Sashe 27
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dubu ashirin na yan ɗari biyar sababbi Hafiz ɗin ya ajiye mun, nayi nayi ya ɗauke kuɗin sa har matar sa na bawa amma tace aa kyauta ya mun tukuicin girki idan ban karɓa ai ba zasu ji daɗi ba se dai idan rainawa nayi hakan ya sa nayi masa godiya ina ganin Bilal nata kallo na na aje kuɗin kan center table muka raka su muna dawowa ya kwashe su yana cewa
"Tun da bakya so ni bari na ɗauka".
"Kai kuma baka san fulako ba so kake kawai an bani kuɗi nayi zuruf na amshe ai se ka mun faɗa ma" na faɗa ina dariya. Na ɗauka wasa yake da ya ɗauki kuɗin ze ajiye mun daga baya shiyasa ban damu ba. Sati biyu da suka biyo baya aka fara registration na NYSC.
Se da naje Cafe suka ce mun se na kawo certificate of marriage da appointment letter ko ID card na miji na da kuma shaidar canjin suna in dai ina so a bar ni a garin da nake kuma kar nayi zaman camp. Tilas na haƙura da yi a ranar na koma gida, Bilal baya nan sun tafi Katsina gaisuwa acan zasu kwana dan haka na kira shi na gaya masa yace na bari idan ya dawo se muyi magana. Washe gari suka dawo, be tada zancen ba se ni ce na masa magana ya ce mun ze tambayi in da akeyin certificate of marriage ɗin da change of name. Tun ina sauraron naji ya ce an yi ko ga yanda ake ciki har aka kwana uku shiru be ce mun komai ba, da na sake masa magana ma da ɓacin rai yace mun ai yana sane shima jira yake yi wanda ya bawa yayi ya ce masa an gama tun da dai ba da kansa ze yi mun ba ai dole na jira. Ganin ransa ya ɓaci yasa na bar maganar, har ya rage saura kwana biyu a rufe registration be sake ce mun komai ba tun da na tuna masa wancan ranar dama ya fara wasu attitudes se kawai na rabu dashi da yamma ranar nace masa zan je gida be kuma hanani ba na tafi.
Cikin sa'a na tarar da Uncle Mudassir ƙanin Mama a gidan, ina faɗa musu abin da ya faru ya hau faɗa yana cewa da uban me na zauna yi ga waɗan da muka gama karatun tare har sun ci ƙarfin service ɗin su? Tare muka je dashi aka mun registration ɗin as single, ya karɓi details ɗin yace ze bawa wani abokin sa dake aiki a NYSC ɗin ayi mun ƙoƙari a barni a Kano. Yanda Bilal be ce mun ba nima na masa shiru se sa aka kwana uku muna zaune da dare yana danna waya ya kalle ni yace
"Wai ashe an rufe registration din NYSC, amma ɗan iskan mutumin nan be kyauta mun ba dole naje naci uwarsa gobe. Kullum na kira shi ya ce mun yau gobe gashi har an rufe beyi abun nan ba" ya wani fututtuke kamar gaske. Kallon sa kawai nayi na maida kai naci gaba da danna wayata.
Sosai naji zafin ko in kular daya gwada mun tun akan zuwa karɓan result da kuma zancen service ɗin nan yanzu. Se na tuna da wata magana da ya taɓa faɗa a gaba na tun ina diploma, lokacin da Nasir ze auri matar sa tana karatu yace ze ci gaba da ɗaukar nauyin ta. A gaba na yake cewa Nasir ɗin bashi da hankali.
"Kai ka sakata a makarantar balle ka ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ta? Ai wlh nan da ka ganni idan iyayen yarinya sun ga zasu bani auren ta tana karatu to su san duk lalurar ta tasu ce ko kuɗin fensir ba za'a ɗora mun ba tun da ba ni na sakata a makarantar ba". A lokacin kwata kwata ban nazarci maganar sa ba a rashin hankali na ma gani nayi daidai ne tun da ina jin Abba na yawan cewa ko ze mun aure se na gama makaranta dan babu dalilin da ze saka ka ɗorawa miji hidimar da bashi yayi niyyar kansa ya saka maka yar a makarantar ba. Tuna wannan abun yasa naji raina ya sake ɓaci kawai na tashi na bar masa gurin nayi kwanciya ta a ɗaki be kuma damu ba balle ya biyo ni yaji ba'a si dan dama ni ce nake kasa zaune na kasa tsaye idan ransa ya ɓaci shi kuwa ko a jikin sa duk fushin da zanyi se dai ya jira na gama hawa na sakko.
An yi posting cikin rashin sa'a aka cilla ni Bauchi, uzurin da abokin Uncle Mudassir ya bashi na cewa state of origin ɗina Kano ce kuma banyi registration da wuri ba dan haka list ɗin yan Kano ya cika da daga wata jahar ne ma ya iya cucu cuku a jefani amma yanzun ma babu damuwa registration kawai zan je nayi se a mun relocation. Sanda ya kira yana mun wannan baya nin duk se na rikice na rasa ta in da zan fara. Kwana biyu da suka wuce Bilal ya tsare ni da masifar akan me naje nayi registration a matsayin mara aure kuma ba da umarnin sa ba? Yayi rantsuwa akan muddin aka kai ni wata jahar se dai nasan yanda ze yi amma har idan da yawun sa ne ba zan je ba tun da na raina shi na fara yankewa kaina hukunci ba tare da sanin sa ba. Yanzu haka bama magana, tsaka ni na dashi kallon banza ko abinci na baya ci in ya fita tun safe se nayi bacci yake dawowa ɗazu har Hajjan su ce ta kira bin ba'asin me ya faru? Bata kuma tsaya taji uzuri ma ba ta ringa surfamun faɗa wai dama taji ƙishin ƙishin ɗin na raina shi bana jin maganar sa to wlh na shiga hankali na kuma taka a sannu idan ta juyo kai na ba zan ji da daɗi ba.
Maganganun ta suka kulle mun kai na kasa gane in da ta dosa, ni ce na raina Bilal? Kuma waye yake kai mata tsogumin? Matar da sa albarka ne tsakanin mu idan naje ko yayanta suka zo ko mukayi waya bakin ta baya gajiyawa da gode mun da yi mun addu'a ita ce zata kira tana mun wasu maganganu da ban ma gane kan su ba. Ina cikin wannan jimamin kiran Uncle Mudassir ya same ni, kai na ya sake kullewa na rasa ina zan kama. Haƙura zanyi da service ɗin nabi yanda Bilal ke so ko kuwa na barshi na bi son rai na? Ina buƙatar me bani shawara.
[1/8, 9:55 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*
*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
*Page 12*
"Idan har izini na kike nema ban yarda ba, ko da yake ai kin saba yin gaban kanki. Kiyi duk yanda kika so Halima lokacin ki ne dama kika samu". Abinda Bilal ya gaya mun kenan bayan dana same shi akan maganar posting ɗina zuwa garin Bauchi. Duk yanda kuma naso da ya zauna muyi magana ta fahimta yaƙi, ƙarshe ma barin mun part ɗin yayi gaba ɗaya ya tafi can part ɗin sa da falon kaɗai muke amfani dashi ina jin sa a daren ya gyara ɗakin tun da dama da hado da komai a ciki ya dawo ya ɗauki bedsheets da bargo ya koma can.
Kwanan mu uku bana sanin fitar sa bana sanin dawowar sa. Hankali na ya tashi matuƙa, har ƙasan raina ina jin na masa laifi kuma ya cancanci yayi fushi tunda matar sa nake ya kamata ace duk wani abu daya shafe ni yana da masaniya a ciki musamman irin wannan abun da tilas nake da buƙatar sahalewar sa. 'Amma kuma na bashi damar sa', zuciya ta ke raya mun. Daga ƙarshe dai ɓangaren da yake ganin abin da nayi ba daidai bane ya rinjayi wanda yake ganin ina kan daidai. Ranar laraba daya kama washe gari Alhamis za'a fara shiga Camp da sassafe Uncle Mudassir ya kira ni. Bayan mun gaisa yake ce mun
"Tun jiya naso na kira ki, ina ganin idan da hali ki shirya kawai ki tafi yau tun da gobe za'a buɗe camp ɗin. Kin ga idan kika kwana can zaki fi fita da wuri kije ki gama abin da zakiyi a goben ba tare da cunkoso yayi yawa ba jibi kiyi juyowar ki".
Shiru nayi, se da naji yana ta hello hello kafin na sauke ajiyar zuciya nace
"Dama tun da na gaya masa zancen tafiyar ne yake ta fushi, kuma yace in har da yawun sa ne be amince ba" na ƙarasa muryata na rawa. Se yayi shiru kusan minti ɗaya kafin ya ce mun
"Shikenan, kiyi yanda kika ga ya miki Halima" be ko saurari abin da zan sake faɗa ba ya kashe wayar sa. Duk se na sake shiga ruɗani. Na ɗauka shi da yake namiji ze fahimce ni ya kuma ƙarfafa mun da nabi umarnin miji na amma daga amsar sa na gane ransa ne ya ɓaci har ya rasa amsar bani shi yasa ya kashe wayar. Na zabga tagumi gaba ɗaya ma ƙwaƙwalwa ta ta cushe na kasa tuna ni. Na sauke tagumin jin wayata ta ɗauki ƙara na ɗago ta daga cinyata, Abba ne yake kira se naji wani rauni ya saukar mun nan da nan hawaye ya tarar mun a ido.