← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 158

Sashe 130

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Suby ne Zahra kaɗai sukayi saura sai da suka tayata suka gyara gidan tsaf kafin suma suka mata sallama suka wuce lokacin Bilal ya fito zai tafi sallar la'asar suka gaisa har sannan dai fuska ba yabo ba fallasa ya ce mata zai je gidan Hajja daga can wannan ya sa su Suby suka fasa tafiya suka zauna ƙulla yanda za'ayi kar bomb ya tashi.

"Amma fa ko wannw Malami ya miki aiki wlh ya iya Zully bai ci miki kuɗi a banza ba" Zahra ta faɗa. Zulaiha tayi murmushi ta ce
"Kin san dai bana harkar Malamai"
"Haba Hajiya, a wannan karon dai ƙarya kike wlh rufe masa baki kikayi" Zahran ta sake faɗa Zulaiha ta rantse tana cewa

"Har Umma haka take cewa wai da asiri na samu Bilal kuma wlh tallahi ke ni ko a sallah bana addu'a a akansa kawai ikon Allah ne".

BILAL
Yana dab da gidan Hajja wayarsa da sai a lokacin ya kunnata tun daren jiya ta shiga ringing, ya cirota ya duba ganin Hafiz ke kira ya saka ya gangare gefen hanya ya ɗaga dan dama so yakeyi idan ya fito daga gidan Hajjan ya wuce gurinsa su ƙarasa zancen shaguna da suka fara.

Sai da Hafiz ɗin ya zolaye shi ya tambayi amarya kafin ya ce masa
"Dama maganar takardun gurin can ne, na bawa Barrister ya duba ya ce ba original bane, idan original ɗin suna kusa ka kai masa please sai ka turawa da Turad account ɗin da za'a saka kuɗin idan kuma a wanda yake da shi ne sai ka kirashi a waya ka gaya masa kawai".

Mamaki ne ya rufe shi jin abinda Hafiz ɗin ya faɗa, takardu ba Original bane kuma kamar yaya? Cikin duburburcewa ya ce

"Kamar yaya ba Original bane? Anya ya duba su sosai kuwa?"

"Ka dai san in dai aiki ne Barrister Umar ya san aikinsa, so tunda ya ce papers ɗin nan ba original bane na yarda, amma idan kana da ja akan hakan kaje ka same shi idan ya so sai kuje tare gurin waɗanda ka siya idan ma kuskurensu ne duk za'a gane" Hafiz ya sake faɗa daga nan kuma ya masa sallama.

Ajiye wayar Bilal yayi y dafe stirring zufar tashin hankali na keto masa. Ya ma za'ayi ace takardun shago ba original bane bayan da shi akayi komai akayi sealing deal, shi ya biya kuɗin kuma a hannunsa ya karɓe su ko Jalilar gani kawai tayi amma daga na gidan har waɗannan ɗin a hannunsa suke bata taɓa riƙe su ba.

Wayar ya ɗauka ya shiga kiran Kamalu wanda ya musu hanyar shagunan cikin rashin sa'a aka ce wayarsa a kashe. Fasa zuwa gidan Hajjan da yayi niyya yayi ya juya ya tafi gurin Barrister Umar, yayi shiru yana kallon takardun daya baje masa, nasa da wasu yana nuna masa banbancin original takardu da kuma nasa da ya ce forging ɗin su akayi.

"Shiyasa ake cewa idan zakuyi cinikayya ku ringa saka expert da suka san kan abun amma saboda ɗan kuɗin da zaku biya sai ku gwammace kuyi daga ku sai dillalai bayan dillalan nan wasu marasa tsoron Allahn property ɗaya sai su siyarwa sama da mutum biyar sai dai wanda yafi ƙarfi ƙarshe yayi nasara akai. Yanzu dai gaskiya waɗannan takardun naka da su da takardar tsire basu da banbanci tun wuri kuma kayi abinda ya kamata kafin su sake siyarwa da wani su bashi takaddun gaske" Barrister Umar ya faɗa.

Da wannan sabuwar damuwar Bilal ya koma gida dan gaba ɗaya ya rasa mai ya kamata yayi gashi wayar Kamalu a kashe ya kuma je har inda yake zama an ce baya nan wai yayi tafiya kuma basu san lokacin da zai dawo ba.

Gida ya wuce ya birkice takardunsa ya fito da na gidan daya siya bayan ya siyar da asalin gidan Jalilah. Zama yayi ya duba takaddun tsaf yana tuna abubuwan da Barrister ya nuna masa da suke nuna banbancin original da fake takaddun, ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi bayan daya tabbatar na hannun nasa original ne. Tunani ya shiga yi to na gidan daya siyar fa? Suma fake ɗin aka basu ko kuwa na gaske ne? Sai kuma ya taɓe baki a fili ya ce

"Oho koma wannene can su ta shafa tunda ni dai na rabu dasu" wannan ya ɗan samar masa da nutsuwa har ya shiga gurin Zulaiha da yana shigowa ta taho tana masa oyoyo amma ko kallonta bai yi ba ya wuce ɗakinsa bata yi zuciya ba kuma ta bishi ta ajiye masa ruwa da lemo mai sanyi dama ya tarar da kwanukan abinci amma ba ta su yake ba sai da nutsuwar sa ta dawo kafin ma ya tuna da yana jin yunwa.

Washe gari kuwa kamar yanda ya ce da safe ya ce ta shirya suje Asibiti dan daren jiya duk yanda ta so ta kama kanta yanda Suby ta ce kasawa tayi amma da yake batayi amfani da turaren kan tace ba shiyasa har ya samu damar tureta wai ya gaji bacci yake so yayi. Abun ya mata ciwo ƙwarai amma ta danne tara shi zatayi zata rama komai sala sala da zarar komai ya sake hawar mata saiti. Tayi dana sanin ƙin jin ta Suby da tun farko tace tayi ɗinkin ciki da wajen a ganinta iya gyara da kayan matsin da tayi amfani dasu sun isa amma gashi an samu akasi.

Marairaicewa tayi ta tsarashi akan idan sukaje Asibiti ai tonon silili zai yi mata. Ta ce zata kira Binta wacce ta ce masa Yayar Suby ce tazo gida kawai ta mata amma ya ce Aa, daga ƙarshe dai sukaje Asibitin da Bintan take aiki dama kuma tun jiya sun sanar mata dan haka dama a shirye take ko ta kirata taje gidan ku suje Asibitin su sameta tayi mata ɗinkin tace mata

"Wannan uban buɗewa ke kuwa Zully kamar wacce ta haifi yaya goma? Gaskiya kinyi ganganci ki kuma godewa Allah dan mutumin nan yana sonki in da wani tun jiyan sai dai ki ƙarasa daren a gidanku wlh".

Manage this please bana jin daɗi wallahi 😭😭
*KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 54*

Jinyar stitches ɗin Zulaiha ta saka Bilal baya fita ko ina idan ba masallaci ba, duk ayyukan gidan shi yakeyi, sannan ya kula da ita a ɗan taƙin lokacin kuma ya ɗan fara samun nutsuwa daga tsoron sababbin halayen da ya ringa gani a gurinta tun bayan da aka ɗaura musu aure. Ranar data kwana uku ƙanwar Ummansu Anty Habi taje gidan ta kai mata gamje gamjen magunguna da ta ce na Aljanun da suke shafarta ne. Shi ya ringa jigilar dafa mata na wanka safe yamma kuma ya hura mata coal tayi turare, maganin na sati ɗaya ne ranar data cika satin tana yi kuwa Aljanun suka tashi.

Lokacin ya fita siyo kayan miya ya dawo ya tarar da ita su Suby sun daddanneta tana wasu abubuwa suka ce masa wai a haka suka tarar da ita suma. Dukda dai yayi mamakin ta inda suka shiga gidan tunda ya rufe daya fita ita kuma sun ce sun sameta ta hau iskoki to waya buɗe musu ƙofar?

Haka ya fita can masallaci ya samo wanda zaiyi mata ruƙiyya, suka ringa kafa masa Sharuɗan kar a ringa ɓata mata rai, kar ayi mata faɗa da sauransu in ba haka ba zasu dawo daga haka dai suka fice sai kuma suka riƙe mata ƙafa, sati biyu taci tana jinya kafin ta ware gaba ɗaya suka durfafi sabuwar rayuwar amarci tunda ɗinki ma ya warke, duk yanda take ƙoƙarin dannewa kar tayi abinda zai sake jefa zargin wani abu a zuciyar Bilal ɗin ta kasa.

Ranar da suka sake gamuwa dukda shi ya fara nuna buƙatar abun amma tun kafin ayi nisa taga ya canza, karsashin daya fara da shi ya sakeshi sai ƙananan tsaki da ya ringa saki, bata damu ba ta cigaba da shafashi a ƙoƙarin mayar dashi kan network amma sai kawai ya tureta lokacin da wayar sa tayi ƙara. Abun ya mata ciwo matuƙa, tana sauraron wayar da yakeyi data gane da Hajja ne kuma masifa take masa dan sai bata haƙuri yakeyi kafin ya kashe bayan ya ce mata gashi nan zai zo gidan yanzu da yake da yamma ne.

Tayi ƙwafa ta bishi da harara sanda ya shiga banɗaki, sai kuma ta tashi da sauri ta ɗakko Humrar kiranyenta ta shafa sannan ta ɗebi maƙale mata a hannunta ta koma ta zauna tana murmushin mugunta, Tunda ba zaiyi dan Allah ba toh kuwa zai yi dan dole.

Bilal kuwa daya shiga banɗakin sakin ruwa yayi akansa dukda garin da sanyi sanyi amma bai damu ba, duk da ya san gaskiyar abinda ya sameta amma kuma zuciyarsa ta kasa karɓar abun har yanzu. Yana son Zulaiha tamkar rai, amma da zarar ya tuna cewar bai sameta a Mace ba sai yaji duniya ta masa zafi, duk sanda buƙatuwar ta ta motsa masa kuma da zarar ya tuna abun sai ya ji komai ya mutu kamar dai yanzun a matse yake ya kuma yi ƙoƙari ya kawar da tunanin amma suna farawa abun ya zo masa take yaji komai ya mutu duk yanda ya so daya daure ko dan ganin kamar itama tana so ɗin amma ya kasa.
Chapter 130 · 0% Book details