← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 158

Sashe 150

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Alhajin Allah kada ka bada maza mana, ni idan na faɗa maka irin ibtila'in daya ringa saukar mun bi da bi sai kayi mamaki amma dana mayar da komai gurin Allah ba gashi ya wuce ba? Ita rayuwa dama akwai samu akwai rashi ai, kuma sau tari jarabta tana zama matakin nasara idan kayi haƙuri sai kaga Allah ya maido maka da dubunsu" Alhaji Yusuf ɗin ya faɗa Bilal sai jin sa kawai yakeyi ba dan yana gane komai ba.

Har ƙofar gida ya kaishi kafin ya masa sallama ya wuce yana sake jaddada masa kada fa ya sakawa kansa damuwar da zata haifar masa da wata rashin lafiyar yayi biyu babu, dukiya dai ta tafi ba dawowa zatayi ba, a waya ya shiga kiran Zulaiha dan baya jin zai iya fita daga motar da kansa. Ƙirjinsa ya masa nauyi haka kansa sara masa yakeyi sosai tamkar wanda ale kiɗan gangi a cikinsa.

Ya kira Zulaihan yafi sau biyar bata amsa ba daga ƙarshe haka ya lallaɓa baya ko ganin gabansa ya fita daƙyar bai ko kashe motar ba balle ya kulleta ya fita yana bin bango har ya tsaya jikin get ɗin kafin ya shiga bugawa da duka ƙarfin daya rage masa.

ZULAIHA

Tana kwance tana baccin huce gajiyar da Ahlan ya tara mata a haɗuwar da sukayi jiya. Tunda suka fara mu'amala babu wani abu daya taɓa shiga tsakaninsu, zai ɗauketa su fita yawo gari ko suje Hotel amma ba abinda yake mata sai dai suyi hira duk shaye-shayen da yake ƙoƙarin koya mata sai jiyan tukunna ta kasa riƙe kanta dan tunda Bilal ɗin ya tafi ita kaɗai ta san a halin da take ko da ba wani samun yanda take so takeyi sosai a gurin nasa ba amma yafi babu, yanzun da baya nan ga hirarraki da wasannin banzan da sukeyi da Ahlan ɗin kullum idan ta koma gida har kuka takeyi kafin ta samu tayi bacci, jiyan ji tayi kamar ya zuba mata wani abu a lemon da suka sha dan sai bayan komai ya lafa kuma ta shiga jin haushin kanta haɗi da nadamar abinda ya faru ƙarshe bata ko jira shi ba ta hawo Adaidaita sahu ta koma gida.

Tun bayan tafiyar Bilal ta samu free get, gari na wayewa zata yi wanka ta fice sai dare zata dawo, hankalinta kwance take al'amuranta. Ɗaki Ahlan ɗin ya kama musu ko bai kirata ba zata tafi tayi kwanciyarta ta wuni a can irin yanda ta saba a lokacin da take gida sau da yawa zata fita da sunan makaranta amma hotel zata wuce can zata wuni sai magriba ta koma gida abunta.

Duk yawon makarantar data ringayi asar kuɗi kawai ta ringa yiwa Bilal amma ba karatun takeyi ba, canjin department ɗin ta na uku kenan yanzu ita daya kamata ace tayi graduation kamar yanda Bilal ɗin yake zato amma maganar gaskiya 200L take shima da taimakon wani saurayinta da yake HOD a wani department shi ya shiga ya fita idan ba dan haka da tuni an koreta tareda su Suwaiba. Toh yanzun ma dai bata da banbanci da korarriyar dan tuni semester tayi nisa har ana shirin fara exams amma bata san ta yanda zata fara sanarwa da Bilal ɗin zata koma makatanta ba.

Ƙarar bugun da yakeyi tamkar zai ɓalle ƙofar ya farkar da ita, a gigice ta rarumi zani ta ɗaura ta fita tana murza ido, sai data tareshi ganin yana shirin faɗowa. Jiki na rawa ta kamashi suka shiga ciki ya zube akan carpet yana sauke numfashi kamar mai cutar Asthma. Yanayin da yake ciki ya saka ta wartsake babu shiri ta rarumo wayarta ta shiga kiran layin Hajja.

Hajja na zaune tareda Anty Ladidi tana bata labarin halin da ake ciki, Ladidin tayi tagumi tana cewa
"Tun jiya Yaya Habiba ta kirani ai ta gaya mun harda yanda suka tarar da Fadila itama. Ashe ɗan abu ta kazan uba mijin nata mayaudari ne, ya zo ya yiwa mutane lamɓo an bashi yarinya yaje yana gana mata azaba kamar wanda dama yayi auren ɗaukar fansa? Ai nace mai yasa suka barota a gidan basu tasota a gaba sun taho ba? Ko sai ya kasheta tukunna sai ya bugo waya yace azo a ɗauki gawarta ko me?"

Cike da mamaki Hajja ta ce
"Wace Fadilar kike magana akai?"
"Auta mana ko muna da wata Fadilar ne bayan ita?" Ladidin ta bata amsa, kafin ta sake magana wayarta dake kan cinyarta tana jiran kiran Bilal tunda Abubakar ya gaya mata ya tura masa saƙo ta shiga ringing, ɗagawa tayi kawai ganin number daga can muryar Zulaiha ta cika mata kunne cikin tashin hankali take sanar mata ga Bilal ya zo ita dai bata gane kansa ba gashi nan numfashinsa yana sarƙewa.

Miƙewa Hajjan tayi da sauri kafin kuma ta koma kamar wacce aka ja tayi zaman yan bori, cikin tsananin azabar data ziyarci bayanta zuwa ƙugunta ta saki wayar hannunta tana wayyo Allah dai-dai nan Abubakar ya shigo, ganin yanayin Hajjan bai ko tsaya jin ba'asi ba ya kinkimeta daƙyar, tare suke da Abokinsa Isma'l ya shigo ya gayawa Hajja abokin zai shiga su gaisa kenan dan haka ya sakata a motar Isma'l ɗin suka wuce Asibiti da sauri.

A hanya yake tambayar Anty Ladidi mai ya faru tace masa bata sani ba an dai kirata a waya ne ta miƙe tsaye kuma ta koma ta zauna gashi sun baro wayar a gida balle subi ba'asin kiran ko na menene?

Aminu Kano suka kaita sun ci sa'a babu ɓata lokaci aka karɓeta emergency, a ransa ya ringa jin babu daɗi, ƙaryar da yayi saboda Bilal ya zo gashi Allah ya tabbatar da abun. Layin Bilal ɗin ya shiga kira cikin sa'a Zulaiha dake ta sake gwada layin Hajja taji ƙarar waya a jikinsa ta zaroshi ganin Brother ya saka ta ɗaga da sauri kafin ma yayi magana ta shiga karanto masa halin da ake ciki.

Salati ya shiga yi jin wata sabuwa kuma take kuma ya fahimci dalilin faɗuwar Hajjan, ya balbaleta da masifa yana cewa
"Ke mahaukaciyar ina ce da zaki kirata? Mai yasa baki nemi wani daga cikinmu ba?"

"Da Allah Malam dakata mun, ina da number ku ne ko ya aka soma? Toh ban kira ɗin ba idan kaga dama ka tsaya masifa kada Allah ya sa kazo ka taimaka masa" ta bashi amsa haɗi da yin tsaki kafin ta kashe wayar.

Tashi tayi ta wuce ɗaki ta sako doguwar riga kafin ta fita waje ta nemo wanda zasu kama matashi kawai ta kaishi Asibitin, ta manta da mota shiyasa ma har ta tsaya neman taimako zai zo yana nema ya faɗa mata magana.

Mamaki ya kamata ganin babu mota a ƙofar gidan, amma kuma data tuna a yanayin daya shigo sai mamakin ya gushe tunda dai ba zai iya tuƙi a hakan ba ta yuwu wani ne ya kawo shi. Ganin motar Alhaji Zakariyya mai gidan dake jikinsu tana tahowa ta shiga ɗaga masa hannu, bayan ya tsaya ta faɗa masa abinda yake faruwa, shi ya kira masu gadin kan layin suka shiga suka ɗakko Bilal ɗin suka sakashi a mota kamar matacce kafin ta shiga suka wuce Asibiti.

Wani private Asibiti ya kaisu dukda ta gaya amsa Aminu Kano suke zuwa amma yace gara aje mafi kusa, idan yanayinsa ya dai-daita ya fita daga hatsari sai a mayar dashi ko ma inane. Suna tare da Alhaji Zakariyyan yana ta kwantar mata da hankali Bilal kuma yana ciki tareda likitoci har sanda Abubakar da ɗaya daga cikin masu gadin ya gayawa Asibitin da Alhaji Zakariyyan yace zasuje ya isa. Ya ballawa Zulaiha harara kafin ko ya ɗauke ido itama ta maka masa tata, yayi ƙwafa ya wuce suka gaisa da Alhajin yana amsa godiya sai lokacin ya wuce bayan ya musu fatan Allah ya bashi lafiya.

Ba jimawa Likita ya fito, Zulaiha ta tashi d sauri haka Abubakar ya kallesu yana cewa
"Kune yan uwan mara lafiyar da aka kawo ɗazu?"

"Eh ni matarsa ce" ta bashi amsa da sauri Abubakar ya sake hararta kafin ya ce
"Ya jikin ɗan uwana likita? Mai ya same shi dan Allah?"

Office yace su bishi, a taƙaice yayi musu bayanin jinin Bilal ɗin ne yayi mugun hawa sakamakon wata damuwa ko tashin hankali daya fuskata a bazata.
"Mun bashi duk wani taimako da yake buƙata a yanzu ya kuma samu bacci zamu jira zuwa ya farka kafin kuma mu san mataki na gaba" Likitan ya faɗa. Godiya suka masa suka fita Abubakar ya wuce gurin biyan kuɗi ya bada abinda aka buƙata. Yana gurin Anty Amina ta sake kiransa dan suna hanyar kai Hajja Asibiti ya kirasu duka ya faɗa musu harda Fadila da ya samu number ta cikin sa'a, suna gama waya da Zulaihan kuma ya sake kira ya sanar musu halin da Bilal ɗin yake ciki, akayi sa'a kuma Anty Amina tana ta gurin Asibitin Malam ɗin dan haka tana zuwa tace ya tafi gurin Bilal ita da Ladidi zasu tsaya da Hajja kafin su Habiba su ƙaraso.

Kira tayi tana sake tambayarsa jikin Bilal ɗin yace musu da sauƙi da kuma abinda aka ce yana damunsa.
"Itama Hajjan sunce jininta ne ya hau" ta faɗa masa, yayi ajiyar numfashi ya ce
"Nayi tunanin haka dama, amma dai babu wani abu bayan wannan ko?" Ya tambayeta. Tace

"Haka muke fata amma dai basu ce komai ba yanzu sun ce sai ta farka an gani"

"Shikenan, bari na tambaya nan ɗin naji idan zai yuwu mu ɗauke shi kawai a dawo dashi nan ɗin dan nan Asibitin bai yi mun ba gaskiya" Daga haka sukayi sallama.

Gurin likitan ya koma ya faɗa masa buƙatar sa sai likitan yace suyi haƙuri dai zuwa ya farka idan ma zasu kaishi wani gurin.

"Ka raina kulawarmu kenan Alhaji" Likitan ya faɗa yana murmushi, Abubakar ya ce
"Ba haka bane, mahaifiyarmu ce itama babu lafiya tana can AKTH ɗin, idan aka haɗe su guri guda hankalinmu zai fi nutsuwa guri ɗaya shine dalili"

"Haka ne gaskiya, Allah ya bata lafiya babu damuwa kuma da zarar naga yanayin jikin nasa yayi yanda za'a iya motsashi zuwa wani guri sai ayi hakan" cewar Likitan.
Chapter 150 · 0% Book details