← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 158

Sashe 25

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*PAGE 11*
Daƙyar na koma cikin falo na zauna ina jin kaina yana saramun. Me yasa Bilal yake haka? Kullum ace abinci ne ze ringa haɗa mu rigima?
Ina nan zaune ya fito daga ɗaki yanayin shigar sa na gane nisa ze yi. Ko kallo na be yi ba ya fice sabbin hawaye suka ɓalle mu. Zuciya ta tana raya mun na barshi naga iya gudun ruwan sa amma gangar jiki na taƙi bani haɗin kai, bazan ce ga sanda na miƙe na bi bayan sa ina kiran sunan sa ba amma ko a jikin sa ya yi ficewar sa daga gidan ya bar ni a tsaye ina hawaye. Se da nayi kuka me isa ta, har na danna layin Anty Labiba zan kai mata kuka na se dai nauyi da kunya suka sa na katse kiran, Ina kallo kuma ta biyo baya amma na kasa ɗagawa.

Har aka kira sallar magriba be dawo ba, bayan na idar da sallah ina zaune wani tunani ya faɗo mun. Mu'azzam na kira, bayan mun gaisa na tambaye shi yana ina ne?
"Ina kusa da gidan ki, da zan shigo ma amma bani kaɗai bane kar nayo miki gayya kuma baki san da zuwan mu ba" ya faɗa. Se na marairaice nace
"Yawwa, dan Allah ka agaza kazo zaka taho mun da saƙo"
" Saƙon me? Na gaya miki fa ina unguwar ba wai daga gida zan fito ba" ya faɗa se nayi saurin cewa
"Ai a kanti zaka siyo mun abun, lemo ne ba wani abu ba ka siyo mun Exotic carton ɗaya idan kazo se na baka kuɗin".

"Ke yanzu duk uban lemukan da aka kawo miki da gara har kun shanye shi ko mutane kika yi ta rabarwa? To se dai ki aiki mijin ki babu wani lemo da zan kawo miki" ya faɗa yana niyyar katse kiran na san halin sa tunda ya fara hakan da wuya ze kawo mun ɗin amma idan yaƙi ban san kuma ta hanyar da zan bi mu shirya da Bilal a gajeran lokaci ba dan haka nace

"Haba ɗan uwana, ina da lemo kala kala shi ɗin ne dai ya ƙare kuma shi nake iya sha yanzu". Shiru yayi har nayi zaton ma ya kashe wayar kafin naji yace
"Shikenan zan kawo miki wane flavor?"

Jin na samu mafita hankali na ya kwanta se na tashi na shiga tattare kayan abincin dana aje masa na maida kitchen tun da baze ci ba. Ba'a ɗauki minti ashirin ba Mu'azzam yazo, carton biyu ya siyo mun be ko zauna ba muka gaisa daga tsaye yace ana jiransa ne. Ɗaki na tafi na ɗakko masa kuɗin amma yaƙi karɓa.
"Lallai ƙani na an fara hankali" na tsokane shi, se yayi murmushi kawai yana kallon fuska ta dana lura tunda ya zo yake kallo na yace
"Me ya same ki naga idon ki sunyi jaa kuma sun kumbura fuskar ki ma haka?" Se naji kamar ya fama mun abin da yake damu na nan da nan ido na ya kawo ƙwalla se dai ban bari sun taru ba na ƙaƙalo murmushi nace

"Babu komai, yau na tashi duk bana jin daɗi ne shiyasa".
"Se ki gaya masa ya siyo miki maganin malaria tun da kina barin ƙofa a buɗe dama dole sauro zasu shigo miki" ya faɗa yana fita. Na bi bayansa, se da muka je get ya sake kallo na yace
"Halima fuskar ki ta nuna kina da damuwa" kawai jin ɗumin hawaye nayi akan fuska ta ba tare da nasan saukar su ba. Ya gyara tsayuwa yana kallo na yace

"Duk da ke kika siyawa kanki amma ba zan baki shawarar ki shanye baƙin ciki a son kar ayi miki dariya ba. Idan kika ji ba zaki iya ba ki tafi tun lokaci be ƙure miki ba" daga haka ya fice ya barni tsaye a gurin ina kuka mara sauti. Se da gabana ya faɗi da naga kiran Mama bayan tafiyar Mu'azzam babu jimawa. Tunanin ko ya faɗa mata wani abu na shiga yi, to amma me ze ce mata?
Se da ta mun kira biyu kafin na amsa a sanyaye muka gaisa ta tambaye ni jiki na ce da sauƙi.
"Karki kuskura ki tasa kayan zaƙi kice zaki ringa sha, Mu'azzam ya gaya mun kin ce ya siyo miki lemo to ki tattara su ki aje in ba haka ba wuya zaki kirawa kanki tun yanzu" ta faɗa. Se naji dariya ta kamani, wato in da lissafin ta ya tafi kenan ciki ne dani amma dan a rabu lafiya se kawai na bita da toh. Bamu jima ba mukayi sallama tana sake jaddadamun na kiyayi kayan zaƙi ni dai da toh kawai na ringa bin ta. Maganar da mukayi da Mama tasa na danu sauƙi cikin zuciyata se kawai nayi shafa'i da wutri nayi kwanciya ta.

Ban sanda Bilal ya dawo gidan ba na dai farka cikin dare na ganshi a baya na. Da safe tamkar bamu samu saɓani jiya ba lafiya lau ya tashi yana jana kamar yanda muka saba ni ce ma nake ɗararewa. Ban yi gigin taɓa masa dankali ba na ɗumama sauran abincin da be ci ba jiya muka karya dashi, da ze fita yace mun na shirya idan ya dawo zamu fita wannan tasa na ware nima. Gidajen yayyen sa mata muka zagaya waɗan da suke ciki ɗaya da wanda suka haɗa uba. Har unguwar su Anty Labiba muka je amma ƙememe yaƙi yarda mu shiga wai takanas zamu shiryo muje ba ratse ba. Dake dai mun shirya ya sakko daga fushin ban matsala ba kar ya sake birkice mun tun da dai yayi alƙawarin zamu je da weekend na wuni shikenan.

Haka rayuwa taci gaba da miƙawa a lissafi aure na da Bilal yana cikin wata na biyar kenan a kuma cikin wannan lokacin nayi karatu game da zamantakewa ta dashi ta rannoni biyu. A bangare ɗaya na tabbatar da cewa Bilal yana so na domin irin kulawa da tattalin da yake bani na san cewa ba duka haka maza suke ba. Yana da sauƙin kai sosai a halayya sannan ya ɗauke ni matsayin ƙawa be hakan ne yake ƙarawa zamanmu armashi.

Idan har yana gida tare muke duka ayyukan gida. Kasancewar sa me tsafta sam baya shiri da ƙazanta be kuma so jikin sa ba, da sassafe kafin ya fita aiki ze share mun tsakar gida ya wanke haka da falo na nasa ze share yayi mopping ni kuma naji da gyaran ɗaku na da girki idan ya wuni a gida kuwa hatta sharar ɗakunan shi zeyi ya gyara ko ina tsaf ya kunna turare dan idan yayi gyaran nafi ganin gurin yayi yanda nake so saboda babu algus, kullum ze yi shara tofa se ya ɗaga kujeru ya share ƙasan su haka duk wani abu dake ajiye se ya ɗaga ya goge har mamaki nake yi yanda sam abin be dame shi ba kamar ma hakan na samar masa da jin daɗi dan cike da walwala yake ayyukansa wankin toilet dama ko na wanke na ɗakin sa cewa ya keyi be fita ba ze zauna ya sake wankewa tas yanda yake so haka wankin kaya har undies yake wanke mun wani lokacin muyi tare ina masa ɗauraya wani lokacin yace ban iya ba na barshi se dai na zauna daga gefe ina masa hira waɗannan halayyar tasa take sake ƙara mun son sa da ƙaunar sa a zuciya nake kuma ganin ɗaya ɓangaren na halayensa da bana jin daɗin su a matsayin ajizanci irin na ɗan adam domin kuwa babu wani mutum da yake cikakke dole ka kasance da halayen abin so da kuma wanda ba kowa yake so ba.

Daga cikin abin da ke yawan janyo saɓani tsakani na Bilal shine ƙorafi. Ko dan yana yawan zama a kusa da ni ne tun da idan ya fita aiki ya dawo idan ba sallah ba ba in da yake zuwa in kuma ranakun hutu ne yana gida, ba ƙaramin abu bane yake fitar dashi ko ya fita ma baya jimawa ze dawo dan haka ko yaushe muna tare dan haka duk abinda zanyi akan idon sa ne kuskure kaɗan kuma zan yi yayi ta mita yana ƙorafi kenan. Abin da be kai ya kawo ba se ya zama na magana a gurin sa.

Sannan na lura Bilal yana da son ya zama duk wani abu da zanyi ya zama da sanin sa. Sannan mutum ne me tattali da son abin sa. Har idan ina so na ga fushin sa to fa na taɓa abun sa ba tare da izinin sa ba tun da kuma na fahimci hakan nake kiyayewa shikenan nayi maganin fitinarsa. A watanni biyar ɗin nan bani da wata matsala idan aka cire rashin fita da Bilal baya bari na a sanda naso se kuma rashin walwala ta kuɗi a hannu na. Ina samun kuɗi dan kusan duk sanda zanje gida Abba se ya bani ko ya tura mun a account a cewar sa kar na ringa damun miji na da bani bani, Saboda gudun fitinar Bilal ko ƙorafi akan kayan sa bana saurar komai daga gare shi duk abin da nake so cikin kuɗi na nakeyi har shima nayi masa na kuma yiwa yan uwansa.

Abin sa na sake lura dashi yana jin daɗin shi na hidimta masa amma baya so nayi wa wani dan har idan wani ya zo mana nayi masa kyauta a gabansa ko beyi magana ba a fuskar sa ina karantar rashin jin daɗi abun na damuna da na gaji nayi masa magana akan hakan se yace wai abin da nakeyi ze janyo masa raini a gurin masu zuwa gidan mu shi megida ya kamata ace idan ma kyautar ce yayi ba wai ni ba, saboda a zauna lafiya se ya zama idan yana nan mukayi baƙi idan kuɗi ne zan bashi nace ya basu idan kuma wani abun amfani ne zance gashi in ji shi shikenan na samu lafiya da wannan ma.
Chapter 25 · 0% Book details