← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 158

Sashe 136

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana uku Jalilah tayi a Kano ta wuce Abuja bayan ta bar alhakin sauke kayan da suka fara isowa a hannun Bilal. A tsakanin kwanakin har rama yayi; duk wanda ya sanshi kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci yana cikin damuwa matuƙa, duk in da yake tunani zai buga lissafi ya fita abu ya gagara, idan ya haɗo nan sai can ya rushe ga Alhaji Lawan ya taso shi a gaba da zancen kuɗinsa dan tuni ya kwashe kayansa ya bar gidan kamar yanda ya ce har Ahlan mamallakin gida na asali ya saka an sake gyara ko ina sai jiran shigar amarya kawai.

Yana kwance idanuwansa a rufe kamar mai bacci amma a zahiri idonsa biyu, Zulaiha ta shiga ɗakin tun kafin kuma ta isa gareshi ya shaƙi kamshin turaren da yake jansa gareta tamkar mayen ƙarfe duk sanda ya shaƙe shi, bai motsa ba dukda yanda lokaci ɗaya hankalinsa ya fata tashi kuma jikinsa ya amsa har ta iskoshi ta zauna gefen ƙafafunsa cikin salo ta shiga shafa sangalalen ƙafarsa tana kiran sunansa a hankali, duk yanda ya so ya daure amma ina sai da taci galaba akansa.

Haka ya ringa aiki da iya ƙarfinsa tsayin lokaci har saida ya gaji kafin ya saketa ya kwanta a gefe yana mayar da numfashi. Cikin hayyacinsa dai bai taɓa irin wannan daɗewar ba sai fa sanda take saka masa wannan abun daya ɗauke ya kuma yi mamakin yanda bata tambayeshi ba ko da yake ai da kunya.

Tsaki mai ƙarfin da Zulaihan ta saki ya saka ya juya ya kalleta da mamakin dalilin tsakin, ta tunzura ƙaton bakinta gaba kafin tace

"Wai wane irin wulaƙanci ne haka Bilal? Yau kwana nawa baka ko shiga ɗakina ba balle ka sauke mun haƙƙina? Sannan yanzu ni na kawo kaina babu wani dogon wasa ba komai ka faɗa mun kalli ko minti 5 bakayi ba ka wani jibge kamar wani kayan wanki toh wlh ni ban gamsu ba, dama na san kai lusari ne shiyasa nafi gane inyi da kaina amma kaƙi; toh wlh ka tashi dan ni ban ma fara jin komai ba" ta ƙarasa tana ƙoƙarin hayewa jikinsa.

Bilal dake kallonta cike da al'ajabi yayi saurin janyewa kafin ya kalli agogo dan ya tabbatar da minti biyar ɗin da tace, karfe takwas da minti goma t shigo ɗakin yanzu agogo yana buga takwas da rabi har da mintoci a sama a ƙalla suk ɗauki sama da minti 15 tare amma shine take cewa minti 5 tsabar ta raina ƙoƙarinsa?

Ganin da gaske takeyi tana neman danneshi da ƙarfi ya saka ya buga mata tsawa kafin ya tashi zaune yana kallonta ya ce
"Mai yake damunki? Me kika sha?"
"Ni babu abinda na sha kuma lafiya ta ƙalau lafiyar ce ma ta kawo haka kai zan cewa mai yake damunka? Malam ka nemi maganin sanyi da basir kawai dan ni ba irin tsohuwar matarka bace" ta faɗa tana wani juya ido. Sai ya kasa ce mata komai kawai ya zuba mata ido yana kallonta, shi dai tunda yake da Halima bata taɓa raina ƙoƙarinsa ba kullum cikin kwarzantashi takeyi tana nuna masa shi ɗin sadauki ne nagaske amma yau shi Zulaiha ta kalla ido da ido ta kirashi da lusari?

Ya sha tsallake Halima a lokacin da shi da kansa ya san tana buƙatar kasancewa tareda shi amma bata taɓa ƙorafi ba, sau da yawa zata iske shi amma ya ce mata bacci yakeji kuma haka zata barshi bai ko taɓa damuwa da wane hali zata shiga ba amma yau ga wata bayan ya biya mata buƙatar ta raina har tana ƙoƙarin danneshi da ƙarfi

"Ni dai ban yafe ba wlh" ya tsinci kalaman Zulaiha kafin ta sake sakin tsaki ta fice daga ɗakin ta barshi a tsaye cikin maɗaukakin mamaki. Wanka ya shiga tun yana ciki kuma yaje jiyo ƙarar wayarsa dan haka yayi sauri ya fito a zatonsa Hafiz ne dan ya kirashi yana so ya masa zancen salaryn sa ko akwai yanda zai taimakeshi sai dai bayan daya fito ya duba wayar ya tarar Alhaji Lawan ne ya kirashi. Tsaki yayi ya ajiye wayar ya shiga shiryawa dukda dare ya farayi amma dole ya fita.

Sai da ya hau titi kafin ya sake duba wayar, saƙon daya gani ya buɗe, ƙirjinsa ya huga dum kansa ya sara, gefen hanya ya samu yayi parking ya shiga ƙoƙarin neman layin Nasir amma cikin rashin sa'a akace a kashe yake. Gidan Nasir ɗin ya nufa kai tsaye, Nasir yayi shiru yana saurarensa har yayi shiru kafin ya ce masa

"Ya kirani tunda yamma ya faɗa mun idan ya kiraka baka ɗauka dan haka ya yanke shawarar kai maganar gurin shari'a, tun farko Bilal sai da nace maka ka haɗa kuɗin mutumin nan ko da ace basu cika ba ka rage masa wani abu a zauna ayi rubutu ka faɗi nawa zaka ringa bashi kuma zuwa tsahon wane lokaci amma kaƙi, yanzu ga abinda nake guje maka nan yana shirin faruwa".

Tsaki Bilal yayi ya ce
"Ban gane in biya kuɗi ba saboda me?"
"Au saboda me ma kake tambaya?" Nasir ya faɗa cike da mamaki, tsaki Bilal ya sakeyi kafin ya ce

"Look Nasir, ni fa ba wasu kuɗi da zan biyashi. Gida ya siya kuma d shaidu da komai ya biya kuɗi an bashi takardu akan me yanzu zai zo da wani rainin wayau? Nima fa gidan nan siyan sa nayi kuma na siyar masa, ai kamata yayi ya nemi wanda ya zo ya ce shima ya siyi gida idan ma shari'a ce dashi ya kamata yayi"

"Toh idan aka je gaban shari'ar na tabbatar in dai ba mahaukacin Alƙali aka samu irin ka ba abu na farko da za'a farayi shine kowa ya zo da wanda ya siyi gida a gurinsa nan kuma wa zai kawo?" Nasir ya faɗa yana buɗe murfin motar, Bilal ya watsa hannu alamar Oho, Nasir ya girgiza kai cike da takaici ya ce
"Shikenan sai da safe" daga haka ya fita daga motar.

Daga gidan Nasir Bilal gidan Hajja ya wuce, fuska ba yabo ba fallasa ta karɓe shi abinda bai zata ba dan tun waccen ranar bai sake zuwa gidan ba a waya ma sau biyu ya kirata kuma duk bata amsa ba shiyasa daya ga fuskarta a sake yanzun abin ya bashi mamaki ya kuma sha jinin jikinsa dan ya san da wahala idan ba tarko zata masa ba.

"Ka ji ɗan albarkan yaron nan yace ba sai ta tafi da komai ba ya rigada ya zuba abunsa" Hajjan ta faɗa masa, yayi ɗan murmushi ba tareda ya ce komai ba sai Hajjan ce ta sake cewa
Asabar ta sama ɗaurin aure"

"Amma Hajja wai a gurin wa akaje neman auren da har aka tsayar da lokaci?" Ya faɗa yana kallonta ta zabga masa harara tace
"Kai a gurin ubanwa aka nema maka naka auren?"

"Amma ni Hajja mun daɗe da yarinyar, na santa na san iyayenta na kuma san duk halayyarta sa'annan ni namiji ne shari'a ta yarjemun da na wakilci kaina a neman aure. Gaskiya ya kamata ace anyi bincike asan wanene wanda zata aura ɗin asan asalinsa da kuma menene sana'arsa, zamanin nan da mugaye sukayi yawa mutum yazo yana wasan kuɗi irin haka ai ya kamata a saka masa alamar tambaya" ya faɗa kansa a ƙasa.

Banza Hajjan tayi masa kusan minti biyar kafin tace
"Sai ka saya mata ɗankunne da sarƙa da kuɗin kayan ɗakin"

"Ni fa wlh Hajja bani da wasu kuɗi yanzu, kafin lokacin idan na samu zan bata amma ban ɗauki alƙawarin siya mata Gwal ba" ya bata amsa, ta watsa masa wani kallo kafin ta kai ga magana ya rigata kamar zai fasa kuka ya ce

"Wlh Hajja ina cikin matsala. Duk yan kuɗaɗen da suke hannuna sun ƙare a harkar bikin nan waɗanda na saka ran zan samu kuma abin bai yiwu ba yanzu haka account ɗina wlh ko dubu ɗari bani da ita".

"Wannan kuma kai ta shafa ba ni ba, wato ni da wuyar naƙuda da shan wahalar raino harka girma sai da ka zama abin moro sannan zaka koma bawan can wata ƙatuwa da iyayenta ko? To wlh baka isa ba ko sata zakayi kaita shafa ni dai na gaya maka ka siya mata sarƙa da ɗankunne" Hajjan ta bashi amsa cikin ko in kula. Har kusan sha biyu yana gidan, sai da Abubakar ya shigo har ya kulle ƙofa ma ya tarar da Bilal ɗin a falo shi kaɗai dan tuni Hajjan ta shige ɗaki ta kwanta Fadila kuma dama tana gidan Anty Habiba wai ta fara gyaran jiki.

Kamar Abubakar ɗin ba zai kula shi ba dan har ya juya ko mai kuma ya tuna sai ya koma ya shiga falon yana kallon Bilal ya ce
"A nan zaka kwana ne?"
Agogon dake ɗaure a hannunsa ya duba ya buɗe ido ganin lokaci kafin ya ce masa

"Ban san lokaci ya tafi haka ba"
"Ya kamata ka tashi toh dan naji iska tana kaɗawa kamar hadari ne yake tasowa" Abubakar ya sake faɗa, sukayi shiru kafin ya ce

"Kana aikawa da yaran can abubuwan buƙata kuwa?"

Kallon rashin fahimta Bilal ɗin yayi masa dan haka ya ce
"Su Al'amin, kana aika musu da kuɗin abinci da na sauran buƙata? Sannan kuɗin makarantarsa da sauran abubuwan duk kana kulawa da su?"

"Ai ita ta matsa na saketa kaga kenan ta shirya kula da su" ya bashi amsa ba tareda ya kalle shi ba. Abubakar yayi murmushi ya ce

"Ai sabon abu bane, ko a sanda take gidan naka ma ai ita take ɗauke da nauyin kanta da na sun kaga ba zai zame mata sabo ba dan taci gaba. Wlh Yaya Bilal kayi babbar asara, samun mace tamkar Anty Halima a zamanin nan sai sa'a kuma tunda ka rabu da ita ba zaka mai da irinta ba ko mace dubu zaka aura wlh ba dai ka samu irin Halima ba
Chapter 136 · 0% Book details