Sashe 25
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Matsowa sauran Fulanin sukayi Gaba daya sukayi masu Danejo ƙawanya, Duk sun baza idanuwansu akan yarinyar, Cikin ƙanƙanin Lokaci ya kammala Yi mata treatment ɗin Raunin nata, Sannan Ya kalli Danejo yace ta dauketa takaita Cikin bukkarsu, ta kar6o bargunan da suke lullu6a dasu, A rufa mata ajikinta, sannan a hado garwashin wuta, A sanya mata a cikin ɗakin don ya ɗumama.
Bayan danejo ta dauketa, takaita Cikin bukkar su Saman shimfidar da suke kwana ta kwantar da ita, ta fita zuwa sauran bukkokin ta kar6o bargunansu, da zannuwa duka Ta haɗosu a hannunta, ta shigo cikin bukkar ta lullu6a mata su, kamar yadda kakansu yace ta yi mata, tana Cikin nannaɗeta cikin bargunan, Adda ta shigo hannunta ruƙe da murfi na karfe, Garwashin wutane jawur a saman shi, A gefe ɗaya ta ajiye garwashin wutar,
Kafin ta samu wuri ta zauna gefen danejo, magana suka soma Yi cikin fulatancinsu,
"Tausayinta nake ji, ƙaramar yarinya da ita, ko ya akai ta faɗa Cikin ruwa? Shin ina iyayenta suke ne? taya akai ta shigo Cikin kurmin dajin nan"? danejo ce ta yi maganar fuskarta da alamun tausayinta,
Adda tace"Nikaina nakamu da tausayinta, Allah kaɗai yasan daga wata uwa duniyar take, har na ƙosa tafarka, duk da nasan zaiyi wuya ace tana jin yarenmu, baiwar Allah gata kyakkyawa da ita kamar ta macen aljanna da kaka yake bamu labarinta"
Murmushi danejo ta ɗanyi kafin tace"Tunkafin ma tafarka Na ji nakamu da sonta sosai, kamar ni na haifeta" wani irin kallo Adda tayi mata"Ke da ko aure baki da shi," danejo tace"Ae ba laifi bane don na kirata da ƴata, balle kuma ni dana Tsinceta cikin ruwa kinga kuwa, a yanzu bata da wani makusanci daya wuce ni jinjina kai adda tayi "bazan biye maki ba, sarkin surutu" ta miƙe tare da fucewa daga Cikin bukkar.
_Taƙaitaccen tarihin danejo, Fulanin dajine, Masu yaɗa zango acikin daji wurin da ke da yalwataccen Abincin da dabbobin su zasu ci, kuma Su yi kiwo su yi noma, fulanine dake rayuwa acikin daji, babu wayewa attare dasu, kuma suna da ƙarancin ilmin addini, a wannan Lokacin saboda su kadai suke rayuwar su a daji,_
Family din danejo basu dayawa, Saboda yawancinsu ba'a wuri ɗaya suke ba, Kowa Ya kama gabansa, Kaɗan ne suka rage, Ita dai takasance marainiyace, Iyayenta sun rasu tun kafin ta mallaki hankalinta, kuma ita kaɗai suka haifa, ta taso A hannun ƙanwar mahaifiyarta wadda suke kira da inna wuro, ƴa'ƴanta huɗu bawuro shine babban ɗanta,Yana da mata Ɗaya Haulatu, ɗansu ɗaya wanda suke kira da cubaɗo, bayan shi sai Adda itace ta biyu, sai gidaɗo sai kuma ƙanwarsu hasiya, Kakanninsu duk sun rasu, Ɗaya kaɗai ya rage masu na 6angaren Mahaifiyarsu, sukaɗai suke rayuwarsu a wuri ɗaya.
Yinin ranar Danejo bata motsa ba, ta kasa ta tsare sai Yarinyar ta farka, saboda ta ƙwallafa rai akanta sosai, tunkafin ma tafarka tasan wacece ita, Allah ya jarabceta da son yarinyar,
Tun tana sa ran zata farka, har dare ya yi bata farka ba, har sun fara fidda rai, Su uku ne acikin bukkar, Danejo da kuma Hasiya, suna ta zaman jiran tafarka har bacci ya yi awon gaba da su.
Tsakar dare lokacin kowa Yayi bacci Cikin ƴar bukkarsa, ta soma mutsu mutsun buɗe idanuwanta, ƙoƙarin motsa Jikinta tayi sai dai ina sam takasa,tamkar an ɗaureta da igiyoyi haka take ji, ga wani irin zafi da take ji ajikinta, sautin muryarta sam baya fita, Can ƙasan maƙo shi take sambatu,
"Daddy mu koma gida, tsoro nake ji,"tun sautin baya fita harya fara fita da ƙarfi, da iya ƙarfinta na ƙarshe Ta yaye bargunan da suka lullu6a mata, buɗe idanuwanta tayi sosai tana kallon Bukkar, Wasu jerin kwaryoyi tagani a jere, da wani akwatin karfe da sauran tarkacensu na fulanin daji, Wurga eyes dinta tayi akan Fitilar kwan dake Ajiye a ƙasa wadda ta haskaka Cikin bukkar, kafin takai idanuwanta kansu Danejo dake ta bacci daga zauna suna gadinta,
Wani irin tsorone Ya ziyarci zuciyarta, hankalinta ya tashi matuƙa, ganin baƙin fuskoki, Ga kuma wani wuri mai kama da A kurkukin kaji, rushewa tayi da matsanacin kuka, a firgice Danejo da hasiya suka farka jin sautin kukan Mutun, Tsareta da ido su ka yi suna kallonta kamar yadda take kallon su, Cikin harshen fulatanci suka soma ƙoƙarin rarrashinta, Ta wawware masu gray eyes ɗinta, jin suna yi mata gwaranci,
Cigaba da kuka tayi tana faɗi"Daddy! wayyo Allah na!! Ina daddyna ya ke!! Su wanene ku! A ina nake ne!!" miƙewa Ta yi da ƙyar saboda ba isasshiyar lafiya gare ta ba, Jikinta sai kerma yake yi, Ga uwar zufa data wanke mata jikin nata, ganin tana ƙokarin neman hanyar fita daga Cikin bukkar yasa suka miƙe da sauri Suka nufe ta zasu ruƙeta, watsawa ta yi da gudu tana bin jikin bukkar a ƙokarinta nata gano hanyar da zata fuce, su kuwa sun dage sai haƙuri suke bata"kiyi hakuri ki zauna baki da lafiya, muma mutane ne kamar ke kada kiji tsoron mu baza mu cutar dake ba" tunda suka soma magana take ta faman zazzare masu idanuwanta, saboda bata fahimtar yaren da su ke yi mata magana da shi, ballantana kuma harta fahimci cewa lallashin da suke Yi mata,
"Wayyo Allah daddyna, Ni ku maida ni wurin daddyna, Inaso nagan shi," sosai take Yi masu kuka, mai tsiwar gaske, gaba daya sautin kukan nata ya karaÉ—e kunnuwan duk wani mai yin Bacci acikin bukkokin,
Kukanta Ya ishesu, É—aya bayan É—aya suka soma fitowa daga cikin bukkokinsu, kowa yana ta faman Yin hamma, A haka suka nufi bukkarsu danejo, inda suke Ji yo sautin kukan nata.
Inna wuro ce ta shigo ciki, tare da su haulatu, gaba daya suka É—aura idanuwansu Kan ANGEL, dake ta kuka, tambayar su Danejo su ka yi meke faruwa?Suma su ka ce basu sani ba, ta tashi tana ta kuka, kuma su basu san harshen da take yi masu magana da shi ba" adaren ranar babu wanda ya runtsa Cikinsu, taruwa sukayi akanta sunata aikin lallashi, ta burkuce masu sam bata fahimtarsu, kamar yadda suma basu fahimtarta, sunan Daddynta kawai take kira,
Koya rayuwar Angel zata kasance acikin fulanin daji? Yarinyar da ta taso Cikin kulawa da soyayyar mahaifinta, batasan rashi ba, batasan maraici ba, Ta saba da rayuwar gatanci sai abunda takeso daddynta yake yi mata, Yau gata a ƙurmin daji, Cikin fulanin daji mutanan da basu Jin harshen hausa Sai fulatanci, ita kuma bata Jin fulatanci daga hausa sai turanci, Sai kuma larabcin data koya a makarantar islamiyar da take zuwa, Taya zata Iya jure zama dasu? Abincinsu yanayin rayuwarsu sam ta banbanta da ta mutanan dake rayuwa Cikin gari,
Kafin safiya tayi Angel ta galabaita sosai, Idanuwanta sun kunbura saboda rashin bacci da kuma kukan data sha, sun ƙanƙance, jijiyoyin wuyanta duk sun firfito rudu ruɗu jikin fatarta, le6enta ya faffashe hada busasshen jini, ga wani irin zazza6i na tashin hankali daya rufarmata, a ƙarshe yanke jiki tayi ta faɗi asume, Jinya ta koma sabuwa, magunguna suka shiga haɗa mata nagargajiya ƴan dabarunsu da ba'a rasa ba, Hada wasu ganyayyaki suka jiƙa mata acikin gora, suna bata tasha, Allah ya haɗa jininsu da ita, musamman Danejo kullum A tare da ita take kwana, Ba ƙaramin tausayinta suke Ji ba, Saboda ko magana bata Iya furtawa, Jikinta yayi tsauri sosai, Babu sauƙi tamkar zata rasa ranta, ga shi ko a bincinsu bata Iya ci, Furace kaɗai itama ɗin sai sun ɗura mata abaki tukunna take wucewa ta makoshinta daƙyar, angel ta wahala sosai, ta rame ta bushe ta ƙanjame tayi duhu tamkar ba yarinyar nan mai ƙiriniya ba,
Kusan Wata Uku ta yi Acikin wannan mawuyacin halin, kafin Allah ya kawo mata sauƙi, tafara buɗe baki tayi magana, Sai dai subi ta da ido don basu fahimtar me take cewa, kullum saita yi masu sambatu akan su nemo mata daddynta, daga baya da ta fahimci basu gane yaren da take yi masu, Saita Zuƙunna ta sanya yatsanta a kasar wurin da ruwa ya jiƙa,ta soma Zana fuskar mutun Asaman ƙasar, data kammala zanen ta kirasu tana nuna masu zanen, Suka zuba ido suna kallon jagwalgwalon zanan fuskar da ta zana, Kallon juna su ka yi Alamar basu fahimta ba, fashewa tayi da matsanancin ku ka, Ta watsa da gudu Tabar wurin bukkokinsu, Suma suka bi bayanta a guje, suna ƙokarin kamota gudun kada wata muguwar dabbar daji ta halakar da ita,
Cikin ƙurmin dajin ta nutsa, har tazo inda wannan ruwan Yake inda Taj ya jefa ta ciki, Juyo wa Tayi tare da kallonsu, sai faman haki suke yi sun sha uban gudu, da hannu ta dinga nuna masu cikin ruwan Saboda ta gane cewa a nan ne inda daddyn ta Yazo da ita Ya wurgata ciki,
Duk yadda taso ta fahimtar dasu, Sam sun gaza fahimta, dunƙule hannayenta tayi tare da murzasu, tana kwatanta masu a cikin mota suka zo dajin, Nan ma still basu gane me take nufi ba, Zuƙunnawa tayi agaban ruwan, ta rushe da matsanancin kuka, duk jikinsu yayi sanyi,
Babu yadda angel ta iya adole ta haƙura taci gaba da rayuwa acikin fulanin daji, tun bata saba ba da su ba, har ta fara sakin jiki da su, Bata da abincin daya wuce fura da nono, da kuma Gasassar masara, Sai kuma nama idan sunyi farauta, shigarta ta koma ta fulanin daji, Danejo ce tayi mata kyautar kayanta, Wanda tun tana yarinya kayan suke ajiye cikin akwatin ƙarfenta, Zuwan Angel Cikin rayuwarsu Ta fiddo da kayan, Ta bata su ta sanya,