← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 158

Sashe 16

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Amina na zaune ta zabga tagumi tana sauraron Goggo Habi dake zuba tijara, tun yammacin jiya data sauka gidan ta ce a fito mata da kayan lefe ta gani aka ce babu shi kenan ta dasa tijara in tayi ta gaji ta huta an jima ta ci gaba, yanzu ma zuwan Inna Salamatu Yayar su Alhaji Aminu ta biyu yasa aka sake maido da zancen sabo.
"Ni tun da uwata ta haife ni ban taɓa jin labari ko ganin neman aure irin wannan ba, ni fa tun ga ni na da yaron sau ɗaya ban ga miji a nan ba yana yawo da wata shegiyar suma kamar zakaran da yake tashen balaga na ɗauka shiritar yarinta tasa ta biye masa da zarar ta samu nutsatstse me hankali zata rabu dashi ashe abu dai bana ƙare bane. Ban da ma sakaci irin naku na iyayen yanzu ke Amina kina ina har kika bari har tayi sabo da wannan lalata mogal ɗin?

Irin waɗannan samarin dama kowa yasan basu aje ba basu bawa kowa ajiya ba se dai suyi wanka su ringa yawo kwararo kwararo duk in da suka ga yarinya me ɗan gwaɓi gwaɓi su shiga jikin ta su hanata kula mazan arziƙi daga ƙarshe su gudu su barta, in kuma Allah ya ƙaddara an yi aure ayi ta tsallen tsiya ana jeka ka dawo akan me?

Tun da suka ce zasu zo neman auren me yasa baku dakatar dasu ba ku ce kun wa yar ku miji se yanzu zaki zauna kina tagumi da maganganun banza da ba zasu miki amfani ba to wlh tun wuri ki tashi tsaye ki ƙwato yar ki tun ba a kai ki an baro ba, ke Salamatu da zaki ce aure saura sati biyu mutane zasu yi surutu idan aka fasa in yar ta shiga garari uban waye ze taimaka musu balle a guji maganar da zasu yi? Allah ya tsinewa duk wanda be yi surutu ba, dama ai mugun hali irin na mutanen yau yasa suka yi shiru kaf maƙwaftan ku ace an rasa wanda ze bugi ƙirji ya faɗawa Aminun gaskiya idan duk su yan uwansa maza yan ubanci yasa sun yi shiru suna kallo yar sa zata shiga gararin rayuwa su sauran da za a haɗa auren su tare idan da haka nasu maneman suka shuka rashin arziƙi ai ba zasu ja baki su kulle ba se shi za a masa mugunta a bar shi son ya ya rufe masa ido to ba a isa ba se kuma naga uban da ze ƙulla auran nan" Goggo Habi ta faɗa.

Mama dai juya kai kawai take yi ta kasa cewa komai, tun da Anty Labiba ta kira ta ta gaya mata ta yiwa Bilal magana da kanta be ce komai ba daga nan ta ƙarasa cire ranta akan al'amarin auren sa da Halima ta kuma godewa Allah daya sa matsalar ta ɓullo daga gurin sa ko hakan ze sa Halima ta hankalta ta Kuma haƙura se dai ko da ta yiwa Abban zancen cewa yayi kar ayi saurin yanke hukunci a jira aji ta bakin su tun da akwai sauran lokaci.

"Amma Hajiya na ke ganin abi komai a sannu ya fi, shi lamarin aure sirri ne ba'a san abin da Allah ya ɓoye ba be kamata ace muyi katsalandan a ciki ba. Aure nawa akayi a cikin irin haka daga baya kuma se kiga Allah ya warware komai ya wuce kamar be faru ba balle yaron nan ba wai zauna gari banza bane yanda kike tuna ni. Da aikin sa, a gwamnatin tarayya yake aiki bama state ba kin ga ko ai yana da albashin da ze riƙe aure mace biyu ma ba ɗaya ba, shi shirin aure kowa ya sani Allah ke yi ba mutum ba duk kuɗin ka duk tana din ka se kiga abu ya zo maka ba a yanda kayi tsammani ba musamman ace aure ya taso ga gini abin duk se a hankali fatan mu dai Allah yasa haɗin ya zama alkhairi duk wani ƙyale ƙyale da bidi'a ba shi ne ba".

Kallon ta Goggo Habi tayi tsaf tace
"Lallai Salamatu dole ki ce haka, tone tone babu kyau amma da se in ce ai ba zaki ga aibun abun ba tun da irin auren da aka miki kenan da Mijin ki na Farko Haladu me kifi har yamma tayi za'a tafi kaiki ɗakin da aka bashi aro a cikin gidansu ba'a kwashe hatsin da aka ajiye a ciki ba. Haka muka raka ki aka ajiye ki a ɗakin uwar sa, ina kwananki uku Allah jiƙan rai Halima taje ta ɗakko ki aka kashe auren irin haka kike so a maimaita to ba da mu ba wallahi ba a taɓa ba ba kuma za a fara akan Halima ba"

"Haba Goggo dan Allah ki de na faɗar haka" Mama ta faɗa se ta juya kan ta kafin tayi magana Abba da Baba Salahu suka yi sallama hakan yasa tayi shiru. Sama sama ta amsa gaisuwar da suka mata dan tun jiyan tace komai daya faru laifin Abba ne shi kuma Baba Salahu ta ce yan ubanci yasa yaƙi gayawa Abban gaskiya. A tsanake Abba ya sanar musu da abin da Halima ta gaya musu ya rufe da cewa
"Da nasan ze zo da wannan maganar da ban fara rabon katin ɗaurin auren nan jiya ba. Gashi jar abokanai na na wasu garuruwan duk jiya na aika musu dan kar ya zama a ƙurarren lokaci har an fara turo mun da gudumma yanzu se dai na maida musu na bawa kowa haƙuri kenan".

"Aa wace irin magana kake yi haka ai ba cewa yayi ya fasa ba uzurin sa ya bayar be kammala gini ba, abun duk me sauƙi ne kiran sa ya kamata ayi aji ta bakin sa ko a kira su waliyyan nasa, idan lokacin ne baze ishe shi ba se a ɗaura auren a bar biki zuwa sanda ze kammala se su tare idan kuma haya ze nema duk ba wani abu bane suyi zaman su wata rana se kaga komai ya wuce kamar ba ayi ba" Inna Salamatu ta faɗa se Goggo Habi ta miƙe tana cewa

"Da ba cikin ku dayayda Aminu ba se in ce kema hassada kike masa Salamatu ko da yake dama ai duniyar nan ta lala ce kai dai kayi ta kanka kawai to in ga dan bantan uban da ze zauna dashi ko iyayen nasa maza azo a haɗa duk tsiyar da suka kawo a maida musu yanzun nan ba se an jima ba gara da akayi haka Allah ya haɗa kowa da rabon sa ma alkhairi kan ta farau fasa aure ko a kanta za'a ƙare balle ace? Maza Amina taso muje ki tattaro komai da kika san ya kawo gidan nan a fitar dashi".

Mama ta sauke tagumin data zabga tun da Abba ya fara maganar tace
"Ai babu wani abu nasu a gidan nan Goggo"
"Mantawa nayi, to bari in ɗauko hijabi na ke Salamatu ki tashi ki raka ni can gidan nasu muje mu zage su dan ba zamu bar su haka ba ladan ɓatawa jikata lokaci da yayi dan uban sa" Goggo Habi ta sake faɗa, se Abba yayi saurin cewa
"Duk abin be kai na haka ba Goggo ayi haƙuri" ta musu banza ta shige ɗaki. Daga ciki ta ƙwalawa Mama kira ta tashi ta tafi. Bayan barin su gurin Inna Salamatu ta kalli Abba tace
"Kada ka biyewa zancen Habiba kasan ta da rikici tun zamanin ƙuruciya balle yanzu da girma ya cimmata, maganar yaron nan uzuri ne babba yazo dashi tun da dai muhalli a aure yana gaba da komai. A gani na kar a biyewa shaiɗan ace za'a fasa auren nan akan wannan, arziƙi da babu duk daga Allah ne nan duk daga babun muka taso gashi yanzu ubangiji ya bawa kowa bakin rabon sa. Ni dai shawarata Aminu ku kira iyayen yaron nan kuji ta bakin su, in har ba su suka ce a bar maganar auren nan gaba ɗaya ba karku bari ace daga gefen ku matsala ta ɓullo ba".

"Amma Yaya maganar gaskiya fa lamarin nan abin dubawa ne. Yau da ace yaron nan ya nuna iya ƙoƙarin sa a sabgar nan za'a fi samun ƙwarin guiwar kyautata masa zato amma fa ki duba tun da aka fara maganar nan wane yunƙuri yayi ko iyayen sa suka yi, ko sadaka za'a basu auren yarinyar nan ai yaci su nuna yabawa amma yau har saura kwana goma sha huɗu ba kira ba aike kuma jiya fa ko jiya naga katin auren ƙanwar sa Alhaji Malam ya raba a kasuwa kuma sunan ta ita kaɗai aka buga ban da nasa" Baba Salahu ya faɗa, Abba dai be ce komai ba ya harɗe hannu biyu yana sauraron yan uwan nasa. Shi kaɗai yasan yana yin da yake ciki a zuciyar sa ga irin kukan da Halima takeyi gaba ɗaya komai ya dagule masa.

Sallama Baba Salahu ya musu yace Abba suyi magana da Mama, duk abin da suka yanke ya sanar masa, bayan fitarsa Inna Salamatu tace su je can falon sa suyi magana saboda Goggo, bayan sun nutsu tace masa
"Kar ka bari shaiɗan ya shiga zuciyarka kamar yanda ya samu guri a zukatan sauran. Ba se na tuna maka ba ka fini sanin a yanayin daka auri uwar yarin yar nan ba, idan ban manta ba se da ɗaurin auren ku ya rage saura kwana uku kafin nayi ɗaukar adashi na baka ka biya kuɗin hayar gidan da kuka fara zama. A shekara goma na farkon auran ku se da kuka zauna a gida bakwai, da daɗi babu haka Amina tayi haƙuri da kai daicdai da rana ɗaya bata gaza ba har Allah ya yanke ya kawo ku in da kuke yau, yanzu idan ba wanda ya sani ba wa za'a faɗawa irin wahalar da kuka sha a rayuwa ya yarda? Baka zaton gwaji ne ubangiji yake yi maka yaga ta yanda zaka godewa ni'imar da yayi maka. A sanda Amina ta aure ka dai dai da kayan sakawar ka irgaggu ne Aminu amma yanzu fa? Ko cewa kayi ba zaka maimaita kaya ba kana da sararin da kullum zaka saka sabo.
Chapter 16 · 0% Book details