← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 158

Sashe 43

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Akan me zaka koreta kuma a ɗora mun laifi har azo ana zagin iyaye na da basu ji ba basu gani ba?" Na faɗa cikin shashsheƙa. Kamar wani na Allah yayi ƙasa da kai kafin ya kwaso rantsuwa yace
"Bani na koreta ba"
"Ni na kore ta kenan kaima ka sake tabbatar da hakan?" Na faɗa ina fashewa da sabon kuka. Se ya taso ya dawo in da nake ya jani jikin sa yace
"Ita tacewa Hajja kin barta da yunwa kuma da tayi miki magana ki bata abinci shine kika ce ba zaki bada ba ta koma gidan mijin ta ko ta tafi gidan uban ta taci wai tazo ta takura miki ta hana ki sakewa a gidanki. Tun kafin Hajja ta dawo ta kira ni ta gaya mun abinda Fadilan tace kin mata na kuma tabbatar mata ƙarya be nasan ba zaki mata haka ba ita kanta se da na same ta na ja mata kunne shine ma nasa ta tattara ta koma gidan ta kafin Hajjan ta dawo na ɗauka maganar ta mutu kin san Hajja ita kuma da ruƙon magana in dai ba ta amayar ba bata jin daɗi amma nasan tunda ta rigada ta miki faɗa yanzu shikenan maganar ta wuce musamman tunda ta tabbata hakan be faru ba ƙarya Fadila ta gaya mata". Haka ya ringa lallashi na yana gaya mun maganganu har seda ya wanke baƙin sa da na gani na maida laifin kacokam kan Fadila domin ita ta shirya komai na kuma yarda bashi da laifi abu ɗaya da naji ba daɗi da be tsaya mun ya fitar da gaskiya ta a gaban Hajja ba, amma kuma dana tuna ita ɗin bata da daɗin sha'ani be zama lallai ta fahimce shi a lokacin ba ta yuwu ma ta haɗa dashi yanda kuma take magana ba tare da tauna kalami ba se ta faɗa masa wani abun mara daɗi da ze iya tasiri a rayuwar sa tun da mahaifiyar sa ce.

Babu kunya kuma kwana biyu da yin haka da yamma ina zaune se ga Hajja da jikarta Mansura suka zo da kwanukan abincin dana kai mata waccen ranar wai ta rakota ta bani haƙuri, ni abun ma se ya bani kunya ya bani takaici. Ta ringa zagin Fadila tana cewa duk ita ta zugata se daga baya da Bilal ya zaunar da ita ya mata bayani ta gane gaskiya tasan bata kyauta ba data hau kan magana kawai ta zauna ba tare da bincike ba. Ni dai nayi ta Allah Allah ta tafi kafin ta sake samun wani abun da zata ce na mata laifi har raina kuma na ƙudire tsakani na dasu gaisuwar mutunchi babu dogon zumunchi tunda na fahimci abun a jinin su yake su rufe ido su ciwa mutum mutunchi idan abu ya haɗo ku daga baya kuma ba kunya su waske.

BAYAN WANI LOKACI
[1/25, 11:31 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 18*
Haka rayuwa taci gaba da gangarawa; yau fari gobe baƙi. A yanzu da nake lissafa watannin aure na goma sha biyar da Bilal shekara ɗaya da wata uku kenan, tabbas a zaman da mukayi nayi karatu da yawa tattare da halayen sa waɗanda a baya ban san su ba. Babban abinda na fara naƙalta da Bilal shine mutum ne me son abinsa. Tabbas Bilal nada son abin sa kuma ya kan iya rufe ido ya cima koma wanene mutunci har idan ya shiga gonar sa, idan yayi wani abun se na shiga mamakin ta yanda har muka shafe tsayin shekaru shida muna soyayya ya akayi ban taɓa fahimtar shi ɗin haka yake ba. Da fari abun ya dame ni ko nace yana damu na, amma dana zauna nayi wani tunani na kuma yi amfani da maganar Hausawa da suka ce idan mutum ya nuna yana son abun sa ka taya shi, se ku zauna lafiya. Hakan nayi amfani dashi kuma nake zaune lafiya da Bilal.

Idan akwai abinda yake sosa mun rai wani lokacin be wuce yanda ni kullum na buƙaci wani abu a gurin sa da yake ganin be zama dole ba ze rufe ido yaƙi mun amma ina kallo ko da bashi ne ze ci ya yiwa yan gidan su. Tabbas ina jin babu daɗin hakan a raina; a ƙalla ko da ba a duk sanda na buƙata ba, na kan so ace yana kamanta kyautata mun nima. Amma kuma wani sa'in idan nayi tunanin sai naga hakan ba komai bane. Hajja mahaifiyarsa ce ita tilas ya hidimta mata suma kuma sauran yan uwan sa idan yayi musu zumunchi yayi wa da wannan nake danne kaina musamman kuma da alhamdulillah duk abin da na rasa a gurin Bilal na kan samu sama dashi a gurin iyaye na da basa gajiya da hidimta mun musamman Abba kusan ko da yaushe naje gida ko mukayi waya ko wani cikin ƙanne na ze zo se ya bayar da saƙon kuɗi ko abin amfani an kawo mun. Ita kanta Mama duk da yanda kullum Anty Labiba take cikin zugata akai na wani sa'in taji wani sa'in ta toshe kunnenta; musamman tun da ciki na ya fara girma, wani tausayi na take ji bini bini zata yo mun miya ta bayar a kawo mun se dai Bilal ya tafasa mana shinkafa ko taliya muci.

Nayi zaton tun da ciki na ya fara girma Bilal ze yi tunanin ya kamata mu fara siyan kayan baby muna ajiyewa, ban masa magana ba, saboda tun saɓanin da muka samu da babbar sallah akan naman layya nayi alƙawarin ba zan saka masa baki a duk wani abu daya shafe shi ko kuma ya zama dolen sa ba. Raguna guda biyu ya turke tun ana sallah saura kwana biyar wanda yace ɗaya Hafiz ne ya bashi ɗaya kuma shi da Abubakar suka haɗa kuɗi suka siyawa Hajja. Ranar jajiberin sallah Babangida ɗan ƙanwar Hajjan ne yazo ɗaukar Rago, guda ɗaya ya ɗauka ya tafi dashi ba'a rufa awa ɗaya ba se gashi ya sake dawowa ina cikin ɗaki kukan ragon ne ya fito da ni dan sam banji motsin buɗe get ba ban ma san daya fita be kulle mun ƙofar da kyau ba.

Ganin yana kici kicin kwance Rago yasa na dakatar dashi ta hanyar tambayar sa lafiya? Ina kuma za'a kaishi?
"Hajja ce tace duka biyun za'a kai can gidan, na leƙo ina ta sallama na zata ma bacci kike baki amsa ba" ya bani amsa. Mamaki ya kamani; me yasa za'a kai ragon kuma can gidan? Na tambayi kaina. Ban sake ce musu komai ba ina tsaye ya gama kwance shi yaron da suka zo tare ya ja shi suka fita waje in da ya bar mashin ɗin sa. Har na ɗauki waya zan kira Bilal a lokacin sr kuma na ce bari kawai se ya dawo, ina tsaka da haɗa masa abin shan ruwa kuwa ya shigo. Daga yanda naga be damu da rashin ganin ragunan ba na fahimci da sanin sa kenan aka kai can.

Se da aka sha ruwa bayan ya dawo daga sallar isha'i kafin na taso masa da zancen,
"Ni nace akai can dan nasan idan an bari a nan ke da kike fama da kanki ba iya aikin zakiyi ba ƙarshe ki tara mutane su cinye" amsar daya bani kenan. Dama cike nake da haushin ƙin yi mun ɗinki da yayi wannan sallar ma yace shi ba ɗinki ne a gaban sa ba ai ina da kaya na saka mana amma a gaba na ya shigo da atamfofi uku harda lace ɗaya na Hajja da Fadila wadda ta sake dawowa gida zama yaƙi daɗi se haushin ya zamar mun biyu ga wancan ga na ɗauke rago yanzu kawai na tashi na bashi guri ba tare da nace komai ba.

Washe gari bayan an sakko daga sallar idi ya kira ni wai na shirya na tafi can gidan nasu muyi aikin nama; se naji maganar ma kamar ta rainin wayau. Shi da yace ya kai can ne saboda ina fama da kaina ba zan iya a gida na ba kuma yanzu in tafi taya su acan. Ce masa nayi kaina na mun ciwo se dai gobe, nayi kwanciya ta haka na wuni ƙamshin suyar hanjin maƙwafta duk ya gama cika mun ciki na ringa ji kamar na yafa mayafi na leƙa ɗaya daga gidajen a bani taɓi. Naci burin suyar naman sallah har spices na karɓo a gida da naje amma ya wani ɗauka ya kai gidan su. Da magriba naji ba zan iya haɗiye kwaɗayi na ba kawai na kira Mama nace ta bayar da hanji a kawo mun na ji daɗin da bata tsaya bin ba'asi ba tace toh ba a ɗauki lokaci ba kuwa Imam ya kawo mun da zafin sa da alama sunyi daren aiki lokacin aka sauke.
Chapter 43 · 0% Book details