← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 158

Sashe 51

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dole kice kin manta mana tun da kin raina ni baki ɗauke ni a bakin komai ba; idan uwar da ta haife ki ce ta faɗa miki magana zaki tafi sharafin gaban ki ne ba tare da kin aikata abin da ta umarce ki ba?" Ta faɗa cikin tsananin fushi,
"Kiyi haƙuri" na faɗa murya ta na karyewa. Kamar ma na sake zuga ta ne tace
"Saboda tsabar baki da tausayi mutumin na kwance hajaran majaran bayan kece silar shigar sa halin da yake ciki amma abincin da zaki bashi ya ci kike baƙin ciki a kai; mu da muka zo jinyar sa baki bar mu ba kin haɗa mu da shinkafa da mai se kace wasu mabarata kika shige ɗaki kika bar mu wato kora da hali kike mana ƙarara, to yanzu zamu tafi se ki ƙarata Bilal dai ba zaki canza masa uwa ko dangi ba ba kuna ki isa ki hana wani nasa shigowa cikin gidan nan ba".

"Ikon Allah" na faɗa a zuciya ta dan ban hango dalilin wannan faɗan rashin dalilin nata ba; kuma ta ina na zama silar ciwon Bilal? Kiran da Anty Labiba ta mun daga kitchen ya sa na sake cewa tayi haƙuri na juya na tafi ina ji tana ci gaba da banbamin ta da faɗar maganganu.

"Me za'a girka miki kafin mu wuce?" Anty Labiban ta faɗa bayan dana shiga kitchen ɗin, se kawai na faɗa jikin ta na fashe da kuka. Yanda tayi sak nasan jikin ta ne yayi sanyi kafin ta tattaro ƙarfin hali ta janye ni tana cewa
"Meye haka kuma? Kukan me kike yi?"
"Dan Allah Anty badan hali na ba kiyi haƙuri" na faɗa cikin shassheƙa. Se ta ce
"Da kika mun me Halima?"
"Ni dai kiyi haƙuri dan Allah ki tausayawa rayuwa ta ki taya ni roƙon Abba ko sati biyu ne naje nayi a gida idan na warke se na dawo" na sale faɗa, se tayi tsaki ta ce
"Ke baki da baki ne halan? Ni da Allah ki nuna mun in da kayan girki suke idan kuma bakya buƙata mu tafi magriba ta kawo kai".

"Shinkafa kawai muke da ita se mai kuma kin ga bashi da lafiya balle ya bayar da abin da za'a yi cefane ko kuma ya siyo" na bata amsa cikin kuka. Se ta kama baki tana kallo na tace
"Su yan uwan nasa da suka cika gidan duk cikin su babu wanda yasan hanyar kasuwa ko da zasu siyo cefanen?"
Shiru na mata na ci gaba da kuka na. Duk yanda na ringa roƙon su akan su tafi da ni gida amma basu saurare ni ba, ƙarshe ma fasa jiran zuwan Mu'azzam ɗin suka yi da zasu tafi Mama Fauziyya ta ce mai aikin ta Baba Jummai zata dawo gobe zuwa jibi idan yaso se tazo ta ringa mana wanka Zainab kuma ta taya ni raino da gyaran gida tun da yanzu Yayar Bilal tana nan base ita ɗin ta rin ga zuwa ta mana kamar yanda ta yi niyya a farko ba.

Bayan sun fito Hajja ta tsayar dasu kamar gaske tana cewa
"Har kun fito kenan?" Mama Fauziyya ce ta amsa mata da
"Eh, mun fito".
"Allah sarki, abu dai duk yazo ba yanda aka tsammace shi ba. Banda ma dai Allah ya taƙaita ƙila da wata maganar ake yi yanzu ba wannan ba, daga zangar fa wai ya fita yabi sahun Halima shiru shiru tun da tace zata je gida da rana har gurin sha ɗaya bata dawo ba shi kuma wayar sa wai ta mutu taƙi ɗaukar caji kwata-kwata. Ni nayi mamaki ace a unguwa kamar wannan me cike da tsaro har a iya buge mutum a masa ƙwace; su kuma wanda suka tsince shi da rashin azanci maimaikon ko a masallaci ne su bayar da sanarwa se kawai suka kai shi asibiti suka yasar wai ashe suma ba yan unguwa bane hanya ce kawai ta biyo da su, mun dai shiga tashin hankali matuƙa amma dai mun godewa Allah tun da ya bayya na babu dai mashin babu waya, kuɗin akawut ɗin sa ma se jiya daya tura Habubakar ya ciro aka ce an kwashe komai; waɗannan azzaluman mutane dai se dai kawai mu bar su da Allah" ta ƙarasa tana share hawaye.

"Toh fa subhanallahi ashe abin da ya faru kenan" Mama Fauziyya ta faɗa cikin jimami, Hajja tace
"Wlh Hajiya. Abun dai ba daɗi, duk hankulan mu sun tashi ace mutum magidanci an neme shi a rasa har kwana biyu abun akwai ruɗani".

"Ikon Allah, amma Bilal ɗin ya ɓata har kwana biyu amma ba'a sanarwa da matar sa ba?" Anty Mimi ta faɗa, se Hajja tace
"To ai mu ma bamu san abin da ya faru ba se jiya da safe. Tun dai da ya baro can gidan waccen ranar bamu sake ji daga gare shi ba na san kuma lafiyar Allah Bilalu baze kwashe kwana biyu bai je mana ba, idan kuma tafiya ce ta kamashi dole ze sanar mun kuma ze kira a waya mu gaisa amma dai bamu ɗauki abun da girma ba tun da ba wani labari muka samu mara daɗi ba.

Abokin ƙanin sa ne fa can ya gano shi a Asibiti, banda shaƙiyancin kuma irin na yan zamani maimakon kai tsaye ya faɗa masa ga Bilal a asibiti kawai se yace masa wai ina yayan su? Ya kamata ya bincika shi yaji ko yana lafiya. To tun da dama muna ta jimamin kwana biyu mun ji shi shiru shine fa yana faɗa mun hankali na ya tashi muka taho nan gidan babu kowa se makwafcin sa yace mana ai yau kwana biyu kenan ba kowa a gidan. A lokacin har Habubakar ɗin yace a kira Halima muji ko tana da masaniyar in da yake ni kuma nasan in har ita wani abu ya same ta ba zamu kasa ji daga gare ku ba dan haka na ce masa aa kar a tayar mata da hankali ga tsohon ciki mu tafi gurin yan sanda kawai a kamo shi abokin nasa daya fara kawo zancen a tuntuɓi Bilal aji ko yana lafiya. Shine fa da aka kamo shi ya ce ya ganshi a Asibitin Murtala se likita ne ya mana bayanin yanda aka kawo shi babu waya kuma baya magana shi yasa suka rasa ta yanda zasu nemi yan uwan sa dama jiyan suke niyyar kai cigiya gidan radio".

"Toh Allah ya rufa asiri ya kiyaye faruwar na gaba bari muje mu har an fara kiran sallah" Anty Labiba data gaji da sauraron ta ta faɗa tana yin gaba se Hajja tayi saurin tare su da cewa
"Nace mai zai hana ku tafi da Halima gida Hajiya? Tun da kunga shi mijin nata ba lafiya ga ɗanyan jiki kada ɗawainiyar tayi mata yawa dan shi ɗin ma can gida na zamu wuce dashi yanzu".

"Babu damuwa ai Hajiya ku tafi da shi ɗin Allah ya bashi lafiya ita ɗin se tayi zaman ta za'a kawo mata waɗan da zasu taya ta zama" Mama Fauziyya ta faɗa. Se Hajja tayi shiru kafin kuma ta tace
"Amma dai haihuwar fari a al'ada ai gida ake tafiya ayi wanka balle ita wannan da ga halin da ake ciki"

"Wace al'ada mu ai tuni muka yada zancen zuwa wanka gida, gara dai yarinya ta zauna a ɗakin ta. Dama saka ruwa ne wahalar jegon ai kuma za'a kawo wacce zata ringa yi mata ina ganin ai babu wata damuwa" Mama Fauziyyar ta sake bata amsa dan tuni Anty Labiba ta fice Anty Mimi kuma ta zama hoto kallon Hajjan kawai takeyi.

"Ai shikenan tun da haka kuka zaɓa se ta zauna, amma kowa na ɗauke ɗan sa ya kula dashi ki zaku bar taku bakwa ko tsoron ya lallaɓa da ɗanyan jego ya haike mata duk matsalar data sameta ai ku ne da kuka na wani ba" Hajja ta faɗa cikin fushi fushi.

"Ba abinda ze same ta se alkhairi Hajiya idan ma kuma ya haike mata ai ba haramun bane matar sa ce, Halima dai ba in da zata je a gidan ta zata yi jego" Mama Fauziyyar ta bata amsa itama cikin fushi daga nan suka yi tafiyar su.

Komawa nayi na zauna kan gado na tallafe fuskata naci gaba da share hawaye ina jiyo Hajja na masifa da faɗar maganganu bayan data tabbatar sun fice daga gidan. Ban san ya akayi ba kuma da Hajja ta tashi tafiya basu tafi da Bilal ɗin ba kamar yanda tace. Na zata ita ma Anty Aminar ta tafi se bayan tafiyar su Hajjan kuma naga ta dawo tace mun gida taje ta dawo, har da cefanen kayan miya tayo da nama da kaji guda biyu a daren ta dafa mun ɗaya tace na zauna na ci, se da na ƙoshi kafin ta sakawa Bilal sauran yaci.

Da Bilal ya shiga ɗaki ze kwanta ta ce na tashi na je ko akwai abin da ze buƙata na taimaka masa tunda har sannan jikin sa be gama yin karfi ba. Yana zaune akan carpet ya ɗora kansa jikin gado na shiga, cikin sanyin da muryar sa tayi ya miƙa mun hannu yana cewa
"Zo Halima". Na isa kusa dashi na zauna ya kwantar da kaina a kafaɗar sa yana cewa
"Ki yafe mun Halima" ban san yafiyar me yake nema ba amma kawai naji hawaye sun ɓalle mun. Ya rungumeni yana cewa
"Nasan haƙƙin ku ne ya kama ni amma na godewa Allah da ban mutu ba tareda na nemi yafiyar ku ba, je ki karɓo mun ɗana na ganshi" ya faɗa yana saki na. Se da na share hawayen kafin na fita na karɓo shi, ya haɗa ya rungume mu ni da yaron yana cewa

"Kiyi haƙuri da abin da nayi miki ke da Amirah waccen ranar wlh sharrin shaiɗan ne ban ma san meya hau kaina har na aikata abin da nayi ba".
Chapter 51 · 0% Book details