← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 158

Sashe 9

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba wasa nakeyi ba bana son auren nan Alhaji kwata kwata abin yaƙi kwanta mun a rai. Wlh ba ƙaramar murna nayi ba da ya ɗauke ƙafarsa ya dena zuwa itama naga ta fita a batunsa, ni da ka sani da suka ce zasu zo kawai ku ce musu an mata miji tun da dama tun asali ai ba kuɗi suka kawo ba magana kawai akayi" Hajiya Amina ta faɗa bayan da suka zauna da Alhaji Aminu yayi mata magana akan rashin dacewar abin da tayi a ganinsa.

"Me yasa zaki ringa faɗar haka Amina? Ban taɓa zaton zaki shiga layin waɗanda basa son haɗi tsakanin Halima da yaron nan Bilal ba. A duk sanda na kalle su rayuwarsu ta kan tuna mun a yanda muka fara tamu tarayyar" se tayi saurin katse shi tace
"Karka fara haɗa rayuwar mu da tasu domin akwai banbanci"
"Wane banbanci? Irin son da kika nuna mun? Wace irin sadaukarwa ce baki mun ba Amina? A sanda na nemi auren ki ban ko kama ƙafar Bilal rufin asiri ba. Bana manta ƙanin da yan gidanku suka mun me riga ɗaya. Kin ciyar dani, kin tufatar dani kin kuma zauna dani cikin halin matsi har muka kawo yau menene banbanci cikin abinda yake faruwa a rayuwar Halima yanzu?" Alhaji Aminu ya faɗa cikin kwantar da murya.

Hawayen da suka tarar mata a ido ne suka fara sauka, ta saka gefen hijabinta ta share tana cewa
"Ko da na so ka na so ka ne a matsayin ka na Aminu kai ma ka so ni a Amina. Babu son rai ko so. zuciya a tarayyar mu. Baka dashi amma kowa ya shaida kai me zuciya ne kuma kana kan tafarkin nema. Baka taɓa roƙo na nayi maka abu ba kuma na sani a duk sanda na maka abu kana karɓa ne saboda ka faranta mun kuma a duk sanda Allah ya baka dama ka kan kwatanta kyautata mun kaina daidai yanda zaka iya. Mahaifi na ya faɗa mun ya baka aure na saboda ya yarda da kai ya kuma yarda da nagartarka ya kuma san akwai da babu ba zaka wulaƙanta masa ni ba saboda ya yarda tsakani da Allah kake so na. Wace madogara kake da ita da har ka yarda zaka bawa wancan yaron auren yarka?

Ban ce baya son ta ba amma son da take yi masa ya kere wanda yake mata nesa ba kusa ba, kai namiji ne. Be zama lallai ka hango illar dake tattare da irin wannan tarayyar ba. Bance a duk in da son mace yafi yawa yana kasan cewa matsala ba amma muna amfani da abinda yafi faruwa musamman a irin al'umar da muke ciki yanzu. Yanzu ka kalli abubuwan da Halima takeyi, akan Bilal bata ji bata gani ba kuma ta shakkar ɓatawa da kowa. Har ta kai yanzu bata shakkar ɓacin rai na akan duk abinda ze faranta ran Bilal. Tun be aure ta ba take haka ina ga kuma sun zauna me kake tunanin zata zama? Ni dai gaskiya ina jiye mata tsoro domin zuciyata ta kasa nutsuwa akan al'amarin nan mafi sauƙi a haƙura mu cigaba dayi mata addu'a Allah ya fito mata da wanda ya fishi alkhairi".

Shiru Alhaji Aminu yayi kawai, sam ya kasa ganin abinda take kira da matsala cikin al'amarin Halima da Bilal. A iya binciken sa ba'a samu yaron da wani halin banza ko shashanci ba. An san asalinsa, yana da sana'a ga yarinya tana son sa to me ake nema? Sau tari shi ma ya kanga kamar Haliman ta zurma da yawa amma yanayin ta ne a haka tun tana yar yarinya ta kan tsananta son abu, ko cikin kayan wasan ta ta kan tattala tare da kulawa da wanda ta fi so bata taɓa fitar dashi idan suna wasa ta sa'anninta shiyasa yakan mata uzuri akan abubuwa da yawa nata haryar kenan ta bayyar da soyayya. Cikin nutsuwa ya ringa kwantarwa da matar tasa da hankali tare da nunar mata da babu komai. Kamar yanda yasan tana wa yaranta addu'a karta gaza, taci gaba da yiwa Halima in sha Allahu duk ma hasashen da wasu sukeyi baze yi tasiri ba.

"Yanzu haka nan da wace hujja zamu ce zamu hana shi aurenta? Go be fa suka ce zasu zo saka rana naga da ƙorafin ki ya tsaya wasa ba aure zeyi ba yanzu kuma ya yunƙuro se ki zo da wata magana daban Amina ban fa san ki da haka ba na kuma san ba kowa yake zugeki ba illah Labiba kuma zan kirata. Ita dai tunda Halima taƙi ƙanin Alhaji Saleh shikenan ta tsangwami zancen auren ta Bilal" Abban ya faɗa. Seta girgiza kai tace

"Babu ruwan Labiba wlh, kuma ko da taƙi al'amarin tana da hujjoji da ababen dubawa ne ai kuma son da takewa Halima yasa har take adawa da abinda take ganin ze iya zaka matsala a rayuwarta dan dai ka sani ko ni da na haifi Halima dan dai soyayyar uwa da abin cikin ta daban ce amma bazan ce nafi Labiba ƙaunar Halima a zahiri ba" Mama ta faɗa. Se yayi murmushi yace
"Bana in kari da ƙaunar dake tsakanin Labiba da Halima wani haɗi ne daga ubangiji wannan na kuma san duk abinda zatayi akanta zatayi ne don ganin rayuwarta ta in ganta. Ƙaramar uwa da yarta, ai babu me shiga tsakaninsu dan idan aka juyo ta wani fannin muna nan za ta iya baki kunya kuma ta juya tabi bayan yarta. Ni dai abin da zan ci gaba da faɗa miki shine ki ci gaba da yi mata addu'a kawai in sha Allahu e mun ce gara da akayi ba kuma zamuyi nadamar wannan tarayyar ba" da maganganun daya danneta kenan harta sakko tabi ta tasa taci gaba da addu'ar da dama kullum cikinta take.

A daren ta kira Anty Labiba ta gaya mata zancen zuwa sa ranar a take kuma tace a cireta ciki bata cike da iskancin Bilal da Halima. Tun dai taji ta gani ai shikenan mai Allah ya tabbatar da alkhairi. Dariya kawai Maman tayi ta kira Yayarta Hajiya Rumana kawai tace zata yiwa Matar Yayansu Lawan Anty Laure magana tun da taga ta fara harkar snacks na biki, duk da ba'a gidan zasu zo saka ranar ba amma zatayi abin tukuici akai can gidan Baba Salahun.

Washe gari lahadi ƙarfe huɗu na rana Kawunnan Bilal biyu da Aminin mahaifinsa ɗaya suka je saka ranar auren mu gidan Baba Salahu. Kusan a kowanne ɓangare ana al'ada, wasu su kan yi tsohuwar da aka saba akai akwati da kayan sa rana. Wanda suka zamanantar da abun kuma kuɗi suke badawa waɗan su kuma a sanda aka kai kuɗin aure ake haɗawa da na sa ranar ko kuma a haɗo kayan tare da lefe to su dai su Bilal bamu san wanne zasuyi a ciki ba, dama sanda akayi tambaya basu bada komai ba Abba yace baya buƙatar wani kuɗin na gani ina so ko na aure yanzun ma haka nan suka zo da saka rana shekara ɗaya se dai Baba Salahu yayi tsallen albarka yace basu san zance ba.

Watanni shida shine abin da suka yanke zasu aurar da yar su, bayan duk dogon zaman jiran sa da aka sha har idan suna ganin hakan ya musu gajarta to fa suyi haƙuri kawai domin a cikin dangi akwai wanda dama suka ci burin haɗa ta dashi. Aminin mahaifin Bilal ne yace ba za'a yi haka kuma tabbas kam iya lokaci an basu domin be manta ba an tafi shekara ta uku kenan da sukayi tambayar auren kuma shi kansa be san ranar har ta shekara suka shiryo ba da tun kan su zo dama ze gaya musu yayi yawa musamman dama ga bikin ƙanwar Bilal ɗin da za'a yi duk lissafin sa tare zasu haɗe. Haka dai aka rabu, duk sauƙin kai da rashin ɗaukar duniya da zafi irin na Baba Salahun bayan sun tafi se da ya kira Abba yayi masa mitar mutanen fa ko goro basu zo dashi ba balle wani abu na al'ada. Abban yace babu komai.

Irin murnar dana shiga bayan da na samu labarin a watanni shida masu zuwa zan zama mallakin Bilal ba me faɗuwa bace. Har party na haɗa, cikin sa'a washe garin ranar tayi daidai da ranar zagayowar haihuwata dama dan haka na roƙi Mama da muke hi hi yanzu akan zanje gidan Anty Labiba. Bata hanani ba, dama na gayawa Hansa'u da su Baby zamu je gidan zoo ranar birthday na Baby na bawa kuɗi ta yi mana kayan taɓawa na siyi cake da a jiki aka rubuta mun Happy engagement Mrs Bilal to be ban sanar ma Bilal ɗin bama se da na samu na bar gida haka ko suka je shi da abokanansa biyu muka sha hotuna muka ci snacks muka yanka cake bamu ji ma ba na wuce gidan Anty Labiba dan kar zance ya tashi tace ban je ba. Na dai sha zagi a gunta amma ban damu ba, tace kayan gado yan goron dutse zasu mun duk tarin da Mama takeyi a saboda aure na ba zata bari ta ɓarna tar da kuɗin ta ba har kayan kitchen da take siya da wanda itama ta siya mun Amirah zasu ajiyewa nace duk naji.

Shikenan rayuwa ta dawo mun sabuwa, soyayya da shaƙuwar mu da Bilal se abin da ya sake gaba. Na samu ƙatuwar takadda na zana calender ta wata shida kullum da safe na tashi zan soke ranar ki nake yi tamkar na janyo lokaci ni dai buri na da fata na kawai na zama matar Bilal.
Chapter 9 · 0% Book details