufin tun ina jaririya kuna atare dani? Kenan kune kuke sanyani duk wani mugunta da nake Yiwa daddyna"? Da ruɗu akan fuskarta tayi tambayar, tsohuwa tace"A'a, bamu bane, baƙin aljanine dake atare da mahaifiyarki, Yana matuƙar sonta, Kuma yana da zafin kishi, shine maƙasudin rashin jituwar Iyayenki, Ya tsani Mahaifinki tajudden yaso ya tarwatsa shi, Amma hakan ya faskara saboda Daddnyki mutunne maison yin ibada, bai wasa da azkhar, kuma yana yawan yin sadaka, sannan babbar kariyar dake atare dashi, Yana Yin nafilfilin tsakar dare, A lokacin da benazir ta haifeki, Baƙin Aljani Ya fita daga jikinta ya koma a jikin ki, domin ɗaukar fansa akan mahaifinki, yayi amfani dake wurin ƙuntata mishi, Amma A yanzu Baƙin Aljanin baya atare dake,

Angel fa ta shiga ruɗu, duk da tana kokwanton maganar tsohuwa, Bakasafai Take yarda da zantuttukan ta ba saboda sanin Cewa Ita ɗin Babbar maƙaryaciya ce,

"Kin tambayi sunana, Zaki iya kirana Da TAMIRA Shine Asalin sunana," Tsohuwa Na kai ƙarshen maganarta, Ta yunƙura ta miƙe daga saman Kujerarar, Da sandar hannunta ta nuna ma angel hanyar fita daga ɗakin, batare da musu ba, Angel ta miƙe ta nufi hanyar fita daga Cikin ɗakin Har takai bakin ƙopat fita, Muryar tsohuwa ta dakatar da ita,

"Shawarar Da nake so Na baki, Kada ki kuskura kice zaki Sanya naci akan sai kin gano ainihin ma'anar Kurkukun ƙaddara, domin kuwa daga ranar da kikasan ma'anarshi, Bazaki sake runtsawa ba, Kuma ba zaki sake Jin daɗin abinci ba, duk wani kingin jin daɗi da ya yi saura acikin rayuwarki, Zaki rasa shi ne! Wani irin mummunan faɗuwar gaba angel taji, Har saida ta dafe kinjinta saboda bugun da zuciyarta tayi mai sautin gaske,

Tsohuwa taci gaba da cewa"Ƴan uwanki suna farin Cikin kasancewarki acikinsu, Saboda Kin kawo musu canji acikin rayuwarsu, Ina fata zaki mayar da hankali wurin faranta musu rai, Amma fa kinsan da sanin duk ranar da kika Binciko ma'anar The destined prison, daga ranar daga ke har su, Zaku fuskanci matsanancin tashin hankali, Kuma daga wannan Lokacin bazaku ƙara Yin tozali da TSOHUWA TAMIRA ba, Zaku yi ta yin gwagwarmayar rayuwa ne atsakaninku, na gargaɗe ki ne saboda Ina sane da duk wani ƙudurinki nasan bin kwakkwafin Gidan kurkukun ƙaddara, Shiyasa na sanar dake irin matsalar da zaki jefa kanki da kuma ƴan uwanki" angel na ƙoƙarin Waiwayowa baya ta kalli tsohuwa taji an ingizata waje, Ƙopar ɗakin ta rufe,

Kamar an jehota ta faɗo ƙasa, Cikin ɗakinsu, har kanta saida Ya bugu,

Tun daga wannan Ranar Angel tashiga ruɗani, Kalaman tsohuwa sunyi matuƙar ɗaure mata kai, Tarasa Ina zata tsoma ranta taji daɗi, Kowa Saida Ya lura da canzawar da tayi, Sam tadaina shiga cikinsu, Gani take kamar Dukansu mutuwa zasuyi shiyasa take janye jikinta gudun kada sabon Yayi yawa ta yadda zata rasa kanta idan ta rasa wani acikinsu, Su batool duk sunyi tsammanin rashinsu Parveen Ne yasa ta canza ta shiga damuwa, Kullum cikin Lallashinta suke yi, Akan tayi haƙuri su koma kamar yadda suka ada, Daƙyar suka samu angel ta koma Yi musu wasa da dariya, Harma tana koya musu wasu wasanni donsu farantawa junansu,

Akwana a tashi Yau tsawon Sati Biyu kenan, Ba'a dawo musu da ƴan uwansu ba Har sun fidda rai da sake ganinsu, tun suna tambayar tsohuwa har sun gaji sun daina, kowa ya zubawa sarautar Allah Ido👀

Yau Tun da Suka tashi daga bacci suke ta jiran a kawo musu abincinsu suci amma shiru giants basu zo ba, Tun safe Har marece, Jikinsu duk Ya yi laushi, azeeza tuni ta fara Yi musu kukan yunwa, Lokacin da dare Ya ratsa hasken ɗakin Yayi duhu, Nan fa suka ƙara shiga tashin hankali ganin zasu kwana basu Ci abinci ba, la66ansu duk sun bushe, Ruwa kaɗai suke tasha tun safe, Cikinsu harya ɗaure, wasu daga Cikinsu hada amanshi su ka yi,

a ƙarshe suka haƙura Da abincin, Kowa Ya hau saman gadonshi ya kwanta, Cikin sa'a bacci ya ɗauke su, Ganin sun nutsa acikin baccin su yasa angel ta sanya hannu ta yaye bargon data lullu6e fuskarta da shi, Saukowa ta yi daga saman gadonta, Sumar kanta duk ta cukurkuɗe kamar ƴar mahaukaciya saboda rashin gyara, Cikin duhu take tafiya tana laluban hanya, Fitila taje ta ɗauko ta kunnata, Tana haske Saitin gadajensu Hannah, ganin babu mai motsi acikinsu Yasa tayi sauri Cikin sanɗa ta nufi sashen toilet ɗinsu, har yanzu bata haƙura da Ƙudirinta ba, Nason fasa gilashin nan, Alwashi ne ta ɗaukarwa kanta Koda zata rasa ranta saita Ga uban me ake aikatawa acikin gidan kurkukun, Duk da tana Jin fargaba akan irin gargaɗin da tsohuwa tayi mata, don a lokacin harta fara tunanin ajiye makaman yaƙinta, amma daga baya sai ta dinga jin tamkar ana tunzurata akan taje taci gaba da jaraba fasa gilashin zata Ci nasara, Zuciya da saƙe saƙe, gani take kamar idan ta fasa gilashin ta dira ta cikin tagar, zata samu damar zuwa wurinsu deeja ne, Harma ta dawo dasu Cikin ɗakin, Da yake sune damuwarta,

Tana shiga Cikin toilet ɗin, Taja ƙopa ta garƙameta da jamlock, A ƙasa ta sauke fitilar, ta ɗaga hannayenta Sama tana roƙon Allah Ya bata Ikon Fasa Glass ɗin a karo na karshe don daga yau ta sanyawa ranta cewa idan har bata fasa shi ba, ta gama zuwa tana shan wahala, zata haƙura ne,

Bayan ta kammala yin addu'ar, Da ƙwarin gwiwarta ta kai hannu ta rarumi bokitin ƙarfen, Sai da taja da baya ta watsa dagudu ta buga tsalle ta daki glass ɗin Da iya ƙarfinta na karshe, Amma wani abun takaici ko tsagewa Baiyi ba, kamar dai kullum haka taci gaba da bugun glass ɗin da bokitin amma Yaƙi nuna alamar ana bugunsa, saboda tsabar zufar dake tsastsafo mata ajikinta Tamkar wadda aka tsamo daga Cikin teku, Idanuwanta sun rune saboda wahala, Hannunta sai zogi yake yi mata, ga wani irin fitsari daya Matseta, da sauri ta jefar da bokitin gefe ɗaya ya gangara ƙasa, Tasanya hannu ta kwale wandon jikinta, Zuƙunnawa tayi a bakin magudaji tana fitsari, sai da ta kammala taje gaban fanfo tayi tsaki, tana kokarin miƙewa kwatam ta hango mutumin jingine da bango, Ya goya hannayen shi saman ƙirjinshi, Tun kafin ma ta ƙarasa juyawa ta gane kowanene, Sakamakon doguwar sumar kanshi data hango,

Muryarshi ce ta ratsa kunnuwanta,

"Can I give u a hand"? ras taji gabanta ya faɗi, azuciyarta tace"Danishi! Nashiga uku, kada ace ya ga abunda nake ƙoƙarin Yi, wayyo Allah na" rai a6ace ta ƙarasa juyowa tana fuskantar 6angaren da yake atsaye ya jingina bayan shi jikin bango, Rai a6ace ta nuna shi da yatsa"Wannan wani irin shashanci ne danish? Why zaka dinga faɗo mini Cikin toilet? yanzu da ace na tu6e kaya ina wanka ko ina wani uzirin Shikenan ka gane mini tsiraci na, Wlh bazan ƙyale ka ba" A fusace ta nufi bokitin data jefar ƙasa tasa hannu ta ɗaukeshi Ta daddage ta wurga mashi bokitin, Da sauri danish ya sanya hannayen shi biyu ya cafke bokitin a hannunshi, ɗagowa yayi da lumsassun idanuwanshi ya ɗaurasu akan fuskantar,

"Raunata ni kike so Ki yi? A ƙule tace"kashe ka zanyi " Cikin sanyin murya yace"Am really sorry, na kar6i laifina, kada ranki ya 6aci, daga yau bazan sake ba faɗo maki cikin toilet ba," yakai ƙarshen maganar a yayin da ya ajiye bokitin ƙasa, ya ɗago idonshi Yana kallon Tagar da angel ke ƙoƙarin fasawa,

Zaro idanuwanta ta yi ganin yana kallon glass window É—in da alama yaga abunda take Yi, muryarta na kerma tace"Nasan kaga abunda nake kokarin yi, So nake in fasa gilashin tagar nan, Saboda Ina da matsalar kwakwalwa, Tun lokacin da ina agidan daddyna kafin zuwana kurkukun nan, Na fasa gilassai bila adadin saboda Ni idan nayi tozali da gilas tsoro Yake bani, kuma hakan yana jaza mini matsala, Likita ma yace Idan ina yawan zama inda ke akwai glass zan Iya mutuwa" angel sarkin wayau, idanuwanta cike tab da kwalla takai karshen maganar, hada marairaice mishi fuska don Yaji tausayinta, ya kuma yarda da maganarta,

Danish bai kawo komai aranshi ba, har cikin zuciyarshi ya yarda da kalamanta, matsawa yayi kusa da ita, Ya sanya hannayenshi biyu ya tallabo fuskarta, Idanuwan su acikin na juna, Cikin sigar lallashi yace"Am sorry angel, don't cry pls, da kin faɗa mini tuntuni da na jima da sauke miki gilashin," ta6e baki tayi tare da cewa"Ae bazaka Iya ba, ko Ni nasha gwada cirewa amma na kasa, kullum saina sha wahalar," ta fadi hakanne don tasan Cewa danish bazai Iya ba, ita kanta da take da ƙarfi ta jaraba ta kasa balle shi da yake sai a hankali ba ƙoshin lafiya ba,

"xan jaraba in gani idan zan iya," yakai karshen maganar yana tattara hannun rigarshi, da sauri angel ta ɗauko mashi bokitin ta miƙa mashi, bakinta ƙumshe da dariya So take yasha wahala kamar yarda ta sha, Shima Yaji ajikinshi,

Girgiza mata kai yayi"bana buƙatar yin amfani da bucket, I will use my hands" dariyar rainin wayau angel tayi mashi"wlh bazaka Iya ba, Da hannu fa ka ce, haba dai, kai dai ka kar6i Bokitin inga iya ƙarfin ka," Bai saurareta ba, Ya tunkari Glass window din, Da yake Allah yayi shi da tsawo, Yafi angel tsayi ba sai yasha Wahalar yin tsalle ba kamar yarda take yi, Agaban tagar ya tsaya yana kallonta,

Angel ta ruƙe qugu, Tana jiran ganin Ikon Allah, Fuskarta ɗauke da dariyar mugunta,

hannayen shi biyu ya sanya yana shafa Jikin glass ɗin da ya yi uwar ƙura, ƙasan glass ɗin Ya ruƙo da yatsunshi, Ƙura ido angel tayi ganin glass ɗin kamar ya fara motsi, Gabanta ne ya faɗi ganin Danish ya daddage Ya 6a66ako glass ɗin tun daga tushen shi can cikin ginin dutsen da aka zura shi, Haka ya zaƙulo shi gaba ɗaya ya curo faskeken glass ɗin, Tashin hankalin da ba'a sama shi date,

Kanta Ya gama ɗaurewa, Ta zazzaro idanuwanta waje, kwayar idon kamar zata faɗo ƙasa saboda tsabar mamaki, Gaba daya tabi ta ruɗe ta rikice, Tarasa bakin magana sai bin shi da ido take yi kamar wadda aka dasa ma Aya,
Chapter 74 · 0% Book details