Sashe 164
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"ƙarya ki ke yi min batul! Wai har ni zaki 6oye ma abunda ke damun ki? Me ki ka ɗauke ni ne? Nifa ƴar uwarkice, idan baki faɗamin ba wa zaki faɗa mawa, ni dama tun da aka dawo mana dake ban yarda dake ba, meyasa zaki 6oye min abunda su ka yi maki"? Fuskarta a ɗaure ta yi maganar, kafin taci gaba da cewa"Allah yajiƙan unaiza ba ta mutu ba sai da ta sanar dani komai daya faru da ita, don haka ki daina 6oye min, idan har kina son zaman lafiya to ki faɗamin me aka yi maki!! Cikin shessheƙar kuka batul tace"nifa ba abunda ya faru dani, ki daina tambayata bana so ki tafi kawai," Jinjina kai Angel tayi tare da sassauta muryarta"Its ok xan tafi batul tun da baki so in sani," Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta nufi ƙopar fita, ajiyar zuciya batul ta sauke duk a tunaninta Angel tafiya zata yi tabar toilet ɗin ashe ƙopa ta je ta rufe don kada sauti Ya fita, jamlock Ta sanya ta datse ƙopar da kyau, fuskarta a ɗauke ta juyo ta kalli batul dake manne jikin bango, jikinta sai kerma yake yi
"Zaki Faɗamin meke damun ki ko kuwa kin fi so in bi ta ƙarfi"! Shiru batul bata tanka mata ba, sai faman zazzare mata idanuwanta take Yi, Cizon le6e Angel tayi tare da naɗe hannun rigarta, gadan gadan ta nufi batul, ganin tana tunkarota yasa batul ta bar jikin bangon ta watsa da gudu da niyar ta fuce, Cikin rashin sa'a Angel ta cafko Sumar kanta, ta janyota da ƙarfi ta maka ta jikin bango ta yadda bazata ji zafi ba, Faɗane ya kaure a tsakanin su, Sai nishi su ke yi sun cakumi juna, ga jikin nasu duk ba ƙwari, tuni sun haɗa uban gumi, ƙarfi Angel ta sanya wurin kada batul ƙasa, tare da sanya hannu ta damƙi wandon jikinta ta soma kiciniyar zame mata shi daga jikinta, duk don ta gane ma idonta abunda batul ke 6oye mata........."
💋PRISONERS💋
Ba ta kai ga ƙarasa cire wandon ba, sautin dariyar Batul ta janyo hankalin ta ga kallon fuskarta, tsabar mamaki ne yasa Angel ta sakar mata trouser ɗinta, ta tsaya tana kallon ikon Allah sai tiƙar dariya ta ke yi kamar ba ita bace ta ke ku ka.
"Batul bana son iya shege, menene haka? Dariyar me ki ke yi mini? Kin fara sanya mi kokwanto akan ki" ta yi maganar tana binta da kallon tuhuma yunƙurawa batul ta yi tare da miƙe wa ta zaune, Sumar kanta duk ta tarwaste har ta saman fuskarta, tana dariya ta sanya hannu tare da yaye sumar ta mayar da ita bayanta, A hankali ta ke bin fuskar Angel da kallo, ta haɗe rai har wani huci ta ke yi.
"Meyasa ki ke yi mini haka? Ko dan saboda kin ga na damu da ke ne? rai a6ace ta yi maganar, shiru batul taƙi magana sai kallonta ta ke yi,
GyaÉ—a kai Angel ta yi"shikenan tunda na zama abun tsokana a wurin ki zan tashi in koma É—aki, don't ever expect me to worry about you anymore."
Ƙoƙarin miƙewa ta yi da niyar ta fuce daga cikin toilet ɗin, muryar batul ce ta dakatar da ita.
"Ba za ki iya daina damuwa dani ba, that's why ki ka sanya mini ido, ko bacci nake yi idon ki a kaina, duk wani motsi idan na yi sai kin ji ba'asin shi, irin wannan ƙauna haka........" ta yi maganar da zolaya, hakan ba ƙaramin 6ata ran Angel yai ba.
"Nifa ba abunda ke damuna, lafiyata qalau, don kin ga ina bincikar trouser É—ina shiyasa ki ka É—aga hankalin ki nasan me ki ke tunani nima abunda na ke tunani kenan, sai dai abun da mu ke hasashe bashi ba ne, It's just a rash
ya fito min a wurin, ya addabe ni da ƙaiƙayi, ɗazu dana kwanta bacci, nayi mafarkin Unaizah, hankalina na ya tashi, a lokacin bansan ƙurji bane nadai ji zafi a wurin, gani nake kamar zai yi irin na unaiza, kin ji dalilin dayasa na shigo toilet ina shessheƙar ku ka tare da bincika wandona don inga menene awurin daya haddasa min jin ƙaiƙayi, ban yi tsammanin za ki biyo ni ba, amma tunkafin ki shigo naji motsin mutun nan take raina ya bani cewar Ke ce, shiyasa na ƙara sautin kukan nawa don in firgitar da ke......." bata ƙarasa maganar ba, ta tuntsire da dariya ganin irin kallon rainin wayon da Angel ta ke Yi mata, tana a tsaye ta ruƙe qugu.
"Idan ba ki yarda da magana ta ba, zan nuna ma ki" ta yi maganar tare da sanya hannu tana ƙoƙarin zame wandon jikinta.
"Bana so ba sai na gani ba" ta faÉ—a tana harararta
"Idan ban nuna maki ba hankalin ki bazai kwanta dani ba, " bata jira jin me zata ƙara ce mata ba, ta yi saurin zame wandon kaɗan ta yadda tsiraicinta bazai baiyana ba, ƙaramin ƙurjine yayi jawur dashi daga gani ba ƙaramin zafi ya ke yi mata ba, Ajiyar zuciya Angel ta sauke hankalinta har ya kwanta, gyara wandon batul ta yi ba tare da ta ɗauke idon ta daga kan fuskar Angel.
Zuƙunnawa Angel ta yi agabanta"Idan har ba ki so raina ya 6aci to ki faɗamin me aka yi maki tsawon time da Giants su ka ɗauke ki," ganin irin kallon da batul ke yi mata ne yasa ta kuma cewa"Kada ki ce zaki 6oye mini komai batul, idan har baki so nima wata rana in 6oye maki wani abu dangane dani, "
A tsanake ta soma magana tana kallon cikin idonta
"Angel bayan an ɗauke ni daga cikin ku, kamar yarda na faɗa maku, ɗaki ne su ka kaini ni kaɗai, a saman gadon su ka kwantar dani, bakomai zan iya tunawa ba, na dai san sun cire min kayan jiki na, sannan Naji ana shafa jikina ta ko'ina, ba tare dana iya motsawa ba, kafin daga bisani naji ana tsotse......." bata ƙarasa ba ganin yadda Angel ta runtse idanuwanta, muryarta ƙasa ƙasa tace mata ina sauraronki ki ci gaba da magana
"Jinin da ke fitowa ta gabana shi naji ana tsotse shi"
Zuciyar Angel tuni ta soma tashi.
"Naji zafi sosai kamar zan zauce, tsawon lokaci Ana tsotse shi har zuwa time da naji bacci ya É—auke ni, daga nan bansan me ya faru ba, lokacin da na farka banga komai ba, sai kayan abincin da aka ajiye mini Saman table, a bunda ban yarda dashi ba a cikin kayan abincin akwai wani luluyayyan abu fari fat guda É—aya aka ajiye shi a tsakiyar tsokokin Nama......."
Ba ta kai ƙarshen zancen nata ba, Angel ta yi saurin katse ta da cewa" Allah yasa ba ki ci ba" jin haka yasa ta haɗiyi yawu fuskarta da alamun damuwa tace"Naci Angel, yunwa nake ji sosai a lokacin, komai sai da na ci"
Angel tace"amma bayan kinci sai me ya biyo baya"?
Numfasawa Batul ta yi kafin taci gaba da cewa"bugun zuciyata ne ya ƙaru, na dinga jin faɗuwar gaba, yanzu haka da na ke yi maki magana, akwai Jan tabo saitin zuciyata, zan nuna ma ki shi idan na gama baki labarin abunda ya faru, tsawon 4 days da inayin menstruation abunda ake yi min kenan kamar na ranar farko, Bayan jinin ya ɗauke, saina samu sassauci, sai dai kewarku da ta addabe ni, damuwa ta hana ni yin walwala, haka zan zauna ni kaɗai a ɗakin ina ƙwala maku kira babu mai jina, kamar zan yi hauka Angel, tun ina kuka har na gaji na daina, Sai na koma ina yin addu'o'in da ki ka koya mana, idan na karanta su sai inji sanyi a cikin raina, har ma in shiga toilet in yi wanka, idan na fito sai in kwanta saman gadon da ke a cikin ɗakin, kullum sai an kawo min abinci amma ban ta6a ganin waɗanda su ke kawo min shi ba, sai dai in gan shi A jiye saman table, sannan duk in a ka kawo min abinci sai naga wannan Abun dana faɗa maki luluyayye, Ina jin daɗin cin shi, cikin wata uku da bana atare da ku sau Uku ina yin jinin nan akowani ƙarshen month, kuma duk in nayi abunda su ke yi mini kenan, tsotse jinin da ke fitowa......." hawaye ne kwance a cikin idanuwan ta, ita kanta Angel ɗin idanuwanta A cike suke fal da hawaye gani take kamar Akwai wani abu da su ka yi mata ta hanyar abincin da su ke bata tana ci, musamman da ta ji ta ambaci luluyayyen abun nan fari da a ke sako mata cikin abinci, hankalin ta bai kwanta da shi ba.
"Batul inaso ki faɗamin ko kin ta6a gudowa daga Cikin ɗakin da aka kai ki?" ɗaga mata kai Batul ta yi alamar eh kafin ta ɗaura da cewa"Na ta6a samun damar durawa ta window ɗin da ke a cikin toilet ɗin ɗakin, na watso da gudu Ina neman hanyar da zata dawo dani cikin ku, A tsorace na ke a lokacin bani acikin hayyacina bansan meya faru ba, na dai ji kamar na faɗi ƙasa, kaina ya bugu, Bansan wanene ya mayar dani ɗakin da aka kai ni ba, lokacin dana dawo cikin hayyacina acan na ganni kwance saman gado, tsabar takaici yasa Na fashe da kuka har na kai ga zazzaga masifa ni kaɗai kamar mahaukaciya, a ƙarshe na haƙura na koma na kwanta, ina kukan zuci......." dakatawa ta yi da yin maganar tare da sanya yatsun hannunta ta share ƙwallar da ke gangarowa ta cikin idanuwanta.
"Ina so insan a hawa na nawa ne aka kai ki, Na ta6a yin mafarki da ginin kuma ni idan nayi mafarki yana zama gaskiya, a yadda aka tsara mini ginin hawa Uku ne, a cikin su wannene aka kai ki'?
Girgiza kai Batul ta yi tare da cewa"Ae bazan Iya tunawa ba, amma inaji kamar ginin dana na biyo time dana gudo Acan sama Ya ke," jinjina kai Angel ta yi"shikenan Iya abunda ya faru da ke? Wanene ya dawo da ke? Ko giants ne? Kamar Æ´ar jarida haka Angel ta tsare ta da tambayoyi.