← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 158

Sashe 60

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gurin da ya siya ya yanka aka feɗe masa kamar yan da Bilal ɗin ya ce ayi sannan ya wuce ya kai can gidan ya na komawa gida marin sa ne kawai Hajja ba ta yi ba dan a yanda ta ce ta ɗauka yana da hankali idan ya siyo zai yi tunanin ya fara kaiwa gidan ta ba wai ya wuce ya kaiwa Halima ba. Ta ringa sababi, se kace wacce aka kai musu garke guda hatta da yayan ta sai da abin ya ba su haushi ga mutane duk suna zaune suna jin ta take wannan abun. Suna tsaka da sabgogin su Fainusa ta je ta ke basu labarin yanzu aka kira ta ana can ana bidiri a gidan Bilal, kuma wai duk se ransu ya ɓaci akan me ba'a gaya musu Halima za ta yi taro ba, har Bilal ɗin Hajja ta kira ya ce shi bai san zata yi ba dan be bata ko sisi ba se dai idan yan gidan su ne suka shirya abun su, haka suka zari jiki suka tafi har Hajjan da ta ce zata bisu suka hana ta ta ringa jaddada musu akan duk abin da aka yi su taho mata da shi se gasu yanda suka je haka suka dawo hannu na dukan cinye se ma asarar kuɗin mota da suka yi dan dai ko ruwa ba'a basu ba a yanda suka ce. Suka ringa zagin Halima da yan uwan ta suna wassafawa Hajja irin liyafar da suka tarar ana yi tun daga kwanukan almajiran da suke ƙofar gidan zaka san ana harkar girma a ciki amma tsabar an raina su ba'a kuma daraja su ba haka nan aka bar su kamar wasu almajirai babu wanda ya bi ta kan su suka gaji da zama suka taho.
Saboda yan da abin ya harzuƙa Hajja bata iya cewa komai ba, ta ringa kiran layin Bilal wayar na ringing amma yaƙi ya amsa wannan ya sake ɓata mata rai, duk yan da aka yi da sanin sa shi ya sa ya zagaye ya sa aka kai musu Rago ba tareda ya yi shawara da ita ba.

WASHE GARI
Tun da na yi wankan safe na ci abinci na sake komawa bacci ban farka ba se azahar lokacin har Baba Jummai ta gama soya naman tas ta gyara gidan, ban yi mamakin ganin babu wanda ya zo taya ta suyar naman ba. Se da na sake watsa ruwa sannan na fito, tambayar ta na yi ko Bilal ya shigo ina bacci ta ce be fito ba ba ta ji motsin sa ba. Abinci na fara haɗa masa, sauran sinasir da waina na ɗumama na ɗibi nawa na haɗa komai a try na faki idon Baba Jummai na tafi ɗakin. Sallah na tarar ya na yi, bayan ya idar ya kalle ni da murmushi ya ce
"Kin ta shi kenan?"
Murmushin na mayar masa na ce
"Ashe ka leƙa na tambayi Baba ta ce bata ji motsin ka ba"
"Sanda na shiga tana can tana soya nama, da kamar na yi mata magana na ga ta goya Al'amin ga hayaƙi ga kuma zafin wuta kar su dame shi". Na zare ido ina dariya na ce
"Lallai, ka ce ka so ka siya mana magana ta ce ka mata rashin kunya. Ka san mitar Baba kuwa? Ɗazu fa daga ta masa wanka ta ajiye shi taje zubar da ruwan naga towel ɗin ya buɗe ga farka a kunne na gyara masa ta na zuwa ta fara mun taratsi wai me na ke dubawa a jikin sa kar na mata sharri na ce ta masa wani abun" muka yi dariya tare kafin ya ce

"Amma tana da kirki sosai ga aiki, na lura sam bata son ƙazanta itama ko ina fes fes ɗakin ku yana ƙamshi kamar ba na masu jego ba gaki kema ta na kula mun da ke sosai" ya faɗa ya na jana jikin sa. Ban musa ba na je, yana shafa fuska ta ya ce
"Jegon nan ya karɓe ki My Halims, wani kyau kullum kike ƙarawa haƙuri na fa ya fara ƙarewa". Zabura na yi na bar jikin sa da sauri ya fashe da dariya kafin ya ja try ɗin gaban sa ya buɗe ya na cewa
"Kamar kin san yunwa na ke ji sosai, ɗan ɗebo mun naman nan na taɓa. Idan kuma akwai sauran peppered chicken ɗin jiya ki kawo mun". Zuwa na yi na ɗebo masa naman na haɗo da kazar da ya ce na ji daɗi da na tarar Baba Jummai a garin lallaɓa Al'amin ta bi shi sun yi baccin tare se na ɗauki abinci na na wuce da shi muka ci tare muna hira kamar lokacin ya dawwama.

"Akwai tafiya da zan yi, zamu je wani aiki Abuja daga office. Tun shekaran jiya waɗan da zamu tafi tare suka yi gaba na bari ne dama se an yi suna nima jiki na ya sake warwarewa kafin na bi bayan su cikin kuɗin aikin da aka bamu ne ma na tura miki wani abu daga ciki jiya" Bilal ya faɗa bayan da muka gama cin abinci,
"Toh, yaushe kenan kuma zaka tafi?" Na tambaye shi. Ya ɗan ɓata fuska ya ce
"Gobe nake tunani dan suna ta mun waya akan na taho ni suke jira mu fara aikin".
"Amma fa har yanzu jikin ka da saura, na fa lura da kana sallah ƙafar ka daƙyar ka ke lanƙwasata a haka kuma zaka tafi wani aiki ba zasu canza ka da wani ba?" Na faɗa cikin marairaicewa. Se ya miƙe ƙafar yana cewa

"No na samu sauƙi fa, rashin yawan motsa jikin ne ma ya sa har yanzu nake ɗan jin ciwo amma babu wata damuwa zan iya. Kuma ban da abin ki bayan har an bani kuɗi na kashe se na ce kuma ba zani ba kenan zan mayar musu da kuɗin su".

"Kuma aikin na menene?"
"Bari na zo na je gidan Hajja, naga ta kira ni tun jiya ashe ban lura ba se ɗazu tukunna" ya faɗa ba tare da ya bani amsar tambayar da na masa ba. Tattare kwanukan na shiga yi ina cewa
"Bari to na yiwa Baba magana ta raba naman se ka tafi musu da nasu kawai" na fice daga ɗakin. Ina shiga kitchen na jiyo ana buga get, shi ya fita ya buɗe, gaba na ya faɗi jin muryar Hajja ta na cewa
"Bacci kuke ko me da za'a yi ta bugu ba zaku buɗe ba". Sauri na yi na kashe famfo na bar ɗauraye kwanukan da na yi niyya da gudu gudu na wuce ɗaki na na shige banɗaki.

Kamar na fasa kuka sanda ya zo ya na ƙwanƙwasawa wai na fito ga su Hajja sun zo, se da na kwashi kusan minti biyar kafin na fita falon kaina a ƙasa ba tare da na bari mun haɗa ido ba na samu gefe can na zauna na shiga gaishe su. Bata amsa ba ta fara zazzage mun asalin abin da ya kawo ta wato bin ba'asin wulaƙanta yayanta da yan uwanta da aka yi jiya.
"Har su zo miki taro a hana su abinci, ban da tsiya me akai aka yi abinci da har kuke rowar sa? Ko da yake dama shi taka hayen arziƙi in be nuna halin sa ba ta ya za'a gane shi? Duk wata fuffukar da kuke yi kallon ku kawai muke yi wlh har yaushe Aminun ya zama wata tsiya da har kuke ƙafafa, ai wanda bai san asalin ungulu ba ne za'a ce masa daga masar take ya yarda. Ke ba dan mutuwa me tonin asiri ba har Aminu za'a saka shi a jerin masu arziƙi ne balle ya haife ki kamar Bilal ya kalle ki ya aura ai ƙaryar ki" cewar Hajja.

Na rasa dalilin da ya saka a koda yaushe take ƙoƙarin cin mutunchin iyaye na. Idan ma laifi na mata me yasa ba zata zageni ni kaɗai ba dole se ta haɗo da iyaye na da basu mata komai ba ta zage su ta yi musu cin mutunchi? A karo na biyu Bilal na zaune akan idon sa da kunnuwan sa Hajja ta ke aibata ni da iyaye na Lanti da suka zo tare tana taya ta amma be iya ce musu komai ba.

Baba Jummai ta fito daga ɗaki, na tabbata kuma hayaniyar su Hajjan ce ta tashe ta daga bacci tayi mici mici da ido tana kallon ta ta ce
"Amma dai ko wacece ke baki da ɗa'a ba kuma ki da mutunchi. Ki shigo har ɗakin yarinya ki sakata a gaba kina zagin iyayen ta da basu ji ba basu gani ba"

"Ni a uwar Bilal" Hajja ta bata amsa, hakan be saka Baba Jumman ta tausasa lafazi ba sai ma Kara harzuƙa da ta yi ta ce
"Eh lallai ba shakka ashe rashin arziƙin na ku gado ne. Yanzu dai ban da bakya tsoron Allah har ke zaki cewa wani bai gaji arziƙi ba alhalin ga tsiya nan har ta yi kuka a jikin ku tana neman a kawo mata ɗauki. Ai wlh Halimatu ce da kaico domin ba tayi miji ba, banda ƙaddara ina ita ina ita ina haɗa hanya da kwaɗayayyu irin ku? Da zaki ce sun zo suna an hana su abinci gayyar su aka yi ko kuma shi mara zuciyar ɗan na ki ya bada ƙwayar shinkafa ya ce a dafa balle har ki tada jijiyar wuya saboda an hana su abinci? Se ka ce dai ana yunwa zaki taho ƙafa da ƙafa kiyi rashin arziƙi saboda an hana abinci ba'a bayar ba ki ɗauki matakin".

Nemar hawayen da na ke yi na yi na rasa, na zabura na miƙe tsaye tare da ɗora hannu biyu a kai ina juya wuya kamar wacce aka tsare da bindiga tsabar yanda jini na ya daskare na ma kasa furta komai balle na hana Baba Jummai cigaba da wannna ɓarin bakin da take kamar wacce aka kwancewa kai.
Chapter 60 · 0% Book details