Sashe 7
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Se naji abun wani iri amma na kanne nace
"To banda abinka dama abincin ai ba kai kaɗai nayiwa ba kuma yana da yawa zasu ɗiba nasu su rage maka"
"Ragowar wasu zanci kenan?" Ya faɗa kamar a fusace, se kuma yayi shiru na tsaida idona akansa ina karantar yanayin fuskarsa, se kuma yayi murmushi yace
"To an gode My Halims Allah ya bada lada. Bari na shiga ciki muyi sallama da Yaya Zubaida nasan yanzu zata wuce se nazo na raka ku". Gefe muka tsaya kusan minti biyar ya fito kamar ransa a ɓace, Adaidaita ya tare mana muka shiga ganin ya tsaya be shiga ba yasa na kalle shi nace
"Ka fasa raka mu ne kuma?"
"Zanzo kawai anjima, yanzu zanje gidan gidan Muslim ne naga ko zan samu abinda zanci dan yunwa nake ji sosai wlh". Da mamaki nace
"Wannan abincin kuma fa?" Ya ɗauke kai gefe yace
"Sun cinye, kin san duk bamu wani tsaya munci abinci ba muka taho shiyasa dama da a gurina kika ajiye na ɗiba nawa se na kai musu sauran".
Harga Allah seda naji wata kunta ta kamani amma kuma yunwar da yace yanaji ita ce a gabana yanzu dan haka nace
"Amma basu kyauta ba, to ko muje gida se na dafa maka ko indomie ce. Matar Muslim dake fama da kanta babu lallai ai tayi girki ma". Seda yayi jimm kafin yace
"Amma ba zaki wahala ba? Kin gama wannan girkin ki sake yin wani?"
"Dafa maka abinda zaka ci kake kira da wahala?" Na faɗa ina langwaɓar da kaina ina kallonsa. Me Adaidaitan ya kalla kafin yace
"Shikenan nan, kuje bari na canza kaya se na taho" ya ciro ɗari biyar daga aljihunsa ya bawa me Adaidaitan, seda ya karɓi canji kafin ya koma cikin gidan mu kuma muka wuce. Kallona kawai Mama tayi sanda nake gaya mata zan sake dafawa Bilal abinci wancan da aka kai musu ya ƙare,
"Wato gidansu kika je? Ke wace irin yarinya ce mara jin magana anya Halima kina son ki siyawa kanki ƙima da mutunchi a idon dangin Bilal kuwa? Banda ke sakarya ce a ina kika taɓa ganin mace na zirgilli irin haka akan namiji?" Mama ta faɗa cikin ɓacin rai, nayi ƙasa da kaina kawai na kasa ce mata komai ta cigaba da bambamin faɗa kafin ta wuce ɗaki, seda ta kullo ƙofa sannan na wuce kitchen jiki na rawa na ɗora masa Indomin. Kaji biyu na saka a abincin da na musu ɗazu, dubu biyar Abba ya bani yace nayi cefane harda lemo katan ɗaya da ruwa shima katan na siya musu. Seda na duba freezer babu sauran nam se kifi, Bilal baya son kifi dan haka kawai na daga masa ita da karas da kabeji na soya masa ƙwai guda huɗu. A falon Abba na shirya komai, seda na fita tsakar gida zan wanke kayan da nayi amfani dasu dan famfon cikin kitchen ɗin ya lalace se na gashi tsugunne gaban Abba suna magana.
Ban sam me suka tattauna ba na koma ciki bayan ya shigo seda ya cinye indomin tas yasha lemo kafin ya kalleni yana murmushi yace
"Se yanzu na fara gane kaina"
"Dole ai, ka sha tafiya ga yunwa kuma ai kayi ƙoƙari ma" na faɗa ina murmushi se yace
"Yanzu Abba yake mun magana. Ai ma zata ma kin gaya masa abinda na sanar dake se yace mun wai kin ce masa ƙarshen wata za'a zo gashi watan ya mutu wani ya kama shima harya ƙare shiru me yasa zaki masa ƙarya?"
Kallonsa nayi jin abinda ya faɗa wai nayiwa Abba ƙarya, bance masa komai ba na maida kaina ƙasa ina jan zaren mayafin jikina ina jinsa yana cewa
"Kin kasa fahimtar abinda nake gaya miki Halima. Bawai bana son azo maganar saka ranar nan bane aa ina duba abubuwan da suke gabana daya kamata na kammala kafin ace an fara maganar aure. Yanzu idan akayi sa rana kowa ze tada hankalinsa ne da son jin yaushe za'ayi biki, da zarar an ɗan samu akasi an ɗaga daga sanda aka faɗa se kiji maganganu su kansu iyaye zakiga sun ɗauka kamar mutum ya shigo da shiririta cikin abun. Ni yanzu babban abinda yafi tsayamun shine na kammala gini na kin san kuma dai gini abu ne me buƙatar tana di da lokaci dan ko da kuɗin a zube kin san aikin gaggawa baya ƙarko"
"Haka ne" na faɗa ina kallonsa ƙwaƙwalwata na son bawa maganganun sa ajin daya dace dasu. Yaci gaba da cewa
"Kin san ina da taste, akwai plan ɗin dana tsarowa gini na da idan yanzu nace na katse ko na canza da wani abu daban baze bada yanda ake so ba. Kinga ginin nan shi kaɗai ne nake so ace na kammala duk wata sauran hidima za'ayi abinda ya samu ne na sani lefe ma zaki iya yafe mun ko My Halims tunda dama ke ai kullum cikin sababbin sutura kike ko waɗannan na jikinki ma ai ban taɓa ganinki dasu ba" ya ƙarasa yana wata dariyar data ƙular dani, kafin nace wani abu ya tareni yana cewa
"Wannan bayanin nake so kiyiwa Abba nasan zw fahimce ni tunda ina da hujja me ƙarfi ko shi Baba Salahun idan aka fahimtar dashi ze gane".
"To amma Bilal me ze hana ka kama haya mana ko da na shekara ɗaya ne pending ka ƙarasa ginin naka? Na faɗa bayan dana gama jin nasa uzurin, seya wani kalleni kamar wadda na faɗa masa mugun abu yace
"Haya? In kama haya fa kike cewa Halims? Yanzu ke ba zakiji kunya ace gidan haya aka kaiki ba?"
"Wace irin kunya kuma Bilal mutane nawa suke rayuwa a gidan haya? Ita kanta hayar ai se wanda ya isa ne ma yake da hali ze kama naga wasu sedai su nemi a basu aro" na bashi amsa ina ɓata fuska seya girgiza kai yace
"No Halims wace irin haya ana zaune ƙalau se kace matsiyaci. Mu gama zagin abokananmu saboda rashin zuciya sun kasa mallakar gidan kansu se kuma kawai nima na ƙare a haya bayan Allah ya rufa mun asiri ina da yanda zanyi"
"Oh ashe ma kana da yanda zakayin niyya ce kawai bakayi ba ko kuma nace auren nawa baka shiryawa ba. Da kuma zaka ce tsiya ce take sakawa ayi haya har kana zaginsu wasu da hakan shi muhalli tamkar rabon haihuwa da silar mutuwa Allah ke saukar dasu don yanda kaso da faruwar su ko kauce musu baka da wayo baka da dabara akai kuma idan Allah yaso ya nuna maka iyakarka seya jarabce ka kaima duk arziƙin ka ya hanaka mallakar gidan kan naka. Mutane nawa keda rufin asiri amma har suka mutu suka ƙare rayuwar su a gidan haya? Ka fito fili kawai ka faɗa mun abinda yake ranka game dani domin na fara gajiya da uzurin ka da basa ƙarewa kullum da wanda zaka zo dashi to kawai ka faɗa mun matsayar maganar mun, idan yi yi idan bari bari kawai nagaji da sa banga ƙaho ba Bilal" na faɗa ina miƙewa tsaye.
[12/13/2024, 2:34 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*PAGE 4*
Ban yarda da gaske Bilal yake da yace ze turo saka rana ba se ranar Juma'a da Baba Salahu yazo gidan mu bayan sun gama maganar da za suyi da Abba yasa aka kirani. Seda muka gaisa kafin cikin tsare gida kasancewar sa me ɗan zafi ya kalle ni yace
"Ranar lahadi idan Allah ya kaimu iyayen yaron da yake neman ki suka ce zasu zo saka rana, ina fatan da sanin ki?".
Duk se na duburburce, abun yazo mun a ba zata domin banyi tsammanin faruwar hakan ba. Waccen ranar birkice masa nayi dagaske, duk yanda ya so ya lallaɓa ni naƙi biyuwa ƙarshe na kore shi nace karya sake zuwa in da nake tun da ba aure ya shirya yi ba na gaji. Haka ya tafi yana waige na kuma na kashe wayata, dukda se da nayi kuka tamkar raina ze fita zuciya ta ringa ingizani dana kira shi amma dake har raina na shirya motsawa in tabbatar da matsayina a gurin Bilal tilas na jure.
Zuwan sa uku bayan nan bana fita na kuma yi blocking ɗin sa a wayar Mama tun da ya kira sau ɗaya, sati ɗaya kenan yau daidai se gashi Baba Salahun ya zo mun da labari mafi daɗi a kunnuwana.
Sun kunyar da kai nayi ina murmushin dana kasa hana kai na, Abba dai kallo na kawai yake yana murmushin shi ma, seda Baba Salahu ya sake maimaita mun tambayar kafin cikin jin kunya nace
"Eh, da amincewata Baba".
"To madalla, dama abinda nake so na tabbatar kenan da yardar ki kafin su zo saboda kin san ni bana ɗaukar shaƙiyanci irin naku na yaran yanzu. Se anyi magana ta manya daga baya kuzo da wasa shi yasa kafin manema su zo se na tabbatar da amincewar yarinya yan da zan ci ƙaniyar duk wadda ta dawo zata kawo mun iya shege. To Allah ya sanya alkhairi ciki yasa zamu ga lokaci". A zuciya ta na amsa da "Amin" Abba ya amsa a fili daga nan ya sallame ni na fice. Tsabar murna ban san lokacin dana daka tsalle na rungume Mu'azzam da mu ka ci karo da shi ze shiga falon ba, ya ture ni yana cewa
"Ke meye haka?"
"Alhamdulillah Allah lokaci yayi na kusa zama matar Bilal" na faɗa cikin maɗaukakiyar murna kafin na zube a gurin nayi sujjadar godiya.