← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 158

Sashe 146

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akwai tarin alkhairi a cikin harkar musamman idan ka shigeta da jari mai ƙarfi supply ɗaya idan kayi sai ka samu riba kusan ninkin jarin daka zuba. Tun bayan da suka gama Jami'a a lokacin yana ta fafutukar samun aiki shi kuma Yahya ya fara harkar a sannan ma kayi nayi yakeyi ya nemo kayan wa masu siya a sallame shi har ya samu jarin daya fara siya shima Allah ya saka masa albarka a abun ganin kuma ya fara fasowa gari ya saka Bilal shiga shima.

Yan kuɗin daya fara dasu ba wani na azo a gani bane amma dukda haka ba laifi idan an siyar ana samun riba dan da kuɗin ya fara ginin gidansa kafin harkar birni da ɗawainiyar Zulaiha suka sa ya dakata kafin daga ƙarshe ƙwadayinsa da son zuciya suka rabashi da Yahyan. Cewa yayi sai Yahyan ya bashi jari mai ƙarfi tunda yanzu Allah ya buɗa masa ya faso gari shi kuma ya ce sai dai ya bashi aro idan ya yarda zai ranta masa ko nawa ne amma kuma ba zai ringa karɓar riba ba har sai ya gama biyansa. Nan fa ya yi masa rashin mutunchi har yana ce masa maƙetaci, bayan duk abinda ya masa sanda suna Jami'a shine yanzu ba zai iya bashi wasu yan kuɗi ba sai dai bashi.

Ya akayi kuma ya koma yana bashi haƙuri sannan kuma ya yarda zai karɓi bashin shi kuma a lokacin Yahya ya canza shawara ya ce ya fasa ba zai bashi ba, a bashi bai shiga tsakaninsu bama ya rufe ido ya masa cin mutunchi ina kuma ga ya tambayeshi kuɗi dan haka ya fasa. Sukayi kaca kaca suka rabu.

Ya riƙe abun a ransa wata rana sai ya bawa Yahya mamaki shiyasa ya ringa tara kuɗaɗe har saida suka kai yanda yake ganin zai shiga harkar da ƙarfinsa. Bai koma ta hannun Yahyan ba sai ya nemi wani abokinsa daya san tare suke komai Yusuf, shi ya bar fitar da kaya ya koma noman shinkafa kamar yanda ya gayawa Bilal ɗin.

Shi yayi hanyar wani kamfanin a Turkiyya da suke siyan Citta da Zoɓo. Kusan wata shida kenan da aka tura kayan, yau ne gobe ne zasu isa shiru yana ta jira domin ba ƙananan kuɗi ya narka ba haka ribar da yake tsammanin samu ba yar kaɗan bace sai da Yusuf ɗin ya bashi shawara daya rage kuɗin yayi yawa ba'a zura jiki a kasuwanci musamman shi da zai fara yanzu amma yaƙi,

Yayi tunanin kayan zasu iya isa a ƙasa da wata biyu kamar yanda aka ce masa da zarar kuma an sauke zasu bashi kuɗinsa cas haɗama ta saka bai dubi za'a iya samun akasi wata matsala ta faru ba ya tattar kuɗaɗe kawai ya narka sai gashi an tafi rabin shekara shiru kaya na kan ruwa sai a cikin satin daya mutu aka ce kaya sun isa amma ba'a sauke su ba.

Yanzu zaman da zaiyi a nan na jiran a sauke kaya ne su tura masa kuɗinsa ya biya Alhaji Lawan ya samu yanci ya warwasa ya taka duk wanda yaga dama. Neman shiri da Halima kuma da yakeyi saboda ko da ace an samu akasi an ja lokaci har asirinsa ya tonu an gano maɓoyarsa a ƙalla ya samu wanda zai tsaya masa dan ya tabbatar duk fuffukar da Abba yakeyi sai dai idan Haliman bata birkice masa ba sai yayi mata abinda take so.

BAYAN SATI ƊAYA
Hajja na zaune tsakar gida ita da Anty Amina da Anty Habiba, kiransu tayi kamar yanda tace tun ranar Juma'a rabon da taji daga pBilal da Fadila. Bilal bai ko shiga gidan ba gurin ɗaurin aure an ce mata ya hau mota ya wuce ita kuma Fadila washe gari da tayi aike a kdagai mata wasu saƙo data sa aka karɓo mata aka tarar gidan a rufe, ta kirata kuma suna fara magana tace tana zuwa zata kirata toh fa har yau kwana bakwai kenan idan an kira layin nata ma a kashe kuma cikin ikon Allah su duka babu mai number angon balle a kira aji ko lafiya.

Anty Habiba tace
"Nima nayi ta kira bana samunta, zuwansu Hajar biyu kuma gidan a rufe amma kuma da alama akwai mutane a ciki dan sunce rariyar gidan da ruwa, abinda ya sa hankali na bai tashi ba ai lafiya itace take ɓuya. Kuma dama tace ya gaya mata idan ta tare sai sunyi sati biyu kafin su fara buɗe gida dan baya so mutane su damesu su hanshi cin amarci".

Hajja ta janye tagumi tace
"To dai ko bunsuru ne shi dai ai ba zai kwana ya wuni yana abu ɗaya ba dole za'a tsaya a huta a ci abinci a lokacin hutun kuma a kunna waya ai a gaisa da yan uwa kowa ya san halin da ake ciki, kuma shi baya sallah ne? Ko kuwa sallar ma a cikin gida yake yinta da ba zai buɗe ƙofa ba?"

"Ni yanzu ya za'a yi na sani Hajja?" Habiba ta faɗa. Anty Amina sai dai ta kalli bakin duk wanda yayi magana bata ce musu kanzil ba, Hajja ta sake cewa

"To shi kuma Bilal ɗin fa? Ko da yake dama shima tunda ya auro wannan tsinanniyar yarinyar sai ya shafe satin ma bai zo ba bai kuma kirani ba nima ɗorawa kai ne ya saka na damu da shirun nasa na manta ya saba dama. Ita Fadilar dai nafi damuwa gaskiya dan haka ƙalau na san ba zata ki kiran waya ba ni dai jikina yana bani akwai wani abu, dan haka yanzu abinda nake so dake da Amina ku tashi kuje gidan ku gano da kanku, zancen yayan nan naki masu azabar ƙarya ba abin kamawa bane. Ku tambaya har maƙwafta kuji ai in dai da mutane gidan ba za'a rasa jin motsi ba".

Haka suka kama hanya a motar Anty Aminan, Anty Habiba ce ta kwatanta mata dan ita bata je kai Amarya ba dare nayi ta kaɗa yayanta masu aure suka wuce gidajensu ta kwashi sauran suka tafi gida. Cikin sa'a suna isa suka tarar da get a buɗe za'a fito da mota, Anty Habiba tace

"Ahaf, ai na faɗa suna nan ga angon nan, tsiyarsu suke shukawa kawai shiyasa suka kulle gida amma Hajja duk tabi ta damu kanta". Gefe sukayi parking sai da ya fito da motar ya sauka zai kulle get kafin suka fita, tsayawa yayi yana kallonsu sama da ƙasa, Anty Habiba ta washe baki ta shiga gaishe shi, yanda ya amsa yana ƙare musu kallo ya saka Anty Amina cewa

"Yayyen Fadila ne, baka gane mu ba ko?"
Ba yabo ba fallasa ya ce
"Ayya ban gane ku ba wlh, toh ya akayi?"

Daga Anty Habiba dake murmushi kamar sokuwa har Anty Aminan buɗe ido sukayi suna kallonsa da mamaki, cikin dakewa Amina tace
"Ban fahimci ya akayi ba? baka ji abinda nace maka bane mu yayintane ko kuwa ba zamu zo gidan ƙanwarmu ba sai da dalili?"

Kwarjini tayi masa dan haka ya matsa yana cewa
"Bismillah" tayi tsaki ta wuce Habiba tabi bayanta tana waigen Ahlan daya zaro waya daga aljihunsa yana dannawa. Anya kuwa shi ɗin ne saurayin Fadila da kamar zai kwanta mata tsabar biyayya idan yaje zance Fadilan na gidan? Kofa a kujera baya zama idan zasu gaisa ƙasa yake sauka amma shine yau yake cewa bai ganeta ba lallai akwai ƙatuwar matsala toh.

Ƙwanƙwasa ƙofar falon Anty Amina ta shiga yi a fusace a ranta kuma tana ayyana dama ta san za'ayi haka, amma kuma Tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa zai doka. Yanda ta buɗe ƙofar zaka san a tsorace take, su biyun suka zuba mata ido cike da son tabbatar da Fadilan ce ko kuwa wata mai kama da itace aka samu.

Cikin yanayin tsoro da kuma murna a haɗe ta ƙaƙalo murmushi ta shiga kiran sunansu tana cewa
"Kune? Ku shigo mana" ta juya ciki suka bi bayanta. Ga dai gida har gida, falonta tamkar na wani babban attajiri ko ɗan siyasa amma a kallo ɗaya zaka fahimci matar gidan tayi hannun riga da kwanciyar hankali. Zama sukayi suna kallon Fadilan dake ta murmushin yaƙe tana musu sannu da zuwa kafin ta zauna a shiga gaishe su cikin ladabin da basu san yaushe ta koyeshi ba.

Sukayi jugum jugum bayan gaisuwar, Anty Amina na ƙare mata kallo tana karantar canzawar da tayi a cikin sati ɗaya, rama har a fuska Fadila dake da cikakken jiki dukda bata da kiɓa amma jikinta irin me luf-luf ɗin nan ne haka fuskarta cike take da kumatu musamman dab da bikin kayan matan data ringa sha suka sake cikata amma a sati duk ta zaizaye sai kace wacce tayi amai da gudawa, ga dai haske tayi irin na mai zama guri ɗaya musamman kuma ga Ac amma fa duk tsokar data zo da ita a jikinta t zaizaye.

Ta sauke ajiyar zuciya jin Anty Habiba data gama ƙarewa falon kallo na tambayar ruwan sha, sai ta miƙe da sauri tana cewa
"Kuyi haƙuri, murnar ganinku ta saka ma manta" ta wuce kitchen ba jimawa ta dawo da ruwan faro ƙwara biyu akan try sai kofuna suma biyu ta ajiye musu.

"Yanzu idan baƙin kunya ne suka ce ki basu ruwa haka kuwa zaki dakko tsurar ruwan ki basu Fadila sai kace wacce taba jin hausa?" Anty Habiba ta faɗa, kafin ta bata amsa Anty Amina tayi saurin katseta da cewa

"Dama Hajja ce tace kwana biyu ta jiki shiru ko a waya shine tace muzo mu duba mata ke, tunda kuma kina lafiya shikenan mu zamu wuce" ta miƙe, yanda kasan a ƙaya Fadilan take itama ta miƙe tana cewa

"Ai wayar ce ta faɗa ruwa amma zan kirata nagode ku gaida gida". Habiba zata sake magana dan abin ya ɗaure mata kai Anty Amina ta katseta, ganin kuma Ahlan ɗin ya fito daga kitchen dukda basu san sanda ya shigo ba ya saka tayi shiru suka tashi suka fita tana musu Allah ya kiyaye daga inda take tsaye bata ko ƙara taku ɗaya ba.
Chapter 146 · 0% Book details