← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 158

Sashe 135

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Instruction ɗin jiki ya karanta take kuma ya samu amsar abinda ya daɗe yana ci masa tuwo a ƙwarya cikin tarayyarsu da Zulaihan. A aljihu ya jefa kwalaben guda biyu ya rufe mata drawer ya koma kitchen ya dafa indomie sannan ya koma ɗakinsa.

Wai duk a yaushe Zulaiha ta samu irin wayewar nan bai sani ba? Shi dai a shekarun da suka shafe ko da wasa bai taɓa ganin wata alama da zata ɗarsa zargi ko wani abu zuciyarsa ba. Yana cin abincin maganganun Kawunsu suka shiga dawo masa. Toh ko dama abinda yake magana akai kenan? Ko kuwa akwai wani abun bayan wannan ma?"

Ƙarar wayarsa ta katse masa tunani da sauri ya aje cokalin ya ɗauki ruwa ya sha ganin mai kiran, Jalilah ce ya ɗaga.

Daga can ɓangaren murya washe Jalilar ta ce
"Sweet baka gida ne?"
"Ina gida mana mai ya faru?" Ya bata amsa, ji yayi kamar an ƙwanƙwasa Get kafin a shagwaɓe yaji ta ce

"Amma shine nake ta buga ƙofa kana ji na ba zaka zo ka buɗe ba?"

Ai sai yaji kamar an tsinka masa mari a bazata, yayi firgigit ya miƙe tsaye kamar wanda ya farka daga suma ya ce
"Na'am, me kika ce?"

"Nace ina ƙofar gida kazo ka buɗe, dan Allah I'm stressed enough for today Bilal daga Airport kai tsaye na wuto na gaji kazo ka buɗe mun tun ban faɗi a inda nake ba" Jalilar ta bashi amsa cikin muryar dake nuna gajiyar tata dagaske. Laluben key ɗin motarsa ya shigayi bai ko tsaya saka riga ba dan single ce da three quarter wando a jikinsa ya zura takalmi ya fita bayan ya jefa wayar aljihu ba tareda ya ko katse kiran ba.

Buɗe ƙofar yayi ya leƙa sukayi ido huɗu da Jalilah dake tsaye da ƙaramar akwati a gabanta tana danna waya fuska a haɗe, da sauri ya mayar da ƙofar zuciyarsa ta shiga luguden daka. Bai tsammaci dagaske take ba ya ɗauka dai ta shigo Kanon shiyasa zai tafi ya tarota a inda take ya nemi in da zaiyi mata masauki ashe ita harta ƙaraso ma.

Cikin ɗaga murya Jalilah tace
"Menene haka Bilal? Wane irin wulaƙanci ne wannan?"

Bai amsa mata ba ya wuce ya kunna mota, sai kuma ya fito daya tuna dole dai sai ya buɗe Get ɗin tunda dai motar ba zata fita ta saman katanga ba. Yanda ka san maraya haka ya narke fuska ya nufeta yana cewa

"Bari na ɗakko mota sai muje na kaiki masauki dan Allah". Akwatinta taja ta wuce shi ta shige gidan tana cewa

"A nan naga damar sauka" ya bita da sauri ya riƙe akwatin ta sakar masa ta shige ciki kamar gidanta tana kallon compound ɗin daya sha sabon fenti. Murmushin da Bilal bai san dalilinsa ba ta saki tana cewa

"Gyara aka yiwa gidan ashe? Gashi kuwa ya ƙara kyau" ta wuce falo shi dai kamar wanda aka dasa ya tsaya a guri ɗaya ya kasa bin bayanta.

Turus tayi tana kallon cikin falon kafin ta waiwaya ta kalli Bilal daya sauke kai ƙasa tamkar an ƙure munafuki, har ta buɗe baki zatayi magana sai kuma ta fasa ta ƙarasa shigewa tana kallon gurin. Kusan minti biyu kafin Bilal ya samu ƙarfin guiwar bin bayanta ya shiga falon ta kalleshi fuska babu yabo ba fallasa ta ce

"Ashe dai kayan gurin ne suka ƙara masa kwarjini yanzu kuwa ana shigowa an san gidan gwauro ne" ta ƙarasa da wani murmushi kafin ta miƙe ta nufi ɗaki tana cewa

"Allah sarki Halima sai kuma na ɗan ji tausayinta kaɗan yar yarinya ka mayar da ita bazawara".
Shan gabanta yayi tana dab da buɗe ƙofa ya ce

"Amm an daɗe ba'ayi amfani da gurin ba muje can ɗakina" ta masa kallon daya saka yaji kamar ya fasa kuka dan gani yayi kamar ta gane komai kafin kuma ta saki murmushin daya kasa gane dalilin sa ta juya ya bita a baya suka fice daga falon. Sai da tayi wanka Bilal na tsaye a ɗakin kamar dogari ya kasa zaune ya kasa tsaye har wani zazzaɓi yaji yana neman saukar masa saboda tashin hankali.

A ƙasa ta saki towel ɗin bayan ta fito ta buɗe akwatinta ta shiga shafa mai shi dai tunda ya kalleta sau ɗaya bai sake ba ya mayar da idonsa ƙofa yana amsa mata maganar da takeyi masa da Eh ko Aa kawai harta gama shiryawa lokacin aka kira sallar magriba ta kalleshi ta ce

"Ka shirya zaka rakani wani waje ne"

"Toh bari nayi sallah" ya bata amsa da sauri kamar yana jira. A ɗakin yayi sallah ya jirata itama tayi kafin suka fita ta shiga mota bayan ya kunna yace mata yana zuwa ya koma ciki da sauri. Akwatinta ya ɓoye cikin wardrobe da sauran kayan data bari akan gado.

Sai da suka hau titi kafin ta faɗa masa in da zasuje, Calido suka zauna jiran mutumin da zata gani ɗin shi dai Bilal ya samu guri ya zauna fuskarsa har ta rame saboda tashin hankalin bazata daya sameshi ita tayi musu order abinci tana danna wayarta tana kallon Bilal jefi jefi tana sakin murmushin da ita kaɗai ta san ma'anar sa. Sai da suka fara cin abincin kafin mutumin suka iso su biyu, hannu suka bawa Bilal suka gaisa kafin suka zauna tace suyi order suka ce Aa a ƙoshe suke sun gode.

"Wannan Ahlan kenan, kuma shine wanda na siyarwa da gidan nan na Rijiyar Zaki, amma kuma ɗazu da safe yaje gidan wai ya tarar da mutane a ciki kuma mutumin ya tabbatar masa da siyan gidan yayi ba wai aro aka bashi ko haya yakeyi ba" Jalilah ta faɗa tana nuna mutumin da tun zuwansu Bilal yake jin kamar ya sanshi a wani gurin. Bilal dake zuƙar lemo yayi saurin furzar dana bakinsa saboda yanda ya tasarma bi masa ta hanyar wucewar iska, ya shiga tari kamar ba gobe gaba ɗaya suka rufu kansa suna yi masa sannu. Kusan minti uku ƙafin ya lafa masa idanuwansa sunyi jazir sau ajiyar numfashi yakeyi yana zare ido.

Jalilah ce ta sake kallon mutumin data kira da Ahlan ta ce
"Wannan shine Bilal kuma shine caretaker gidan, kamar yanda na gaya maka ka kwantar da hankalinka babu wata matsala zai yi bincike duk abinda yake da akwai zaka ji mu yanzu sai kuyi exchanging contact ko?" Ta ƙarasa tana kallon Bilal daya zama hoto a gurin daƙyar ya iya miƙawa Ahlan ɗin wayarsa ya saka masa number yayi dialing kafin sukayi musu sallama suka wuce.

"Yanzu ya akayi har wani ya shiga gida ya zauna har yana iƙirarin siyan gidan yayi kai kana nan baka sani ba?" Jalilah ta faɗa bayan wucewar su Ahlan. Bilal dai shiru yayi dan zuwa yanzun ya gane kawai so takeyi ya tona kansa da kansa amma ta rigada ta san komai dukda bai san zurfin abinda ta sani ɗin ba, ƙaramin tsaki yaji tayi kafin ta miƙe tana kallonsa ta ce

"Muje ka kaini Hotel"
"Kayanki fa?" Ya tambayeta da sauri ta ɗan kalleshi kafin ta ce
"Oh, to muje na fara ɗauka sai mu dawo". Suna dab da fita daga gurin idonsa ya hango masa wata kamar Zulaiha tareda mutum biyun da suka rabu da su yanzun nan, tsayawa yayi yana kallon su da yarinyar ta juyo kuma sai yaga ba Zulaihar bace dan kayan jikinta ma ba wanda Zulaiha ta fita dasu bane kawai shaiɗan ne ya haska masa take kuma ya tuna a inda ya san fuskar mutumin wanda ya biyo Zulaiha ne ranar da sukaje siyan Shawarma.

Sai da suka shiga layin gidan kuma yaji daya sani fara kaita Hotel ɗin yayi kafin ya dawo ya ɗaukar mata kayan yanzu idan Zulaiha ta dawo gida fa?

A mota ya barta ya shiga, ganin ƙofar falo a buɗe ya tabbatar masa ta dawo dan haka take sau dubu zai rufe mata ƙofar sai ta buɗe halayyar yan ghetto dai ga fanka ga Ac amma wai iska take sha. Kamar ɓarawo haka ya ringa sanɗa har ya shiga ya ɗakko akwatin, yana kaiwa Get yaji muryar Zulaihan a bayansa tana tambayar yaushe ya shigo, bai kulata ba ya fita itama ta taɓe baki ta koma ciki abunta.

Sau sha biyu saura ya baro gurin Jalilah kuma har suka rabu bata sake tayar masa da maganar gida ba ta dai ce ya zo da safe da wuri, ya wuce zuciyarsa fal tambayoyin daya kasa yi mata. Bashida tabbacin ta san shi ya siyar da gidan ko ba haka ba sannan kuma in dai ita ta siyar da gidanta da kanta kenan tana sane ta bashi fake takardu idan haka ne kuma na Shago ma ita ta canza su, toh zarginsa takeyi dama ko me?

Yaji daɗi da Zulaiha bata je ɗakinsa ba dan bai ko kwanta ba kwana yayi yana safa da marwa idan ya gaji ya zauna tunani kamar ƙwaƙwalwarsa zatayi bindiga yanzu yaya zaiyi? A ina zai nemo Miliyan Hamsin da biyar ɗin da zai biya Alhaji Lawan kuɗin sa? A ina zai samu kuɗin da zaiyiwa Fadila kayan ɗaki ya gujewa fushin Hajja? Ya zaiyi da batun aikinsa wanda a yanzu ne ya fahimci kasassaɓar da yayiwa kansa da yayi wasa da shi? Sannan duk bayan wannan ya zasu kwashe da Jalilah?
[5/27, 7:16 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 56*
Chapter 135 · 0% Book details