← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 158

Sashe 96

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kar kiga kin girma ko kin haihu wlh dukan tsiya zan miki Halima kuma banga uban da zai ce dan me ya saka ba, tun muna shaida juna dake ki faɗa mun mai ya saka kika taho gida yanzu ba sai anjima ba". Kuka na fashe dashi bayan da naja baya daga kusa dashi dan na san dukan daya ambata zai mun tsaf zai aikata dan zuciya ce dashi kamar kuturu duk cikin ƙannen su Mama yafi su zafi ba kuma ya wasa damu dama shiyasa muke shakkar sa sosai. Tsawa ya sake bugamun bayan daya miƙe tsaye da alama neman madoki yakeyi, dai dai nan Anty Labiba da Mama Fauziyya sukayi sallama da gudu kuwa na nufi Mama Fauziyya na rungume ta ina sake fashewa da kuka ta ɓoye ni a bayanta tana tambayar mai ya faru nan kuwa ya fara zazzaga faɗa akan me zan zo gida tsayin lokacin nan na sakina akayi ba kuma naƙi faɗar zuwan me nayi wlh zai mun dukan tsiya idan ban buɗe baki nayi magana ba.

"Kai daɗi na da kai saurin hasala Mudassir banda haka duk maganar ai bata wuce ayita a zaune ba" Mama Fauziyya ta faɗa, Mama ta ce
"Ai kuwa magana ta wuce ta sulhu dan tuntuni nake bin yarinyar nan akan ta faɗa mun mai ya faru tun hankalina yana tashe da lamarin har na haƙura na fawwalawa Allah tunda naga alamar zan ɗorawa kaina damuwa ne a banza alhalin wacce nakeyi akanta ita bata damu ba toh wlh nima yanzu na gaji, cikin biyu dole ayi ɗaya. Ko dai idan sakinta yayi ta faɗa mu san zaman me takeyi ko kuma ta tattara ta koma amma na gaji da zama da ita a haka kullum ina kallonta ina jin ɓacin rai".

"Hmmm mu dai anayi muna jin daɗi" Anty Labiba ta faɗa tana zama akan kujera irin ba abinda ya shafeta ɗin nan, banda kuka ba abinda nakeyi, sai da Uncle Mudassir ya mun tatas kafin ya tafi akan kada na kuskura ya sakw dawowa bai tarar da ɗayan biyu ba, ko dai in koma ko kuma ya samu tabbacin zaman yanci nakeyi. Ba abinda ya sake ɗaga mun hankali irin yanda Mama take nanata ita ta gaji Mama Fauziyyar da take kareni sai in tattara na bita amma ba zata cigaba da zama dani alhalin bata san ina ma saka gaba ba. Duk sai suka sake jagula mun lissafi ga danuwar da na tashi da ita ga kuma wata sabuwa data ɓullo na ringa jin inama ban biyewa huɗubar Hansa'u ba na saurari Bilal ƙila da na bashi dama zai zayyana mun nadamar sa ya kuma nemi yafiyar tawa idan yaso sai in yanke hukuncin da nake ganin ya fi mun yanzu gashi nan a garin jan aji ya tsinke gidan ma kuma zasu tasoni a gaba in rasa ina zan tsoma raina.

Ɗaki na koma na cigaba da kuka sai da nayi mai isata kafin na haƙura na wanko fuskata na koma na zaune bayan na ɗauki wayata zuciyata na ayyana mun na kirashi, tarin missed calls na gani da number da aka kirani da ita ɗazu zai text guda ɗaya,
"Hafiz ne abokin Mijinki Bilal, idan kin samu lokaci ki kirani akwai abinda nake so mu tattauna" abinda saƙon ya ƙunsa kenan. Na natata karanta saƙon yafi sau biyar a raina ina mamakin wace magana ce Hafiz zai tattauna dani kuma mai muhimmanci kamar yanda ya ce?

Tunani na shigayi a zuwan Matarsa ko akwai wani abu dana faɗa mata da bai kamata taji ba amma ban tuna ba, ajiye wayar nayi kawai ba tareda na kira shi ɗin ba kamar yanda ya buƙata dan ni banga dalilin hakan ba. Bacci ne ya kwashe ni ina tsaka da tunanin neman mafita, sanda na farka gari har yayi duhu alamar magriba ma ta wuce na ringa salati in mamakin wane irin bacci nayi haka tun azahar kuma ace babu wanda ya tashe ni da akayi la'asar da ga magriba ma lallai dagaske da Mama tace ta gaji da zamana ba wasa takeyi ba tunda gashi ko a jikinta bata ma ko yi tunanin mutuwa nayi ba ba wanda ya leƙo ni. Hawaye suka ɓalle mun ina wanka ina kuka har na gama sannan nayo alwala ina jin cikina kamar zai haɗe da bayana tsabar yanda yunwa ta gama rarakeni, daƙyar nayi sallolin da suka wuce ni kafin na fito kai tsaye na faɗa kitchen neman abinda zanci.

Mama da Zainab na aikin ƙarasa abincin dare ko kallo na batayi ba sai Zainace ta ce
"Kin tashi Yaya Halima? Tun ɗazu nake leƙo ki naga kina jin daɗin baccin shiyasa ban tashe ki ba". Ban amsa ta ba na ɗebi abinda na gani na fita, bayan mun gama ci tareda Sharifa ina shirin na koma ɗaki tun kafin Mama ta fito falon Mu'azzam ya shigo, ba yabo ba fallasa ya ce mun
"Kina da baƙo yana falon Abba".

Kallon za nayi kafin cikin ɗaga murya na ce
"Wane irin hauka ne haka ni zaka cewa ina da baƙo ko ka manta matar aure ce ni?"
"Wai matar aure" ya faɗa yana nuna ni kafin ya tuntsure da dariya harda buga ƙafa ya wuce yana cewa
"Idan zaki tashi kije Malama ki wuce kar ki ɓata masa lokaci".

Miƙewa nayi da zummar na bishi in ji ba'asin akan me da mutunchi na da kuma aure na har wani zai zo gurina a shigo dashi har falo saiga Abban ya shigo, ba yabo ba fallasa shima ya kalleni ya ce
"Ibrahim bai gaya miki kina sa baƙo ba ne?"

"Abba ya za'ayi da aure na ace wai wani yazo gurina in fita?" Na faɗa ina rau rau da ido kamar zan fasa kuka, sama sama yace
"Bana son sakarci Halima ki wuce kuma tun kafin ranki ya ɓaci". Sum sum na wuce domin na fi kowa sanin fushi ba ɗabi'ar Abba bace har kuma idan ransa ya ɓaci to fa baya yi da sauƙi.

Turus nayi a bakin ƙofa ganin baƙon, Hafiz ne abokin Bilal. Na ƙarasa ciki da ƙaramar sallama na samu kujera can nesa na zauna kafin ma shiga gaishe shi ya amsa cikin kulawa yana tambayata yara na gaya masa Al'amin yana can gidan Anty Labiba Sharifa kuma tana ciki.

"Kiyi haƙuri Halima kin ganni ba tareda kinyi mun izini ba, na yi ta jiran martaninki toh amma gaskiya ina da ɗan uzuri ne wanda kuma ina son mu tattauna kafin na wuce dan ban san ko har zan dawo ba tareda lokacin buƙatar hakan ya wuce ba" ya faɗa, ni dai kaina yana ƙasa ya cigaba da cewa

"Kiyi haƙuri Halima, na san zaki iya cewa menene nawa da shiga cikin maganarki da Bilal amma ki sani ina da dalilin yin hakan, na san kin fi kowa sanin kusancin da yake tsakanina da Bilal. Allah ne ya haɗa jinina da shi kuma Allah shine shaida ina jin sa a raina tamkar wanda alaƙar jini ta haɗa mu shiyasa ban taɓa ƙyashin nayi masa wani abu ba, a zaman da nayi da Bilal na karanci wasu halayensa waɗanda na ɗauka a matsayin tawaya da kowanne ɗan adam yake dashi dole idan ya zamo ya cika ta wani ɓangaren ta wani gefen kuma za'a same shi da kuskure dan haka na karɓe shi a yanda yake ina kuma yi masa uzuri a duk in da ya kuskure domin nima na sani dole akwai ta inda nake da giɓi sai dai ko kusa ban taɓa tsammanin Bilal zai aikata irin abin nan ba.

Kiyi haƙuri Halima ni ne silar da har Bilal ya san Jalilah sai dai bani da wata masaniya ta ƙulluwar wata alaƙa a tsakanin su domin daga shi har ita sun rufeni akan haka. Jalilah Ex ɗina ce kuma dalilin da ya kawo ruɗani tsakaninki da Bilal shine silar rabuwar mu da ita har na fasa aurenta bayan har an yi mana baiko. Yanda kike son Bilal haka Jalilah take so na, albarkacin wannan soyayyar ta saka kuma duk yanda na so na yakice ta daga rayuwata taƙi fita na raga mata har muka cigaba da mu'amalar gaisawa.

Ban ɓoyewa Bilal komai akan Jalilah ba tun a sanda ya fara ganinta har yake tuhunata akan me yasa naƙi aurenta bayan a nasa ganin tafi Suhaila komai na ya mace, na ɗauka abinda na gaya masa akanta zai saka ya hankalta dukda ban taɓa kawo cewar wata mu'amala zata iya shiga tsakaninsu ba sai dai abin takaici hakan ya faru kuma ya rufeni har ta kai a silar ta yana shirin rusa rayuwarsa ta hanyar rabuwa da abubuwa masu muhimmanci ciki harda ke da kuma aikin sa.

Bazan cika ki da surutu ba amma Halima ina so ki san da cewa duk wani abu da kike tunani akan Bilal da Jalilah na sani, na daɗe ina masa addu'ar gane gaskiya tun kafin ubangiji ya kawo irin wannan lokacin da asirinsa zai fasu, kada kiyi tunanin shirun da kikayi yana nufin kin rufa masa asiri domin shi da kansa ya ɗaurawa kansa ƙararrawar da zata yayata sirrinsa har ya isa ga kunnuwan kowa. Jalilah ba zata taɓa yarda da cin amanar da yayi mata ba bayan ta gama ɓata lokacinta ta kuma kashe kuɗinta akansa da tunanin zai aureta sannan ya zagaya yayi amfani da kuɗin ta ya auri wata hakan ba zai taɓa yuwuwa ace ta ƙyale shi ba".

Kusan daga iya in da na dena fahimtar duk wasu maganganu daya cigaba da faɗa kenan, da farko na cika da mamakin yanda yace ya san komai dake tsakanin Bilal da Jalilah sai kuma maganar da na tsinta ta ƙarshe ta goge mun hadda ta kuma jefani a ɗimuwa ko in ce gushewar hankali na wucin gadi cewar da yayi Bilal yayi amfani da kuɗin Jalila ya auro wata?

Har idan dagaske ta silar sa Bilal ya san Jalilah kenan sai bayan ya aureni hakan ta faru tunda ina gidan Bilal suka haɗu da Hafiz hakan yana nufin bani ce wacce aka auro da kuɗin Jalilah ba kenan to me yake nufi? Aure Bilal ya ƙara ko me?
[4/26, 9:17 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
Chapter 96 · 0% Book details