← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 158

Sashe 4

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina fita naga Hansa'u a zaune, a raina nace lallai ma, ƙarata ta kawo ko me? Haka na samu guri na zauna nan kuwa Abba ya haɗa mu duk mu biyun ya mana kaca kaca kowa ya bata laifinta. A yanda yace tun da la'asar daya fita aka bashi labarin wai munyi faɗa a makaranta a raina na ringa tsinewa munafukai nasan kuma baze wuce Nasir ko Musan gidan inji ba sune yan unguwar mu kuma a gabansu mukayi faɗan shine ashe sunzo unguwa suna yawo damu, Abba ya mana kaca kaca yace kuma mu bawa juna haƙuri kuma idan ya sake jin irin haka ba faɗa ba seya haɗa mana harda duka mun san kuma ze aikata. Yana da sanyi da wasa da dariya amma fa kaifi ɗaya ne muddin yace zeyi abu zeyi dan haka muka masa alƙawarin haka ba zata sake faruwa ba. Washe gari kuwa da mukaje makaranta komai ya wuce, dukda dai Hansa'u na lura bata gama hucewa ba amma ni na sake gaba ɗaya ina ta janta har daga ƙarshe ta huce muka cigaba da sabgoginmu.

Ranar Asabar Bilal yace ze zo, tun haɗuwar mu a gidan Anty Labiba be samu ya dawo ba se waya mukeyi, sun sake komawa Abuja ance wannan watan in sha Allah albashinsu ze fara shiga harma za'a biya su na baya da basu samu ba. Naji daɗi sosai ko ba komai maganar aurenmu zata taso masu ganin ba aure na zeyi ba zasuji kunya. Allah ya sani ina son Bilal tamkar rai, yanayinsa da halayyar sa sun min a irin mijin da nake fatan aure na kuma faɗa na ƙara ciki wuya ko daɗi zan zauna dashi domin shi nake so ba wani abu ba duk wanda suke zuwa masu abin hannun da ake ganin sunfi dacewa dani ni basu gaba na shi ɗin shi nake so kuma ina ji a jikina gaba se mun zama abinda ba'ayi zato ba duk masu gulma se sunji kunya.

Kamar ko yaushe nayi masa snacks samosa da cake se dambun nama da Anty Hasiya ƙanwar Abbanmu ta kawo masa na ɗibar masa. Tsayin fara soyayyar mu Allah keda kullum amma duk sanda Bilal ze zo sena masa abinci ko wani abun taɓawa da zan bashi. Tun Mama na biye mun harta fita sabgata a cewarta abin nawa bana ƙare bane, harta kai shi ze faɗa mun abinda yake so ko in tambaye shi babu ko sisinsa haka zanyi yazo ya cinye har ya tafi da saura balle kuma da azumi gidanmu yake shan ruwa idan be zoba zan aika masa dashi haka in sallah tayi zan haɗa sha tara ta arziƙi a kaiwa Hajja mahaifiyarsa sannan in haɗa masa wanda zasu zo da abokanansa suci se an samu me mutunchin gaske ne cikinsu ze iya ɗaukar wani abu yace mun ga tukuici amma hakan ni sam baya damuna domin dan Allah nake masa kuma arziƙin so da ƙauna.

Seda a gama jere masa snacks ɗin da kunun aya me sanyi kafin na zauna muka gaisa muna kashe juna da murmushin ƙauna. Na cika masa kofi da kunun ayar yasha ya gode Allah yana kallona yace
"Wato Halims, bansan kalar murnar da zanyi ba ranar da aka ƙwala shelar ɗaurin aure na dake, ina ga se na hau kan hasumiyar masallaci tsabar murna" na ƙyalƙyale da dariya nace
"Ka dai rufa mana asiri kar ace ango ya karye a garin murnar aurensa" yace
"Allah Halims baki san yanda nake jinki a raina bane kedai kawai Allah ya kaimu ranar da zan nuna miki komai a aikace ba surutun da kike ɗauka wasa ba".

Na sadda kai ƙasa ina murmushi kawai ba tareda na ce masa komai ba, ya fara cin samosa yana mun hira can yace "Albishirinki Halims" na ɗago na kalle shi tareda cewa
"Goro" ya karɓi kunun aya kafin yace
"Albashin mu ya fara shiga, an turo mana na wata uku jiya". Sosai naji farin cikin albishirin ɗin nada na gyara zama ina cewa "kai alhamdulillah naji daɗi sosai Allah yasa albarka" ya amsa da
"Amin" yana cigaba da cin kayan gabansa. Hira muka cigaba ina jira naji ya sako zancen aiko sa rana tunda salary ya fara shiga amma shiru hakan yasa nace masa
"Dama ko jiya Abba yake sake mun magana nace in sha Allah idan kazo zan gaya maka, to ashe ma jira ya ƙare tunda abinda muke tsammani ya iso".

Seya shafa kansa yace
"Eh wlh, ai Baba Malam ma yace kawunku na Galadanci ya masa magana akan akwai bikin da za'ayi acan gidan kakanninku so samu suna so a haɗa"
"Lah bikinsu Salina ya taso kenan" na katse shi se yace
"Ina ga su ɗin ne, yace wai wata shida suke so a saka wancan ɗin". Ɓata fuska nayi nace "har wata shida?" Seya kalleni yana cewa
"Yayi kaɗan ko?"
"Kaɗan ko dai yawa?" Na faɗa ina ɓoye fuskata. Na zata ze tsokaneni akan abinda na faɗa se naji yayi shiru dana ɗaga kai na kalleshi se naga yayi shiru yana kallon center table ɗin dake aje. Da yar damuwa nace
"Lafiya dai naji kayi shiru?" Ɗan murmushi yayi yace
"Babu komai, kawai ina tunanin yanda al'amura zasu kasance ne. Idan son samu ne ma ni nan da wata uku ma a kawoki gida na sedai uzururrukan da suke gabana bana tunanin a shekara ɗaya ma zan iya kammala su" ya faɗa kamar zeyi mun kuka.

Da sauri na kalleshi jin abinda ya faɗa, ya marairaice fuska yace
"Kin san nauyin da suke kaina Halims. Yanzu fa ba tareda anyi shawara dani ba aka saka bikinsu Fauziyyah yanzu haka a yanda akayi sa ranar saura wata biyu da sati uku bikin. Daƙyar fa na lallaɓa Baba Malam ɗin aka maida sa ranar wata shida a lissafi na idan akayi nata kinga na sallameta sannan na koma kan ginina na ƙarasa se azo ayi sa ranar mu idan na samu yanda nake so ma wata ɗaya ko biyu za'a saka shikenan".

Kallonsa kawai na ringayi na kasa cewa komai, ban ma gane kan lissafin da yake ba. An saka auren ƙanwar sa wata shida se anyi nata sannan azo a fara maganar namu a ƙalla dai shekara ɗaya zuwa da rabi yake sake nemowa akan shekara biyar ɗin da muka kwashe. Karo na farko da Bilal yayi wani abu da naji haushinsa har raina amma bance komai ba na sunkuyar da kai kawai ina jinsa yana cewa
"Kin san na gaya miki harda gadonta na haɗa nayi sponsoring karatu na in ba dan haka ba waye ze ɗora mun wahalar aurenta ace se na mata kayan ɗaki dole?"
"Zaka mata mana tunda ai bata da wani yayan da ze mata bayan kai. Kaine makwafin mahaifinta a yanzu" na faɗa murya a ciki, se yace
"Haka ne idan ina dashi zan mata amma a halin da nake ciki yanzu nima ai ban tsaya da ƙafata ba ga kuma tawa wahalar a gabana. Se yanzu nake dana sani lokacin da Alhaji Lawan yace muyi musanye na bashi kango na ya bani wani gida complete dana karɓa canjin nayi wani abu dasu ƙila da tuni yanzu mun haifi Nur da Nurain ko?" Ya ƙarasa da sigar tambaya. Ɗan murmushi kawai nayi yaci gaba da surutan da duk uzururrukan sa da basa ƙarewa ne kullum yana so yayi kaza da kaza kafin ayi waye da waye jin yanda nake amsa masa maganganun yasa yace mun
"Ko kin fara jin bacci ne naji kina amsawa daƙyar?" Se kawai nace masa eh". Yayi murmushi yace
"Karki damu Halims, in sha Allahu komi ya kusa zuwa ƙarshe kinji jinkirin kuma ze zama alkhairi".

Murmushi kawai nayi na miƙe ganin shima ya miƙe tsaye, muna tafe yana cigaba da surutansa ina binsa da toh har muka je get. Seya juya ya kalleni yana murmushi yace
"Halims menene?" Na buɗe ido na kalle shi nace "me ka gani?"
"Duk yanayinki ya canza mana ko akwai wani abu da baki gaya mun ba?" Ya ƙarasa yana jingina da ƙofa tareda langwaɓe kai yayi kalar dake sake wujijji gani cikin soyayyarsa. Sena sauke kaina ƙasa dan ma karya yaudare ni. Ya cigaba da cewa
"Kici gaba da yi mun addu'a kinji in sha Allah zan baki mamaki"
"Toh, Allah yasa" Na bashi amsa. Yaso ya sake jan hirar amma na bashi uzurin kaina namun ciwo ya tafi. Seda na tattare sauran snacks ɗin na kai kitchen kafin na samu Mama a falo suna kallo dasu Imam. Gefe na samu na zauna ina ɓata fuska sau ɗaya Mama ta tambayeni meya faru nace babu bata sake cemun komai ba.

Wayata dana saka caji ta shiga ƙara daga ringing tone ɗin na gane shine hakan yasa na zareta na wuce ɗaki. Sama sama na ringa amsa masa maganganun da duk kame kame yake can yace mun
"Seda naje aje mashin na shafa naji babu komai nace yau Halims tayi mantuwa"
"Mantuwar me?" Na tambayeshi se yayi yar dariya yace
"Baki packaging mun sauran snacks ɗina ba, sannan abincin ma an manta dashi". Dariya da mamaki ya bani lokaci ɗaya amma se kawai na bishi da cewa
"Kash aiko na manta"
"Ko na aiko a karɓa dan kin san da zan fita ma cewa Hajja nayi kar a ajiye mun abinci" ya sake faɗa, ban san lokacin da nace masa
"Ai kana tafiya su Imam suka cinye"
"Kai, harda girkin da kika mun?" ya faɗa se kawai nace masa
"Ni dama banyi maka girki ba ai iya snacks ɗin nayi" ga mamaki se ji nayi yace
"Toh shikenan Allah ya tashe mu lafiya" daga nan ya kashe wayar.
Mamaki sosai ya kamani, wato dama abinci ya biyo baya lallaima Bilal.
Chapter 4 · 0% Book details