Sashe 8
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mu'azzam ya zabga tsaki yace
"Se kace wadda zata auri wani Bilal ɗin farko, rabon shan wuya yasa kika kafe yarinya amma dai Allah ya bada sa'a". Kan na amsa shi na jiyo Abba na cewa
"Kai Ibrahim wace irin magana ce wannan?" Sena fake shi na zabga masa mari a ƙeya kafin na kwasa da gudu nayi ɗakin Mama ina cewa
"Ɗan baƙin ciki se dai ya haɗiyi zuciya ya mutu". Bama ga muciji da Mu'azzam kasancewar mu sakwanni ga kuma banbancin hallaya. Yana da zafi ji yake ma kamar shine sama dani ko dan ya kere ni a girma ni kuma gani da son girma ina so yanda yake ƙanina dole ya bini kamar yanda nake juya Imam da Amirah na uku data huɗun mu.
Mama na zaune tana lazumi na faɗa jikinta ina ci gaba da ihun murna, se da ta ture ni kafin tace
"Mene ne haka Halima?"
"Mama ki tayani murna jibi Bilal ze turo a saka mana rana" seta saki baki kawai tana kallona ni da kaina na fahimci wauta da rashin kunyar da nayi se kuma na miƙe na fice daga ɗakin da sauri ina dariya ina jin ta tana cewa
"Allah ya shirye ki Halimatu Allah ya shiga lamuranki".
Seda nayi rawa nayi juyi akan gado kafin na dire na ɗauki wayata, tun da na kashe ta ban sake bi ta kanta ba. Na kunna kafin ta gama booting ta kawo ji na ringayi kamar na damfarata da ƙasa ko zata fi sauri ina danna lambobin Bilal naji sallamar Hansa'u a falo se na fita da gudu, Mama da suke gaisawa ta kalle ni tace
"Wai wace kalar rashin nutsuwa kika samu kuma Halima?"
Baki na kamar gonar auduga na rungume Hansa'u Mama ta girgiza kai kawai ta shige kitchen ta barmu.
"Albishirinki ƙawata" na faɗa ta amsa da goro, nayi fari da ido kafin na shaida mata jibi za a yi sa rana ta da Bilal. Tayi jumm da farko kafin kuma ta saki murmushin da na tabbatar be kai har ƙasan ranta ba tace
"Na tayaki murna ƙawata, Allah ya tabbatar da alkhairi ya nuna mana lokaci"
"Amin Hansy, amin" na faɗa ina sake laluben lambar Bilal. Muryar Abba da Baba Salahu da na jiyo suna fitowa daga can falon tasa na miƙe ina ce mata
"Muje ɗaki". Ta ringa kallo na kawai na kira Bilal, se da wayar ta kasu katsewa kafin ya amsa murya ba amo sosai.
"Ba ni da lafiya Halims, kewarki zata hallaka ni" ya faɗa kamar irin wanda yake gargadar mutuwa bayan dana tambaye shi me ya faru naji muryarsa a ƙasa. Take hankali na ya tashi, na miƙe daga zaunen da nake ina cewa
"Me ya same ka? Tun yaushe? Shine baka gaya mun ba?"
"Ta ina zan same ki bayan kin kashe wayarki kin yi blocking ɗi na a wayar Mama sannan zuwana uku duk baki bari na ganki ba?, ni dai ki yafe mun kawai idan na mutu dan yan da nake ji kamar bazan tashi ba" ya sake faɗa yana sakin numfashi ban san lokacin dana fashe da kuka ina cewa
"Haba dan Allah kar ka mun haka, kana ina yanzu? Kaje asibiti ko kana gida?"
"Ina gida Halims bazan je asibiti ba tun da na fahimci rayuwa ta ki ke nema gara kawai na sauƙaƙa miki in bar miki duniyar se ki fi jin daɗi kamar yanda kika ce na fita daga rayuwar ki". Ban tsaya sake jin abin da ze faɗa ba na kashe wayar na figi jaka ta dake kan gado nayi ƙofa, Hansa'u ta biyo ni tana tambaya ta lafiya amma ban tsaya ba na nufi get se kawai ta biyo ni. Se da muka hau adaidaita kafin cikin kukan da nake na gaya mata Bilal ne bashi da lafiya. Bata iya riƙe kanta ba ta zabga tsaki tace
"Bilal bashi da lafiya Halima shine kika riki ce haka kina kuka?"
"Ban gane na riki ce ba? In ce miki mijin da zan aura bashi da lafiya har ki tambayi ba a sin rikicewa ta ko kuka?" Na hayayyaƙo mata. Se ta sake yin tsaki tace
"Wlh ƙarya yake, yanzun nan daga gidansu Maryam Abdullahi nake har gaisawa mukayi yana ƙofar gidansu suna hira da Abokanan sa".
Nayi mata banza ina ci gaba da share hawaye tun da ba son sa take ba ai dama komai ma daya shafe shi zata ce ƙarya ne. Ban ko tsaya karɓar canjin adaidaitan ba na wuce ƙofar ɗakin sa na shiga bubbugawa. Abubakar ƙaninsa ya fito daga cikin gida gani na yasa ya tsaya.
"Yaya Bilal ɗin ne bashi da lafiya?" Ya tambayeni cikin mamaki bayan dana tambaye shi ina Bilal. Se na ciro wayata na shiga kiran layin sa, Nasiru ne ya amsa yace suna asibiti jikin nasa ne ya riki ce"
"Subhanallahi, babu jimawa fa Yaya Nasirun ya kira shi duk muna tare a cikin gida bari na shiga na gayawa Hajja se nazo muje asibitin" Abubakar ya faɗa yana komawa cikin gida.
Nasan kara kawai Hansa'u ta mun ta bini asibitin, na ringa rusa kuka ganin Bilal kwance da robar ƙarin ruwa a ido na se naga ya rame yayi baƙi Abubakar da Hajjansu nata jimamin to me ya same shi tun da su dai lafiya lau ya fita daga gida se Nasiru ne yace musu dama kwana biyu yana masa ƙorafin ciwon kai da ƙirji shine suna zaune suna hira wai kawai suma. A asibitin na wuni sur har sallar isha'i se da Abba suka zo tare da su Mu'azzam kafin na bishi muka tafi gida Hansa'u dama ko minti goma bata yi ba da mukaje tace mun zata wuce. A hanya Abba yake ce mun wai typhoid da malaria ne suka kwantar dashi lokaci ɗaya kamar yanda likitan daya tambaya ya faɗa masa. Nayi shiru a raina na raya ƙila basa so a faɗi ainihin abinda yake damunsa ne dan ni likitan ce mun yayi zuciyar sa ce ta kumbura, wai dama yana da matsalar zuciya amma duk tsayin zaman mu shine ya ɓoye bai taɓa gaya mun.
Na share hawayen daya gangaro mun ta gefen ido na sanadin tunanin wai Bilal na da matsalar zuciya da nayi. In da na sani ina zan masa boren da nayi waccen ranar har in share sati ba tare da na amsa wayar sa ko na bari mun haɗu ba. Ko kallon in da nake Mama bata yi ba da muka koma gidan, ban iya bacci da kyau ba cikin dare duk motsi na hankali na yana kan Bilal ga wayarsa dama tun ina can Nasiru ya kashe a dafe na kai safiya tun farar asuba kuwa na shiga kitchen na fara haɗa masa kunun gyaɗa da alala na haɗa masa da farfesun kayan ciki. Saboda kar Mama tayi faɗa na duka gida nayi kan bakwai na gama na shirya wanda zan kai masa na ware na gida sannan na wuce wanka a gurguje. Ina fitowa naji Mama na faɗa
"Saboda jiya ban ce mata komai ba shine yau zata ɗibar mun kaya tayi girki ba tare da ta sanar mun ba to babu in da za'a kai abuncin nan" na jiyo tana faɗa. Nayi saurin zura doguwar riga ba tare da na shafa komai a jiki na ba na saka hijabi na fita. Daga ne sa na gaishe ta ta galla mun harara tana cewa
"Wato bakya jin magana ko Halima?"
"Yanzu Amina ba zan ce magana ta wuce ki barta haka ba se kin sake tadawa?" Abba ya katse ta, se ta juya kansa tace
"Dama ai kai baka ganin rashin dacewar duk abinda takeyi a gidan nan. Yanzu mutunchi ne ace ta tafi ta tare a asibiti tun hantsi ina ga da baku je ba ma a can tayi niyyar ta kwana ko? Sannan yanzu kaga uban abincin da tayi zata kai musu kan ta aka fara soyayya ko kuwa da zata ringa abu kamar mara cikakken saiti. Badai namiji bane, ka bishi a sannu ma ya ka ƙare balle ka nuna masa ba zaka rayu idan babu shi ba"
"Ni da kika nuna mun ba zaki rayu idan babu ni ba nayi miki butulci ne Amina da har zaki fara kafa hujja da halin Maza?" Abba ya faɗa, tuni na sulale nayi kitchen jin maganar na neman canza salo. Na bi ta ƙofar baya na fice ina zagayowa muka ci karo da Mama ta kuwa falla mun marin da da wayo na bazan iya tuna sanda ta dake ni ba.
"Har idan na isa dake Halima umarni nake miki ba shawara ba ki fita daga sabgar yaron nan, ban yarda ba kuma ban amince da cigaban tarayyarki dashi ba" Mama ta faɗa cikin fushin da ban san tana da shi ba. Hankalina ya tashi matuƙa, na aje kwandon hannuna na fashe da kuka ina cewa
"Mama me yasa zaki ce haka me Bilal yayi miki?"
"Ba abin da ya mun amma ina kallo bazan bari ki tura kanki a rami ba. In sha Allahu idan ma da ƙulumboto ya nemi soyayyar ki zan ci gaba da kaiwa Allah kuka na ya warware komai ya raba ki dashi. Na gaji, wannan wane irin bala'i ne? Bilal se kace na billahillazi bakya ji bakya gani akansa? To ba dani ba ko kina so ko bakya so dole ki barshi tun da ba hauka akeyi ba".
Kuka na fasa harda kururuwa Abba ya fito cikin ɓacin rai yace
"Baki ji ba kenan?"
Ta wuce ciki ba tare da ta amsa masa ba tana jaddada mun wallahi na fita se na sha mamakinta yau.
"Dan Allah Abba ka bata haƙuri na faɗa ina kama ƙafarsa, seya ɗago ni yana cewa
"Ya isa, ki koma ciki tunda tace karki fita bari na taso Ibrahim se yaje ya kai musu abincin". Yanda kasan wadda aka wa mutuwa haka na shiga ɗaki na ringa kuka akan hanani komawa dubo masoyi na da akayi. Wuni sur ban fito daga ɗaki ba ko abinci ban iya kaiwa baki na ba seda mukayi waya da Bilal ya gaya mun an sallame shi se lokacin na tsagaitawa kaina har na fita na nemi shayi na sha.