← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 158

Sashe 117

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gurin ƙarfe uku Anty Labiba ta sake shigowa ɗakin lokacin ina zaune a ƙasa na rafka tagumi hannu bibbiyu abin duniya duk ya taru ya mun yawa, shikenan fa na zama bazawara.

"Da wannan zaman ke ba bacci ba da tashi kikayi kika ɗauro alwala kikayi sallah sai kiji sanyi a ranki" ta faɗa tana kallona. Na haɗiye yawu daƙyar kafin na gyaɗa mata kai alamar "toh".

Kan gado ta zaune gefen in da nake cikin taushi ta ce
"Menene matsalar ki Halima? Nayi zaton ke da kanki kika ce ba zaki koma ba ya sake ki yanzu kuma akan me zaki takura kanki kiyi ta koke koke bayan kuma abinda kike muradi ne ya tabbata?"

Hawaye ya shiga zubo mun ta dakatar dani ta ce
"Ba kuka na ce ki mun ba ki buɗe baki muyi magana ta fahimta kawai nake so"

"Ina jin zafin abinda ya mun har raina Anty amma ina son sa, ji nakeyi kamar ba zan taɓa iya rayuwa da wani namiji bayan Bilal ba" na faɗa bayan da nayi ƙoƙari tsayar da kukan da na fara.

Ta dafa kaina ta ce
"Sai kuma me?"
"Kuma ina duba makomar yarana idan mun rabu kinga gashi yanzu har ya fara cewa zai ƙwace su"

"Da kuma me?" Ta sake tambaya nayi shiru tayi murmushi ta ce
"Ki faɗa mun duk abinda yake ranki, ko da ban taɓa makauniyar soyayya irin taki ba amma nima ina son mijina ina kuma da yaya, ko bisa kuskure nayi tunanin wata rana zan iya rabuwa da shi ina jin zafi har raina dan haka zan miki uzuri har idan kina da ƙwaƙƙwarar hujja kuma na gamsu na miki alƙawarin zan wuce miki gaba in fahimtar da Mama da Abba har suma su fahimce ki".

"Ni babban abinda ya fi damuna dama kowa sanda zan aure shi sai da ya ce suna nan zan dawo, ba iya ku na cikin gida ba dangi da mutanen unguwa duka kowa idonsa da kunnuwansa na nan kawai jira ake aji aurena ya mutu a fara yi mun dariya da Allah ya ƙara" nayi ƙarfin halin sanar mata da damuwar da take cin raina.

Wani uban ranƙwashi ta sakar mun a tsakiyar kai kafin ta lailayo ashar ta maka mun kamar ma ta manta da tsakiyar dare ne ta balbaleni da faɗa tana cewa

"Dan ubanki sai munyi dariyar Allah ya ƙara kuma tun daga sanda ya fara auna miki abinci muke miki ita. Wato saboda gudun kar ayi miki dariya ya saka zaki zauna ki lalata rayuwarki ki kashe kanki ƙarshe ya ɗakko ciwo ya shafa miki ya ƙara jefaki a masifar da ta fi wacce kike ciki ko? To ki kiyaye ni, kuma wlh maganar nan ta mutu daga nan.

Na rantse da Allah kika koma gida kika ce zaki cigaba da tayarwa da su Mama hankali sai irin dukan da Mu'azzam yayiwa jakin zan saka ke ma ya miki tunda gashi nan bugu ɗaya da yaji wahala ba ja in ja ya baki takardarki to kema idan aka miki irinsa salin alin iskokan da suke taya miki kina iskanci da layla da majnun ɗin kan nako duk zasu kama gabansu".

Ni dai sosa in da ta ranƙwashe ni kawai nake hawaye ya cika mun ido amma ba damar na bari su zubo dan da alama nata mutanen suna kusa karta mun rotse. Ashe dagaske ita ta saka Mu'azzam ya daki Bilal,

Tsawa ta buga mun ta ce
"Tashi ki ɗauro alwala kiyi sallah, tunda kika auri shaiɗani ibadarki ma sai a hankali dama ta ina kike zaton zakiga dai dai a lamuranki?"

Haka na tashi na yo alwalar kuma da na fara sallar musamman dana tattara hankalina sai na ji nutsuwa ta fara saukarmun hatta ciwon kai da jirin da nake ji kafin na idar da sallolin duk sun ragu, kamar gaske lokacin da Hansa'u ta zo har addu'oi ta bani da wurudai ina yi kuma sosai na samu nutsuwa a lokacin ban san yanda akayi na watsar na sake komawa yar gidan jiya ba.

BILAL
Asibiti Nasir ya ce zai kai shi bayan sun bar gidan amma yaƙi ya ce ya kai shi gida.

"Amma dai da munje, ba fa ƙaramin duka ya maka ba wlh kar kaje ya bugeka a in da zai iya maka illah" Nasir da har ransa daɗi ya ji na dukan abokin nasa da akayi ya faɗa. Cikin sauƙi Allah ya ƙwatar mata haƙƙinta dukda yaga alamar Haliman kamar kurarin banza kawai takeyi kamar dai har yanzu tana son abokin nasa.

"Ni dai ka kaini gida, kuma wlh idan na ji maganar nan a bakin wani Nasir ba zata mana da daɗi ba" Bilal ya faɗa da ƙyar dan yana jin jiki. Nasir ya guntse dariyar sa ya cigaba da tuƙi yana satar kallonsa.

"Wlh sai na nuna masa shi ƙaramin mahaukaci ne, sai ya san ya dakeni" Bilal ɗin ya sake faɗa shi dai Nasir bai ce komai ba har suka isa gidan ya shigar masa da mota ya rakashi ciki ya tambaye shi ko akwai abinda yake buƙata ya ce babu daga nan ya masa sallama ya wuce gida akan zai dawo da safe ya duba shi.

Kwana yayi yana saƙa da warwara akan matakin daya kamata ya ɗauka akan Halima domin duk ita ta shirya komai, yayi ƙwafa ya ɗauki wayarsa ya kunna. Message ɗin Zulaiha ya shigo dama kuma saboda itan ya kashe wayar suna fitowa daga gidansu dan karta dame shi da kira yana gurin Haliman bai ko karanta ba ya lalubo number Halima ya aika mata da saƙo akan karma ta ɗauka ta ci galaba akansa kuma zai karɓi yaransa, maganar yaran ya san ita kaɗai ta isa ta sake zargo masa wuyanta dan ya san ƙulafucinta akan yaran ba zata taɓa yarda a raba su ba.

Yana gama turawa ya latse wayar zai sake kashewa sai ga kiran Zulaiha ya shigo, ya amsa, cikin asalin muryar da ya santa da ita mai laushi cike da kunya da kuma nutsuwa ta masa sallama.

Ya saki ajiyar zuciya, abinda yake akanta ya motsa masa sai ya gyara kwanciya yana cije baki saboda yanda duk jikinsa yayi tsami a hakan ma dan ya gargasa da ruwan zafi sannan ya shafa Aboniki kuma ya sha pain relief.

Ta gaishe shi abinda rabon da ta masa tun randa aka ɗaura musu aure.

"Ashe ɗazu kazo Yaya Bilal" ta faɗa. Ya buɗe ido da mamaki kafin ya ce
"Bangane ba? Ba kina gidan ba sanda muka zo?"

"Yanzu Umma take gaya mun da duk abinda Kawu ya muku, dan Allah kayi haƙuri, na rasa mai muka tsarewa Kawu a duniya da kwata kwata baya ƙaunar mu kullum bashi da wani buri illah na ya tozarta mu mu da mahaifiyarmu" ta sakw faɗa cikin shirin yin kuka. Da sauri ya tare ta da cewa

"Me aka ce yayi mana? Ni ai babu wani na rashin jin daɗi daya faru amanarku kawai ya bamu ya ce baya son kawo ƙara duk abinda ya faru muyi hukunci da kanmu in dai ba abun yayi girma bane"

"Kawai ba zaka faɗi gaskiya bane amma Umma ta gaya mun ya ci muku mutunchi sosai" ta faɗa tana sakin kuka. Duk sai ya diririce ya ringa mata rantsuwa akan shi wlh ba abinda Kawu ya musu idan ma yayi toh hankalinsa baya gurin bai fahimta ba.

"Shikenan toh tunda ka ce haka, ya Anty Halima? Ya su Al'amin kwana biyu ko motsinsu bana ji" Zulaihan ta sake faɗa bayan ya gama lallaɓa ta tayi shiru. Ya sauke numfashi ya ce

"Yau suna can gidansu sun je yini zanje na ɗakko su kuma kaina ya fara ciwo shine kawai na ce su kwana acan" ya lafta mata ƙarya. Tayi wani miskilin murmushi ta ce

"Allah sarki, Anty Halima dai akwai haƙuri gaskiya ko sau ɗaya banji kace tayi rigima irin yanda mata sukeyi idan za'a musu kishiya ba, ko dai bata sani bane?"

"Waya gaya miki? Tayi abunta mana kawai dai ba da yawa yanda mata sukeyi ba; kin san na faɗa matata ta dabance ita" ya bata amsa. Ya ji sauyi a muryarta ta ce

"Allah sarki mu da ba na daban ba"
"Ke kuwa ai kece asalin ta daban ma" ya faɗa ta ce
"Hmm" kawai.

"Amma ɗazu kika ce bakya nan muka zo bayan kuma na ganki har magana munyi?" Ya canza akalar maganar, sai ta ce

"Wlh kwana biyu na rasa mai yake damuna. Tun bayan da aka ɗaura mana aure ni dai sai in ringa ganin abubuwa suna faruwa kamar mafarki nakeyi. Umma ta ce kamar wai iskokai ne suke taɓa ni wani lokacin sai na canza nayi ta abubuwa kuma daga baya idan na dawo hayyacina ba zan tuna mai ya faru ba" ta faɗa. Bilal yayi shiru yana juya maganganun a ransa kafin ya ce

"Amma dama kina da matsalar jinnu ne tsayin lokacin nan ban taɓa sani ba?"

"Wlh nima ban sani ba amma Umma ta ce wai ƙila na gado ne itama haka suka mata sanda aka mata aure amma tana tarewa shikenan suka barta dan ko magani ba'a nema mata ba Kakarsu tace idan aa mata magani za'a gayyato mata wasu ne dan su waɗannan ɗin da kansu zasu tafi ko ba'a musu komai ba toh shine yanzu da Anty Habiba har ta ce muje Ɗanfodiyo Umman ta ce a dakata dai zuwa in tare idan basu rabu da ni ba sai muje"

"Da aljanun zaki tare kenan?" Ya faɗa kamar a tsorace. Tayi dariya ta ce
"Bafa a jikina suke ba kawai shafata suke yi"

"Duk ɗaya ai, kin san yanda kike birkicewa kwana biyun nan kuwa? Harfa zagina kikeyi"

"Subhanallah zagi?" Ta faɗa cikin rawar murya, jin zata saka masa kuka yayi saurin cewa

"Wasa nakeyi amma dagaske dai in zai yuwu gara a fara neman maganin tun yanzu dan gaskiya bana jin daɗin yanda kike canzawa har na fara tunanin ko dama dai haka halinki yake ɓoye mun kikayi?"

"Yanzu tsahon shekarun da muka ɗauka Yaya Bilal har akwai wani hali nawa da zai ɓoyu ace baka sanshi ba?" Ta faɗa cikin kuka. Yayi tsaki ya ce
Chapter 117 · 0% Book details