← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 179

Sashe 125

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yayin da su deeja suke Nan suna shan fira ita haris, Su parveen suna acikin toilet su shida kewaye da tukunyar fulawar nan, Duk sun zuƙunna suna kallon furennin, da alama Gulmace ta ciyo su abunda basu ta6a yi ba, abun ne Ya tsaya musu aransu, Ya hana zuciyoyin su sakat, Lamarin ƴar gidan daddy da Majnun Yasha musu kai,

"Wlh an cuce mu, Sai daga baya na dinga regretting kawo mana waɗannan Ciwon kan da zazza6in, mahaukacin yaron nan duk yadda na ƙwallafa rai akan son Cin cake ɗin nan saida ya lalata shi, Har Yau na gaza manta suffar ƙaton cake ɗin acikin idona" Parveen ce tai maganar rai a6ace,

Azeeza tace"Allah ni sai naji dama ba'a tafi da Æ´ar uwar Namijin nan ba, menene ma sunanta?

Ta kasa faÉ—an sunan saboda yae mata wahalar furtawa, Hannace ta taimaka mata wurin cewa "Ni kamar Gabriella naji yace, shi kuma Gabriel, Allah yafi sauran hankali da natsuwa, babu ruwanshi da kowa ko surutu baiyi, yanzu haka yana can kwance saman gadon shi, tausayi ma yake bani, hakanan an raba shi da Æ´ar uwarshi"

Hibba tace"Ae itama Sarah babu ruwanta, matsalarta ɗaya, ƙorafi kullum sai ta ma mutane ƙorafi akan gado yae mata ƙanƙanta ita ala dole ga me tsawo, Ni fa duk wannan Ƙaramar yarinyar tafi burgeni, Menene ma sunanta"? Tae tambayar tana kallon sauran, Rubina tace"Jar miya take da suna ko jimina namanta, nima tana burgeni, babu ruwanta, ita indai zata samu abinci, taci ta ƙoshi gado take hayewa ta naɗe abunta, sai in zatayi wanka, acuɗa mata baya shine kawai damuwarta,"

Ta6e baki yasmin ta yi, tsegumi ya samu wurin zama a prison, Æ´ar daddy tazo da bidi'a.

"Ni haushina wannan Figaggar yarinyar, wuyanta kamar na cokali mai yatsu, Tun da tazo take ta Turo mana abubuwanta, Allah ji nake kamar insa hannu in matse su, su fashe kowa Ya huta" dariya suka saki gaba ɗayan su jin abunda yasmin tace, Cikin zolaya eve tace"Na lura baƙin Ciki kuke mata don kun gansu tubarkalla ba kamar naku ba, " harara suka watsa ma Parveen da ta yi maganar, Hanna tace"Allah ya kiyaye me za muyi wa baƙin ciki? da alama kin manta a ina muke ne! Ae ba a tunƙaho da kyawun sura a gidan kurkukun ƙaddara, wlh ba fata nake mata ba, amma duk ranar da ta kuskura giants suka ɗauke ta, bana tunanin zata dawo da ƙirjinta yadda su ke"

Gaba ɗaya Sun shagala suna ta zuba ɗumi, babu wanda ya ji takun tafiyarta, ashe ta shigo Cikin toilet din da alama taji suna gulmarta ne, shiyasa ta faɗo musu, Kamar daga sama suka ji zazzaƙar muryarta ta karaɗe kunnuwansu

"You gossip about me because you're jealous, wow,"

Wuff suka mimmiƙe kusan atare suka Juya suna kallonta, Daga ita sai jar vest da short, Ƙirjin nan gasu nan tulu tulu, kana ganin fatarsu daga sama ga zanan tatoo ɗinta na bindin ɗawisu,
Da yake basu iya gulmar ba, da wasu ne cewa za su yi a'a amma sai suka haɗa baki wurin cewa"Eh, muna faɗin ra'ayin mu ne akan ki, An kawo mana masifa ke da Majnun," ruƙe ha6a tayi can kuma saita saki dariya tana nuna su da zira ziran yatsun hannunta, cike da shaƙiyanci cikin harshen turanci tace"Idan na fahimce ku, kamar kuna kishi ne akaina, saboda kunga abu tubarkalla ba kamar naku ba, ashafe kamar allon bango, Ni fa kokwanto nake yi akan ku anya mata ne kamar ni? Cos ba ku da banbanci da ƙattan dake acikin ku, Komai naku irin na maza ne babu ƙirar mace a jikin ku"

tsabar mamaki yasa suka saki baki kamar wawaye suna kallonta, Hibbe ce tai ƙoƙarin mayar mata da martani wurin cewa"To angaya miki muna son nonon ne, ƴar rainin wayau, sai kace ba ɗazu kika gama yunƙurin kashe kanki ba, ae da mun san haka ki ke wlh da mun ƙyale ki....." hibba bata ƙarasa maganar ba, sakamakon tsawar da ƴar gidan daddy ta kwatsa mata, har saida suka ɗan girgiza saboda sautin ta da tsiwa yake fita.

"Da alama ku ɗin dabbobi ne, Nasan ba ku san me ake nufi da dabba ba, saboda na lura Jahilai ne ku baku san komai ba, shiyasa aka killace ku kamar yadda ake yi ma dabbobin, A katafaren gidan daddyna akwai irin ku da ake killace wa, muna da zoo don dai banzo da wayata ba dana nuna maku yadda nake watsawa ƴan uwanku dabbobi hatsi Suna Ci" Duk da basu fahimci me take nufi ba, amma sun yi matuƙar har zuƙa, Sai tsuma suke yi.

ita ko sai tiƙar dariya take yi fararen haƙoranta kamar bata ta6a cin abinci ya gifta ta cikinsu ba, hannu takai tana shafa boobs dinta hada matsasu Yayin da take kallon su tace"Gaskiya najiye maku baƙin ciki, Waɗannan da kuke gani, majiyar daɗi ne su, sai da su ake ado, dasu ake jan hankalin Namiji, ae duk macen da bata da wannan to bata da banbanci da dutse a idon namiji, babu wani wuri da za'a ata6a ajikin ku aji shauƙi, A bushe ku ke.

A matuƙar ruɗe suka kallonta, sun gaza gane inda zancen ta ya dosa, da ya ke ta mai da su shashashu hada cewa idan suna son ganin nata zata nuna musu, don su tabbatar cewa ita ɗin macace ba kamar su ba da suke abushe," shiru su ka yi babu wanda ya tanka mata.

Dariyar shaƙiyanci ta kuma saki tana wasa da harshe tace dasu"wai sun ma san yadda ake yin mu'amala da mace da Namiji? Ko mace da mace? Idan suna so zata koya musu har ma da yadda ake samun baby" Kallon kallo su ka shiga yi atsakaninsu, kamar suce mata eh saboda suna san sanin me take nufi amma sun kasa.

"Alamu sun nuna cewa kuna so, to zan fara koya maku yadda ake yi, ni kawai i naso in wayar maku da kan ku ne, ta yadda zamu dinga jiyar da junanmu daɗi," babu wanda ya lura cewa azeeza ta gudu zuwa cikin ɗakin su, tana shiga taje gaban gadon angel ta fashe da kuka tana kiran sunanta, a lokacin angel har ta fara bacci can cikin kunnanta ta dinga jin shessheƙar kuka Azeeza, a firgice tafarka tana faman yamutsa fuska, azeeza bata jira ta gama buɗe idonta nata ba, taci gaba da magana tana fadin

"Angel kizo ki gani, ƴar gidan daddy zata 6ata mana tarbiya, wai zata koya mana yadda ake samun baby," tashin hankalin da ba'a sama shi date, saboda tsabar ruɗu, A fujajen angel ta ƙarasa waro manyan idanuwanta akan fuskar azeexa hannunta dafe da ƙirjinta take kallon azeeza sai ku ke ta ke yi baiwar Allah.

"Wai hada cewa mu ba mata bane, ƙattai ne, saboda bamu da irin ƙirjinta, kuma ma wai jahilai ne mu ana kullemu kamar dabbobin gidansu....' daƙyar angel ta samu tatattaro maganganun azeeza da suka tarwatsa kwakwalwarta, ta haɗesu wuri ɗaya ta karance su tsaf, tunaninta ya dawo kan saiti lokaci ɗaya ta fahimce su sosai, Muryarta afusace tace"yaushe akai hakan? Ki faɗa min tana ina"

Ta yi maganar tare da wurga eye balls ɗinta kan gadon unaiza bata ga kowa ba, Ruƙo hannunta azeeza tayi ta sauko daga saman gadon taja ta har zuwa sashen toilet ɗin su, tun kafin su shiga ta soma jiyo sautin muryar Ƴar gidan daddy tana koya musu yadda zasu Kusanci junansu, Wata irin kururuwa angel tasaki Yadda kasan Badakare ya durfafi filin yaƙi haka ta faɗa Cikin toilet ɗn, Hankalinsu gaba ɗaya ya dawo kanta, Sai huci take yi idanuwan nan sun kaɗa sunyi jawur, Unaiza kuwa koda angel ta faɗo toilet din bata daina magana ba, saboda tsabar futsara hada cewa"halan itama tazo ɗaukar lecture ne" Wani irin kukan kura angel tayi bata dira akan kowa ba sai asaman jikinta, gaba ɗaya suka kife ƙasa, wani irin jahilin bugu tadinga kai mata kamar xata kashe ta, tana kuka tana fadin"wlh baki isa ba, ashe baki da hankali wawayi kawai Jakkar banza, Ae babu babban jahili sai ke daƙiƙiya, Kuma ke ce dabbar badai su ba, Dama ni nasan zuwanki Cikin rayuwarmu ba alkhairi bane, saboda babu kunya atattare dake ƴar iska kawai....." kuka sosai Angel da unaiza suke yi, Duk ta gurjar mata baki hada jini, Su hannah sai kuka suke yi suma suna roƙon Angel akan ta ƙyaleta kada ta kashe ta,

tace musu ae ƙwara ta mutu saboda shaiɗaniyace ba mutun ba, Sautin Kukan Unaiza ne Ya isar ma kunnuwan masu bacci na cikin ɗakin, ba arziƙi suka farka danish da Gabriel hada Sarah da jamima, hatta majnun sai da ya farka, Bomb ya tashi sauƙi sai wurin Allah,
Chapter 125 · 0% Book details