Sashe 23
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To ban da shirme kuma kukan na menene? Ai lafiya ce take ɓuya. Ki kira Nasir ko wani cikin abokanan sa na gurin aiki kiji ko suna tare tun da hankalin ki be kwanta ba. Amma babu komai ma nasan tun da kina gida ma ai yana haka ku wuni ba kuyi magana ba se daga baya ya baki uzuri" abin da Mama ta faɗa kenan amma hakan be sa naji hankali na ya kwanta ba tun da ni dai tun da mukayi aure ko ƙofar gida ze fita se ya gaya mun. Layin ƙanin sa Abubakar na kira se dai shima na tarar a kashe wannan ya sake dugunzuma hankali na kawai na zauna na fashe da kuka na rashin madafa. Motsin buɗe ƙofa ya farkar dani firgigit daga baccin daya sure ni ba tare da na sani ba ina tsaka da kuka. Dishi dishi nake kallon sa ya tsaya shima yana kallo na kafin ya fara takowa cikin falon se na miƙe da sauri na nufe shi, tsayawa yayi na faɗa jikin sa tare da fashe wa da kuka ina cewa
"Ina ka tafi? Hankali na ya tashi ina ta kiran wayarka baka amsawa me yasa kayi mun haka?"
A dake cikin yanayin da banyi zato ba bayan ya janye ni daga jikin sa ya kalle ni yace
"Kin aike ni ne balle ki bi ba'asin in da na tsaya?"
Se na bishi da ido kawai na kasa cewa komai, ya yi tsaki tare da zagaye ni ya wuce ciki.
Kamar wata wawiya haka na rakashi da ido har ya shige cikin ɗaki tare da banko ƙofa. Tamkar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka naja ƙafafu na da suka yi sanyi na zauna kan kujera haɗi da zabga tagumi. So nake na tunano ta in da na kuskurewa Bilal, me nayi masa da yayi zafi haka? Ina nan zaune ya sake fitowa fuu ya shige kitchen ina jiyo shi yana birkita kwanuka kafin ya sake fitowa da kofin shayi a hannun sa se dublan a plate. Nan cikin falon ya zauna bayan daya kunna Tv ya shiga shan shayin sa, yanda yayi tamkar be san da wanzuwata a gurin ba yasa na fashe da kuka sosai har da shashsheƙa se gani nayi ya miƙe tsaye da kofin shayin sa da alama gurin ze bar mun. Bazan iya jurewa ba, ina buƙatar nasan takamaiman dalilin fushin da yake yi dani se na miƙe da sauri na isa gaban sa na durƙusa tare da riƙe ƙafar sa ina ci gaba da kukan nace
"Ka faɗa mun me nayi maka kake mun irin wannan horon Bilal?"
"Baki ma san me kika mun ba kenan?" Ya faɗa yana ɗage kai sama a ƙoƙarin hana tausayi na yin tasiri a zuciyar sa. Girgiza kai nayi ina ci gaba da kukan nace
"Wlh ban sani ba, ka taimaka ka gaya mun me na maka bazan iya cigaba da jure fushin ka irin haka ba"
"Shikenan tun da baki san me kika mun ba Halima, duk ranar da kika tuna se muyi maganar" ya faɗa yana janye ƙafar sa ya wuce cikin ɗaki se dai be kulle ƙofar ba a buɗe ya barta. Zuciya ta na raya mun na rabu dashi da kansa ze zo in da nake idan ya gama fushin amma zuciyar dake cike da so da begensa ta rinjaye ni haka na sake bin sa ɗaki ina kuka ina roƙon ya gaya mun abin da na masa amma se da mula dan kansa kafin ya maido mun da zancen kilishi"
"Kayi haƙuri, ban kawo hakan ze ɓata maka rai ba amma zan kiyaye haka ba zata sake faruwa ba a gaba" na faɗa ina goge hawaye. Duk da haka be wani sake mun koma yanda muke gaba ɗaya ba se da aka kwana biyu ranar laraba ya fita da yamma babu jimawa Mu'azzam ya zo ya kawo mun manya manyan kaji guda goma in ji Abba da ƙwai shima crate goma dake ya buɗe gidab gona ana kiwon kaji da kifi yanzun an fitar da layers ne da suka dena ƙwai shine aka kawo mun rabo na. Tuwo nayi niyyar yi ganin kajin yasa na fasa na haɗa lafiyayyen farfe su irin wanda Bilal ke so na kwaɓa fulawa na gasa bread dan na lura yanzu abin laifi baya yiwa Bilal yawa tsaf idan na kira shi nace ya taho mana da bred ɗin se ya maida abin na rigima.
Se da akayi sallar isha'i kafin suka shigo gidan shi da Abubakar da Halifa ɗan Babbar yayarsu Anty Na'ima. Can falon sa ya buɗe musu suka shiga na kai musu ruwa da lemo ganin ya fito da laptop ɗin sa yasa na fahimci wani abun zasu yi ba yanzu zasu tafi ba dan haka na ɗora musu jallof ɗin taliya na saka musu kazar a ciki, na sauke kenan na jiyo maganar su a tsakar gida alamun sun fito zasu wuce hakan yasa na leƙa da sauri na sanar musu ga abinci na sauke ina kuma zasu tafi?
"Da kin barshi Anty sauri mukeyi" Abubakar ɗin ya faɗa, zanyi magana Bilal ya rigani yace
"Ku wuce kawai kasan na cewa Nasir ya jira ka kai masa flash ɗin nan kar ku ɓata masa lokaci"
"Haba dai duk saurin da sukeyi ai sa jira dai su ci abincin, idan kuma ba zaku ci anan ba bari in juye muku to se ku tafi dashi kawai" na tare shi. Naga irin kallon daya mun amma ban kawo komai ba na koma kitchen, falon suka shigo suma suka zauna Bilal ya bini kitchen, yana tsaye a kaina na juye musu taliyar gaba ɗaya a kula tun da dama su na dafawa na saka a kwando na haɗa musu da ruwan gora da lemo yana nan tsaye a kitchen ɗin na fita na basu mukayi sallama suka tafi. Bana zaton sun kulle mana ƙofa Bilal ya hau ni da faɗa tamkar ze doke ni, akan me yace su tafi zan ce su tsaya in zuba musu abinci?
Mamaki ya sa na kasa ce masa komai, waccen ranar yayi faɗa dan na yiwa yar uwata kyauta yau kuma yana yi saboda nayiwa nasa dangin menene matsalar Bilal ne? Ban san ya akayi ba kuma ya rage banbamin da yakeyi yana cewa
"Bana so, karki sake mun irin haka a gaban yara salon suce ban isa da ke ba kin raina ni in ba haka ba ya za ayi na baki umarni ki take kiyi wanda ranki ya raya miki? Yanzu da kika juye musu abincin duka ni wanne zanci"
"Allah ya baka haƙuri" na faɗa a sanyaye kafin na shige kitchen na barshi. Na zata ze shige ɗaki ya kulle irin na waccen ranar se kuma na tarar dashi a zaune yana kallo, se da na gama jera abubuwan da zamuyi amfani dasu akan dining kafin nayi masa magana ya taso. Sosai yaci naman nayi mamakin da ban ji ya tambaye ni daga in da aka samo su ba tun da yasan bamu da sauran naman kaza a gidan se wanda yake cikin miya. Kafin mu kwanta se da ya sake ci ya kuma jaddada mun in aje masa sauran a fridge karya nema gobe nace masa na bawa wani.
A haka muka cinye satin, zaman mu ya koma kamar da har ma ya zarce da daɗi da farin ciki. Cikin abin da yasa nake ƙara son Bilal mutum ne shi da baya son jikin sa, ina kwance zeyi shara yayi mopping wani lokacin har girki yake ɗora mun, ranar daya ga ina haɗe kayana da sukayi datti kafin na samu wanda ze yi mun wanki kamar wasa yace na fita dasu tsakar gida, na yi tunanin almajiri ze nemo na fitar na ci gaba da gyaran ɗaki na se kawai ganin sa nayi ta window yana shanya kayan ashe da kansa ya wanke mun. Wannan yasa na ke ƙara son sa saboda ya bani mamakin na same shi yanda ma banyi zato ba. Abu ɗaya yake bani tsoro da halayyar sa yanda yake birkicewa lokaci ɗaya akan ɗan ƙaramin abu da be taka kara ya karya ba, wani lokacin ya sakko da wuri wani lokacin ko se naji na tsani kaina na tsani dalilin daya sa na zaɓi rayuwa dashi kafin ya sakko idan komai ya wuce kuma se ya zama kamar wani saɓani be taɓa shiga tsakanin mu ba.
A haka muka ci sati huɗu da aure se lokacin kuma hutun daya ɗauka ya ƙare ya koma bakin aiki, da safe idan ze fita har kuka nake yi saboda sabon da nayi na kasancewa tare dashi a ko da yaushe bana taɓa samun nutsuwa se naga ƙarfe huɗu tayi lokacin shigowar sa gida yayi. Bahaushe yace yau da gobe bata bar komai ba, a hankali cefanen mu ya fara ja baya. Ɗan yun kayan miya ne suka fara ƙarewa ya rage albasa kawai nake da, da yake ina da dafaffu a freezer markaɗe da jajjage se banyi azancin sanar dashi ba. Ranar wata asabar yana gida, da rana yace na dafa mana shinkafa da wake jollof nayi amfani da bushashshen kifi. A plate ɗaya na zuba mana, har mun fara ci yace na ɗakko masa yaji wai abincin yayi masa salam da yawa dake da manja nayi. Dukda ya saka yajin ya ce beyi masa yanda yake so a bakin sa ba dan haka ya tashi ya tafi kitchen da kansa, se da ya ƙwala mun kira naje yake tambaya ta ya yaga babu kayan miya?