← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 158

Sashe 32

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dake muna da kaji da jan nama ba'a fi kwana uku daya siyo su ba kajin guda huɗu ne manya manya se naman shima da ɗan auki se na ɗibi kaji uku na samu yaro ya yiwo mun cefanen miyar taushe na jiƙa farar shinkafa akan zanyi waina da sinasir. Tun daren na haɗa miyar ya rage ganye kawai zan zuba na saka ta a freezer na kwaɓa meat pie shima na haɗa na deɓi kaɗan na soyawa Bilal na saka sauran a fridge. Ina da samosa da spring rolls dama nace se na haɗa da safen na soya su tare. Na gaji lilis se goma saura na gama gyaran gida da wanke wanken abubuwan dana ɓata dan har zoɓo na haɗa, ina wanka Bilal ya dawo daga ganin fuskar sa na san babu lafiya nan yake sanar mun ɗan Fadila ne ya rasu. Na taya su jimami har nace zan kira ta lokacin yace na bari se da safe, haka nan muka kwana yanda Bilal ya damu kamar ɗan cikin sa ya rasa. Na ringa ayyana yanda zeyi farin ciki idan ya san ya kusa samun nasa ɗan shima.

Washe garin da wuri ya shirya dan zasuyi jana'izar yaron kafin lokacin sallar idi. Nima kafin ƙarfe tara na gama abincin sallah na, na zuba na gidanmu harda na Anty Labiba na ware na gidan su Bilal sannan na fitar da na maƙwafta. Sayyadi almajirin Maman Yusuf na bawa kuɗin Adaidaita ya kai na gidan mu dan ya san gidan ina aiken sa, se gurin sha ɗaya Bilal ya dawo tare da abokanan sa su uku. A falon sa na aje musu abinci suka ci se da akayi azahar suka tafi yace mun na shrya daya dawo daga sallah zamu tafi can gidan. Tsaf naci kwalliya da ɗaya daga cikin laces ɗin dana ɗinka. Yaron cikin jikina yasa fatata ta goge nayi shar dani ga yar kiɓar dana ƙara ta sake fito da albarkatun jikina. Hijab daya dace da kayan na saka dan kar suce suna zaman makoki ni kuma nayo kwalliya. Yana shigowa ya ɗaga ni ya rungumeni, se da yayi kissing goshi na ya haɗe hanci na da nasa yana kallon cikin ido na yace

"Kin san me yasa name ƙara sonki kullum?" Na girgiza masa kai alamar aa, se ya maida kaina ƙirjin sa yace
"Baki taɓa bani kunya ba. Duk sanda zan cika baki akanki se kin aikata fiye da yanda na kwarzantaki. Kasada kawai nayi da su Mansur suka ce zasu biyo ni suci girkin amarya. Nasan ba muyi zancen za kiyi abincin sallah ba amma sanin da nayi tunani na dana Halims a tare suke tafiya banyi shakku akan zaki fitar dani kunya ba se gashi harda snacks. Ke dai Allah yayi miki albarka ya barmu tare kinji my Halims" ya ƙarasa yana brushing lips ɗin sa akan nawa. Na ringa murmushi kamar wawuya jin ya yaba abinda nayi. Se da muka ɓata lokaci a nahiyar soyayya dan se da ta kaimu da canza wanka kafin mukayi sallar la'asar mukayi sabon shirin fita. Cewa yayi cikin sa ya zazzage wai dama ba wani abin kirki yaci ba duk su suka cinye. Na sako masa sinasir guda ɗaya yana ci yace

"Wato yarinyar nan kuɗi ne dake, kikayi ɗinki sallah Allah sarki ni da tsohon kaya naje idi ga kuma daƙwalen kaji kin zuba mana a miya ai se ki bani barka da sallah kuma na samu na zuba mai a mashin". Se da nayi far da ido kafin nace

"Ka so tsokana dai kawai da kayan da kajin naga duk kai ka siya, ni sarrafa su kawai nayi". Be sake magana ba daga yanda naga fuskar sa ta canza lokaci ɗaya kuma nasha jinin jiki na se dai duk son na hakaito me ze kawo ɓacin ran sa lokaci ɗaya haka na rasa se kawai na kama kaina nayi shiru nima. Sanda muka isa gidan su lokacin Abubakar ya dawo shima ya sauke kwanukan abincin da na bashi ya yiwo musu gaba dashi,
"Duka kajin kika dafa kenan?" Ya faɗa a saitin kunne na daidai sanda Hajja ta buɗe flask ɗin miya.
[1/14, 2:09 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 14*

Afuwan kun jini shiru. Wadanda suke cikin comment section group na bayar da uzuri.

A ɗarare na ƙarasa yinin cike da taraddadin yanda zamu kwashe da Bilal idan mun koma gida. Se da akayi magriba ya turo mun text a waya in fito mu tafi. Jikina ya sake yin sanyi, haka nayi sallama da Hajja da sauran yan gidan su tana ta mun godiyar abin arziƙi da tace an kawo musu daga gidan mu cikin azumi ga kuma turmin atamfa dana kai mata dama yanzu kuma na kaiwa mejegon itama Atamfa da wani lace cikin ɗinkunan biki da aka mun sakawata ɗaya ranar naje gidan dashi tace ya mata kyau ni na manta ma da munyi maganar se bayan data haihun ta roƙe ni in bata tayi fitar suna dashi.

Tare da Nasir na same su tsaye jikin motar Nasir ɗin, muka gaisa a mutunche Bilal ya shiga mzaunin gaba hakan yasa na fahimci Nasir ɗin ne ze sauke mu gida. A hanya suna ta hira da zarar Nasir ya sako ni se naji Bilal ya ɗauke wuta gane hakan yasa ko da Nasir ɗin ya sake tsomani cikin maganar nayi kamar ban ji shi ba. Ni kaɗai na sauka ya miƙa mun muƙulli ba tare da ya kalle ni ba na wuce ciki ina tunanin ina kuma zasu je kuma har se yaushe ze dawo amma babu fuskar da zan iya tambayar sa. Be shigo gidan ba se goma da kwata, ina zaune a falo naji tsayuwar mashin ɗin sa, ban motsa ba nasan cikin biyu ko dai ya buga ko ya kirani a waya tun da be fita da key ba ilai ko se ga kiran sa a maimakon yanda na saba daya kira in tashi naje na buɗe Get ɗin tunda nasan kiran na menene se kawai na amsa wayar.

Da murya kamar me bacci nayi sallama, ina jin sa yaja tsaki kafin yace
"Zo ki buɗe" daga nan ya katse wayar. Se da na koma ɗaki na ƙara turare kamar me fita zance sannan na saka hijab na fita. Ban san na ƙarawa kaina laifi ba, ina buɗe ƙofar ƙiris ya rage ya ture ni da tayar mashin ɗin ya shigo ciki, se da na kulle ƙofar na bi bayansa yana kafe mashin ɗin ya juyo kamar ze rufe ni da duka yana cewa
"Tsabar kin mayar dani ɗan iska na kiraki amma kiyi zamanki se yanzu kika ga damar zuwa ki buɗe kofar ko?"

Kallon sa kawai nayi takamaimai ni ban fahimci dalilin wannan hasalar tasa ba. Fuuu ya wuce ɗakin sa, har na bi shi se kuma na juya na shige falo ina ƙarfafa kaina akan bazan bi ta kansa ba tun da dai ba wani abu na masa ba. Sinasir ɗin dana ɗumama na saka masa guda ɗaya da yar miya a bowl na haɗa da tea dana rigada na dafa masa na ɗora komai a try harda ruwa na wuce ɗakin nasa. Ban same shi a falo ba, se na aje kayan na wuce cikin ɗakin ƙarar saukar ruwa da kayan daya cire dake kan gado yasa na gane wanka yake yi dan haka na koma falon na zauna. Kusan minti goma ya fito ya shirya cikin jallabiyya yana ta zuba ƙamshi. Bilal ba dai tsafta da gayu ba, komai sanyi ko ruwa baze kwanta ba tare da yayi wanka ba. Na kan tuna Anty Labiba da take cewa duk buge ne gayun nasa waya sani ma ko tsaka tsami yakeyi ya fesa turare gashi dana zauna dashi na tabbatar da tsaftar tasa ta gaske ce in dai ɓangaren tsafta ne na sarawa Bilal abinda kuma yake ƙarawa abin armashi bashi da son jiki. Yanda baya son ƙazanta baya taɓa bari in da yake wani abu ya kasance da datti ba kuma ya jiran wani ya masa da ya ga guri be masa yanda yake so ba ze tashi ya gyara.

Kamar ma be lura da ni ba ya zauna kan kujera yana wani cin magani, nayi murmushi na matsa in da na ajiye kayan abincin ina cewa
"Ga abinci". Ban damu da shirun da yayi ba dan idan ba ze ci ba nasan ze ce Aa, na buɗe miyar na tura masa try ɗin gaban sa, kwanon miyar ya ɗauka ya kalla kafin ya watsa mun wani kallo yana cewa
"Shikenan naman da yayi saura?"
"Pieces biyu ya rage na saka maka ɗaya na aje ɗaya zan ci da safe" na bashi amsa ina tsiyaya masa shayi a kofi. Ko da ban ɗaga kai na kalle shi ba jiki na ya bani kallo na yake yi ko ma na ce harara ta. Ina jin sa yayi ƙwafa, se lokacin na ɗaga kai na kalle shi duk kuma yanda naso da in share kar na tanka masa na kasa, tsautsayi yasa na furta
"Ko in ɗakko maka ne naji kaja ƙwafa karma naci nayi amai tunda ba'a bani ba".
Chapter 32 · 0% Book details