← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 158

Sashe 33

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban san Bilal ya ƙware a iya sharri ba se da ya dire kwanon miyar hannun sa ya miƙe tsaye yana nuna kansa yace
"Ni kika cewa maye Halima?"
Ban san sanda na miƙe ba nima na dafe ƙirji tare da fito da idanu nace
"Yaushe? Ni nace maka maye Bilal a ina mukayi haka?"
Be amsa mun ba illah kallo na da yakeyi kamar me neman gurin da ze fi masa sauƙin hallaka ni a jiki na kafin ya juya ya shige ɗaki yana cewa nanata
"Ni kika cewa maye ko? Zaki san ni kika alaƙanta da maita Halima". Gaba ɗaya se hankali na ya dugunzuma, babu alamar cewa wasa yakeyi akan fuskar sa ko furucin sa duk ma ba wannan ba tsakani da Allah a yaushe na alaƙan ta shi da maita? Idan ma kuma nayi hakan ai ya sani wasa ne be kamata ace ya fusata ba balle ma kuma duk yanda nake wasa da koma wane akwai irin kalaman da bana taɓa kuskuren furta su.

Bin bayan sa nayi, yana kwance kan gado ya daga kansa da hannayen sa biyu yana kallon ceiling na shiga da ƙaramar sallama kamar mara gaskiya. Daga bakin gadon na tsugunna kaina a ƙasa na rasa me zance masa. In dai ba dama da wani abu a ran Bilal ba be kamata ace ɗan ƙaramin abu haka ya kawo yamutsi a cikin daren nan ba. Murya ba amo na kira sunan sa, be amsa ba na sake maimaitawa har sau uku still yayi banza da ni se kawai na kife kaina a kan gadon na fashe da kukan ƙarya, Anty Labiba tana gaya mun da yawan maza basa son kuka kuma yana daga cikin abin da yafi saurin karya lagon su yawancin maza basa iya jure ganin matar su tana kuka ko da kuwa ace na rashin gaskiya ne. Na rigada nasan ni nawa kukan bashi da tasiri a gurin Bilal gwaji kawai na sakeyi ko Allah ze saka yau hakan yayi tasiri ilai kuwa se ji nayi ya ja tsaki me ƙarfi da har se da na dakata daga dramar da nakeyi, ina kallon sa ya fice daga ɗakin da bargo a hannun sa ya barni a durƙushe ban san lokacin da kukan gaske ya ƙwace mun ba.

Wace irin rayuwa ce haka ace abinda be taka kara ya karya bane ze ringa zama na tashin hankali a gurin Bilal? Sannan wannan halin ko in kular da yake gwada mun idan yana cikin fushi ban taɓa hasashen fuskantar sa daga gurin sa ba. Baya cikin alƙawarin daya ɗaukar mun. Ya gaya mun gidan sa ze zame mun dausayi ne na farin ciki ba akasin haka ba, shikenan nan da laifi na da ba nawa ba se dai shi yayi fushi na bishi da rarrashi ni baze taɓa dubana ya fahimci tawa damuwar ya kwantar mun da hankali ba?"

Ban san tsawon lokacin dana ɗauka ina kukan ba har bacci ya kwashe ni a gurin. Mun yi dashi akan washe garin gidan mu zan tafi na wuni dan haka ko da na tashi naga be sauka daga fushin sa ba ban damu sosai ba tun da gidan zan bari naje in da zan samu farin ciki na gabatar da shagalin sallah ta cikin nutsuwa. Ni kam idin farko a gidan Habibi ya zo mun da mishkila. Ruwan shayi kawai na tun da akwai sauran sinasir muna kuma d bread. A yanda yake a 360 ɗin nan nasan idan na dafa wani abun zamu sake haurawa ne ban ma kuma ji sha'awar cin komai ɗin ba dan haka kafin ƙarfe goma na gama shiri na tsaf. Ban zaci ze ci abin karin dana ajiye masa ba se da na fito naga ya cinye harda sauran kazar dana ɗumama na aje masa da wadda beci ba jiyan da wadda na aje wa kaina, na tattare kwanukan na ɗauraye, a waya na kira shi bayan dana duba babu mashin ɗin sa, se da na masa missed calls uku be amsa ba na huɗun na shiga yayi rejecting se ga text message ya biyo baya yana tambayata menene baze iya amsa waya a in da yake ba?

Sanar masa nayi da na shirya zan tafi gida ya maido mun amsa da
"Ban yarda ba". Na nanata karan ta rubutun yafi sau uku kafin na ajiye wayar lokaci ɗaya hawaye ya cika mun ido. Idan nace zan kira Mama a waya na gaya mata na fasa zuwa nasan kukan da nake dannewa ze fi ƙarfi na dan haka na tura mata da text kawai ina ƙoƙarin kashe wayata dan karma ta kirani kuwa se ga kiran Abba dole na amsa bayan mun gaisa yake tambaya me yasa bazan zo ba? Se da ma toshe baki na dan kar kuka ya ƙwace mun kafin na sharara musu ƙaryar ciki na ne ya kama ciwo. Murya cike da alhini ya shiga tambayar me ya same ni? Munje asibiti toh? Nace masa nasha magani kawai se ya bawa Mama wayar dake nayi mata ƙorafin ciwon mara da nake yawan yi se tace mun na kwanta na huta ƙila aikin da nayi jiya ne na jijjiga jiki na idan kuma ciwon ya wuce misali to mu tafi asibi kawai nace mata irin wanda na sabayi ne kuma nasha maganin da aka bani. Suka ringa jera mun sannu, har mun kashe waya ta sake kira tace ga Amirah nan zasu zo su taya ni zama toh ko da zan buƙaci wani abu.

Sosai nayi kuka, sallah guda yayi mun wannan rashin mutunchin ya hanani zuwa gidan mu bayan duk sun saka ran zan je. Gurin sha biyu su Amirah suka zo, Mu'azzam ne ya kawo su amma be shigo ba ya wuce. Mama ta haɗo su da abinci shinkafa da tuwo se miya stew da Amirah tace yanzu Maman tayi mun ga soyayyen nama na sa da na kaji tuli harda zoɓo da kunun aya Abba kuma ya basu dubu goma a envelope su kawo mun barka da sallah. Ban san sanda na fashe da kuka ba. Ranar wunin ɗaki nayi se dai bini bini Amirah ta leƙa ta tambaye ni ko akwai abin da nake so? Da Abubakar ƙanin Bilal suka zo ma ce mata nayi kawai ta zuba musu abinci tace musu bacci nake yi. Dab da magriba Mu'azzam yazo ɗaukar su har sannan kuma banga idon Bilal ba. Bayan na rakasu na dawo na kwanta a falo sun gyara mun ko ina har abincin da zamu ci da daren ta zuba a kuloli ta ajiye sauran kuma nace su bawa almajirai abin da ze ajiyu kuma ta saka mun a fridge. Ina kwance wayata tayi ƙara, na zata Bilal ne se da na ɗaga ta naga Anty Labiba ce.

Yau ɗin har gidan ta naso naje, ina jin muryar ta bayan dana amsa wayar kawai kuka ya ƙwace mun. Tayi shiru kusan minti biyar ina mata kukan kafin tace mun
"Menene?"
Zuciya ta tana raya mun na gaya mata abin da nake ta dakon sa a zuciya ta ni kaɗai se dai ɗaya ɓangaren na gargaɗi na da kar nayi hakan. Zata mun dariya tace dama se da ta faɗa be zama lallai ma ta fahimci damuwata har ra bani mafita ba kawai zata fassara abun ne da hasashen ta na farko akan Bilal, wannan tunanin yasa na fasa faɗa mata ainihin abin da nayi niyya kawai nace mata bani da lafiya ne.

"Kuma saboda baki sa lafiya se ki ringa irin wannan kukan Halima? Baki san shi kansa kukan bashi da kyau ga me ciki ba so kike ki saka abin da yake cikin ki a damuwa shima? Bana son sakarci, ya kamata dai yanzu ace kin girma tunda nan da ɗan lokaci uwa kike shirin zama kina wa yar rashin lafiya kuka yanzu idan ranar haihuwa tazo kuma se yaya kenan?" Ta faɗa. Se na tsagaita da kukan taci gaba da cewa
"Yanzu da su Amir suka dawo yace mun baki da lafiya, toh kun je asibiti dai ko?"

"Eh mun je ba wani abu bane dama marata ce kawai take ciwo kuma nasha magani ta rage" na bata amsa, se ta ɗan yi shiru kamar bata yarda ba kafin tace
"Shikenan Allah ya ƙara lafiya. Ki ringa kula da kanki duk abin da kika san ze jigata ki kar kiyi, na ma yiwa Mama magana tuntuni ko za'a sama miki me aiki tace a bari tunda baki nema ba amma ya kamata gaskiya saboda ba laifi aikin gidan naki da ɗan yawa kuma yanzu hutu kike buƙata musamman tunda cikin yazo miki da ciwon mara".

"Aa fa yau ne kawai shima nasan saboda aikin da nayi jiya ne amma ba wani abu nake yi da yawa ba duk su shara da mopping shi yakeyi da kansa" na faɗa dan na taɓa yiwa Bilal zancen yar aiki yace baya so, yanzu idan ta kawo ta ya koreta sabuwar gaba ce zata ƙullu tsakanin su. Shiru ta sake yi kafin tace
"Shikenan, Allah y sauwaƙe ya bata lafiya me amfani" daga haka mukayi sallama. Jin an fara kiran sallah yasa na koma ɗaki nayi, se da na idar da isha'i na sake fitowa har sannan kuma Bilal be dawo ba. Ina tsaka da cin abincin dana saka kaɗan naji ana buga get. Bilal ya fita da key dan haka nasan bashi bane, nayi mamakin ganin Anty Labiba da Uncle Saleh bayan dana buɗe ƙofar, ban san sanda na rungume ta ina dariya ba. Rabon ta da gidan tun ranar da aka kawo mun gara, Uncle Saleh be shiga ba a wajen muka gaisa yace ze je ya dawo muka shiga tare da Anty. Na rasa me ma zan bata, har ga Allah naji daɗin zuwan ta over ma. Ganin ina ta kwaso ruwa da lemo na kinkimo kular abinci yasa ta dakatar dani tana cewa
Chapter 33 · 0% Book details