← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 158

Sashe 53

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dama ai son zuciya da kwaɗayin abin da Abban ze masa ne ya saka ya yi masa takwarar ba wai saboda cancanta ya yi ba. Bilal kuma, ai se dai ya cuci wanda be san shi ba wlh amma ni nan kar na ke kallon su" Cewar Anty Labiba bayan Mama ta dawo falon. Mu'azzam yayi dariya ya ce
"Wlh kin gano shi Anty. Tsabar son zuciya ne kawai. Ban da haka ina nasa uban ya mutu? Ba se ya yi masa takwarar ba ko mun ce masa muna so ne?"

"Ai dai zan ga abin da Bilal ze yi ya muku gwanin ta kai da Labiba, ka tashi kaje gidan Hajiya Larai ka amso mun saƙon da ka ce se yau zaka je, ke kuma muje ciki ki duba kayan se muga abin da ya kamata a ƙara. Yau na cewa yan gidan su Abban su su zo su gani idan ya so go be kwana biyar se aje a kai musu ko?" Cewar Mama. Labiba ta taɓe baki ta ce
"Ba dai zaki haƙura da wannan al'adar ɗaukar maganar ba? Meye wani abin zuwa a gani a kayan barka se kace lefe? Kuma da zaki gayya to su suzo kai kayan kin dai san can gidan su Bilal bana zaton ko ƙyalle sun tana da da zasu gabatar a matsayin kayan da suka yiwa yaron nan. So kike a maimaita ta lefe ko a sake samun abun da za'a yi ta terere dashi a dangi, ai shikenan".

"Toh Labiba ya kike so na yi? Kin dai san haka suke al'adar su, yanzu idan ba'a kira su ba se ki ji ya zama abin magana" Maman ta faɗa. Labiban bata sake ce mata komai ba ta wuce ɗakin da suka ajiye siyayyar kayan barkar da suka yi ta shiga fito dasu. Cikin akwati set me uku da kit ɗin sa ta shiga shirya kayan. Kaya masu kyau da tsadar gaske suka siya. Kusan duk wani abu da za'a buƙata na jego sun siya mata, har da set ɗin feeding bottle da bath set komi basu manta ba duk da ana siya Anty Labiba na mitar mijin ta ya kamata ya siya mata amma kuma itan ce me sake zaƙulo wasu abubuwan a siya har da gado ta basu na minal ɗin ta a pre order ta siye shi kafin yazo har yarinyar ta fara tafiya se kawai ta ajiye shi yanzu kuma ya zama rabon su Halima.

Mama dai na tsaye tana kallon ta har ta gama jera na yaron a babbar akwati da ta uku kafin ta shiga zuba na Halima a ta biyun wanda duk an ɗinka su. Kala shida ne Atamfa uku lace biyu da shadda ɗaya se mayafi harda takalmi da jaka set bibbiyu. Sauran tarkacen undies har da body sprays da body mist duk ta zuba a kit ɗin, ta tayar da su tsaye kafin ta kalli Mama tace
"Tsakani da Allah ko mu muka mata cikin iya waɗannan kayan sun isa".

Mama tayi murmushi kawai tana kallon ta, Labiba akwai daru. Ƙarara take adawa da lamarin Bilal da Halima amma yanda ta zage ta kashe kuɗi a sabgar auren Halima zuwa haihuwar ta ba zaka yarda bata son auren ba.
Kuɗin da Abba ya bata ta ciro daga aljihun rigar jikin ta ta shiga ware su, ta miƙawa Mama wani kaso ta ce
"Gashi nan ki rage asara wannan kuma zan haɗa akwai kuɗin ta tun na barkonon da muka taɓa siya zan haɗa su na siya mata sarƙa ta samu ta fitar suna". Mama na dariya wai ta rage asara ta karɓi kuɗin tana juya su tace

"Da kika ce ba zaku yi taro ba"
"To ko babu taro ai dai zatayi kwalliya na san kuma yan uwan sa ba zasu ƙi zuwa ba ƙila su zasu yi sunan; Allah dai ya kaimu gobe muga zubin su, ko zasu mata ƙauri ma oho" cewar Anty Labiba. Sai Mama ta bata amsa da cewa

"Ke ma da neman magana kike Labiba, cewa fa tayi har account ɗin sa sun yashe komai waɗanda suka ƙwace masa waya. Idan ya samu sararin yin haƙiƙa ma ai yayi"

"Idan ma ƙarya ya ke Allah ya biya bakin sa ya sa a kwashe ɗin" Anty Labiba ta faɗa daga nan ta zura Hijabin ra tayi wa Mama sallama akan zata je kasuwar rimi ta dawo.

*******************
Cike da walwala na ƙare yinin ranar ban da ma zuwan Hajja da ta so ta ɓata mana farin cikin mu amma ban bari maganganun ta sunyi tasiri a raina ba. Dab da la'asar Abba tare da Baba Salahu da Baba Munzali suka zo duba Bilal, tun aure na zuwan Abba na farko kenan gida na. Na ji kunya ta yanda ko ruwan robar da zan basu babu a gidan balle a je ga lemo ko wani abu se pure water na juye musu a Jug duk su ukun ma babu wanda ya sha basu jima ba kuma suma tafi.

Basu jima da tafiya ba Hajja ta zo tare wasu ƙawayen ta da suka zo dubiya da kuma barka. Ina ɗaki ina shiryawa dan gama wanka na kenan Abba na kuma yana hannun Bilal yana masa wasa dan shi Anty Amina ta fara yi wa wankan kafin tayi mun.

"Wato kinga gurin zama har da kafa murhu" Hajja ta faɗa bayan da na fito ba tare da ta ko amsa gaisuwar da nake musu ba. Lanti, ƙawar ta ta ce
"Zancen da na ke yi a raina kenan na ce ita haihuwar farin ma ba zata tafi gida tayi wanka ba?"
"Ke ko jaraba irin ta yayan zamani mana. Nan na ke gaya miki jikar Saude ba yanda uwar ba tayi akan ta tafi gida tayi wanka ba taƙi wai da wa zata bar mijin ta? Na ce Allah ya yafe mana mu da zamanin mu ake arba'in biyu" ɗayar ƙawar ta ta da ban san ta ba ta faɗa. Shikenan ta samu fili ta fara zazzaga har tana cewa tsabar mugun ta tasa naƙi tafiya.

"Duk ibtila'in daya faɗawa yaron nan amma saboda rashin tausayi ace ki zauna ki yi jego a gidan nan; ai se ki zauna kici uwar da zaki ci" take ta maimaitawa. Ni se ta bani dariya ma na koma ɗaki na barsu ina jiyo Bilal na mata magana akan ta yi shiru amma se ƙara volume ta ke Lanti tana taya ta. To wace uwa kuwa zanci wadda ban saba ci ba? Tun ma da na dawo ɗin me Bilal ɗin ya yi mun da har zata ce ba'a jin tausayin sa? Ni yanda yayi mirsisi be tambaye ni in da aka samo kayan da ake sakawa yaron ba ma shi ya fi bani mamaki tun da dai dubu goma ce ta gifta tsakani na dashi akan sabgar haihuwa haka ko da wasa be yi zancen asibiti ba balle ya tambayi waye ya biya kuɗin.

Basu jima sosai ba suka tafi, ina ɗakin Anty Amina ta leƙo ta ce mun zasu tafi itama zata bi su taje gida ta dawo, a da ina ganin kamar tafi kowa zafi cikin yan gidan su Bilal amma a yanzu kam na tabbata duk ta fisu kirki domin tayi mun abun da ko jini na ce iya kaci kenan. Daga bakin ƙofa nayi musu sallama na koma ciki, se da na ji Bilal na kira na kafin na fita na koma falon.

"Ki bani aron wayar ki zan yi kira" ya faɗa se na koma ɗaki na ɗakko masa wayar na bashi sannan ya ce na ɗakko masa wani littafi a can ɗakin sa. Numbobin abokanan sa waɗan da ya rubuta ya ringa sakawa yana kira ya sanar musu da an masa haihuwa. Hafiz ya kira a ƙarshe bayan sun gama magana ya bani muka gaisa yayi mun barka tare da ƙorafin me yasa ban kira Matar sa na gaya mata ba? Haƙuri kawai na bashi kafin na mayar wa da Bilal wayar na tashi saboda Abba na daya fara ƙananan kuka.

"Kin ji me oga Hafiz yake cewa?" Bilal ya faɗa bayan daya gama bige bigen wayar, na girgiza masa kai ya yi yar dariya ya ce
"Wai amma shi za'a yi wa takwara".
"Se kace masa me?" Na faɗa ina kallon sa tare da tuno maganganun da suka yi,
"Nace masa Dady aka saka, kin san surname ɗin ku ɗaya. Baki ji yanda ya ringa murna ba ina ga ma yau zasu zo duk da yace suna Abuja ama jirgin 6 zasu biyo zuwa Kano dama".

Kallon sa kawai na ringa yi, yanzu shi Hafiz ɗin idan ba soko ba ne da ze yarda a wace dangantakar Bilal ze yi masa takwara balle har ya saka sunan mahaifin sa ma?
"Kin san ya so ya sakawa yaron sa sunan Dadyn ne amma matar ta ce sunan mahaifin ta za'a saka shi yasa yaji daɗi sosai yanzu dana ce masa sunan Dadyn na saka" Bilal ya sake faɗa yana ruƙo hannu na.

Duk yan da na so na ci gaba da murmushin da nake yi amma na kasa, ina ɗaki ɗazun na tsinci maganar Hajja sanda take Lanti take tambayar sunan yaron ta ce mata Aminu, ina ji ta ce "lallai, baban ta aka wa takwara kenan?" Ita kuma Hajjan ta ce mata
"Baban uban gidan sa dai". Dake nesa nake jiyo maganar se na ji kamar ta ce "Babban ubangidan sa" har ina dariya na ce wato Abban ne kuma ya zama uban gidan Bilal ashe Baban ubangidan sa ta ce.
Chapter 53 · 0% Book details