← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 158

Sashe 84

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan Allah Hajiya ki nutsu, idan ba zaki iya shiru ba kuma ki fita waje. An gaya miki babu abinda ya sameta kawai tana buƙatar lokaci ne babu yanda za'ayi mutum ya tashi daga dogon suma irin haka kiyi tsammanin nan take tunanin sa zai dawo tamkar yanda yake a da sannan wannan hayaniyar da kukan da kikeyi shima kina ƙara mata wata damuwar ne cikin wadda take" ɗaya ɗaga cikin Nurses ɗin ta faɗa a hasale, sai ta juya cikin kuka ta nufi ƙofa na bita da kallo ina so in tsayar da ita amma kuma banida ikon yin hakan.

Wata yar fitila likitan ya kunna ya shiga haska idanuwana bayan ya gama ya zaro biro daga aljihun rigarsa yace
"Idan kina jina ina so ki ringa bin biron nan da idonki duk inda nayi dashi kinji?" Na lumshe idona kafin na buɗe nayi abinda ya ce. Ya mayar da biron aljihu yana cewa

"Yawwa Halima, yanzu ki motsa ƙafar ki na gani" nayi yanda yace sannan ya kama hannuna yace in matsa hannun sa nan ma nayi sannan ya sakeni, cewa yayi na tashi na zauna. Nayi jimm dan kwata kwata banajin alamar ƙashi ko tsoka a jikina ji nake tamkar a iska nace, sai da ya sake maimaitawa kafin na yunƙura a hankali naja jikina Nurse tayi saurin saka mun pillow a bayana na jingina ina mayar da numfashi tamkar wadda tayi tseren gudu. Hamdala yayi kafin ya karɓi folder dake hannun Nurse yayi rubutu ya bata yace taje pharmacy ta karɓo abinda ya rubuta sannan idan ta fita ta turo masa Mama.

Tare suka shigo da Abba, Mu'azzam, Anty Labiba da Mijinta sai Mama Fauziyya. Gaba ɗayan su kallo ɗaya zaka musu ka karanci hashin hankalin da suke ciki, Abba ya matso ya dafa kaina nayi karfin halin tattaro kalmomi na haɗa na kira sunansa, "Abba" ya amsa yana shafa kaina
"Na'am Halimana kin tashi?" Sai na gyaɗa masa kai lokaci ɗaya kuka ya kwace mun Abba ya rungume ni yana cewa

"Kuka kuma Halima menene? Kiyi shiru dan Allah kinga halin da kike ciki babu abinda zai faru ki dena kuka kinji?"

"Ina ganin kuyi haƙuri ku koma waje ƙila ganinku ne ya dawo mata da wani abun kuma a yanayin da take ciki yanzu bama son duk wani abu da zai sosa mata rai balle ya sake ƙara mata wata damuwar" likita ya faɗa. Duka suka fita banda Abba dake rungume dani idanuwansa sunyi jajir tamkar shima zai yi kukan yana ta bubbuga bayana da cewa nayi shiru, Nurse ɗin da Dr ya aika ta dawo da allurai da da drip ya karɓa ya fara haɗawa, zai zare ruwan dake hannuna Abba ya dakatar dashi yace

"Dan Allah kada ka saka mata abinda zai sake mayar da ita wannan baccin"
"Amma Alhaji saboda lafiyarta ne" cewar Dr, sai Abba ya girgiza masa kai yace
"Na sani amma ka ɗanyi haƙuri ku bamu guri zanyi magana da ita". Tsayawa yayi kamar ba zai fita ba kafin ya juya, Nurse ɗin da ta yiwa Mama magana ɗazun ta buɗe baki zata sake magana yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa su fita.

Sai sa suka rufo ƙofar kafin Abba ya ɗago kaina daga kafaɗar sa yace
"Kukan ya isa haka Halima kiyi shiru kinji"
"Tsoro nakeji Abba" na faɗa daƙyar kafin na kama hannunsa na ɗora saitin zuciyata da nakejin ciwo tamkar an hura mun wuta nace
"Zuciyata zafi takeyi Abba mutuwa zanyi"

"Ba zaki mutu ba Halima har sai lokacin da ubangiji ya rubuta faruwar hakan, duk wani tsanani a rayuwa yana tareda sauƙi kiyita nanata Hasbunallahu wani'imal wakeel a zuciyarki in sha Allahu zaki samu salama kinji?"
Kai na ɗaga masa alamar naji take kuma na kama na shiga nanata Hasbunallahu a hankali a hankali na fara jin abinda ya tokare mun maƙoshi yana zagwanyewa, zafin da zuciyata take mun ma ya fara raguwa inayi Abba ma na biyawa a fili sannu sannu har bacci ya ɗauke ni. Ajiyar zuciya ya sauke ganin nayi bacci, sai da ya ɗauke ƙwallar data zubo masa kafin ya gyara mun kwanciya akan gadon ya lulluɓa mun bargo sannan ya koma kan kujerar dake gaban gadon ya zauna yana kallona.

Har ya sauka Lagos zuciyarsa babu daɗi gaba ɗaya hankalin sa na ga son sanin dalilin zuwan Halima gida da sassafe haka da kuma yanayin daya ganta a ciki. Yana so ya kira Mama yaji ko ta faɗa mata wani abu amma kuma baya son yaji abinda zai ɗaga masa hankali ya hanshi nutsuwar yin abinda zajeyi Lagos ɗin. Da zai shiga meeting ya saka wayarsa a Flight mood dan haka sai bayan Magriba lokacin sun tashi gaba ɗaya ya shiga hotel room ɗin sa kafin ya buɗe wayar yana so ya kira wani Abokinsa, Network na daidaita kuma saƙon Mama ya faɗo tana gaya masa Halina na Asibiti sun sameta a sume a ɗaki har lokacin kuma dukda bai san ƙarfe nawa ta tura saƙon ba bata farka ba kuma likita yaƙi ce musu komai yace dashi zai yi magana.

Cikin tsananin tashin hankali ya shiga neman layin Maman amma bai samu ba dan haka ya mayar da akalar kiran kan Mu'azzam wanda bugu ɗaya ya ɗauka kuma yanda ya jishi da bayanin da ya masa akan yanayin Haliman ya saka yaji ba zai iya ƙara koda awa ɗaya a Lagos ɗin ba duk kuwa da bai kammala uzurin da yaje yi ba, sai dai yayi rashin sa'ar rasa jirgi, haka ya kwana a zaune tamkar yanda suma a Kano suka kwana cikin tashin hankali da zullumin halin da Halima take ciki da gari ya waye kuwa ko wanka bai tsaya yiba ya hawo jirgi ya taho musamman yanda Mama ta kira tana rusa masa kuka akan yayiwa likita magana ita dai ayi mata bayanin halin da yarta take ciki idan ma mutuwa tayi a gaya mata kawai saboda tunda aka kawota take nan kwance kan gado bata motsa ba gara ta sani in mutuwa tayi ta ɗauki dangana a basu gawarta su wuce gida su mata sutura.

Koda yazo ma babu wani gamsasshen bayani daya samu daga bakin likitan, abinda ya gaya masa kawai zuciyar Haliman ta kumbura kuma jininta yayi hau sosai wanda yayi sanadiyyar samun partial stroke da tayi sannan ta shiga doguwar suma. Shi dai Abba daya gama sauraronsa saida ya kwashi kusan minti goma a zaune kafin ya iya buɗe baki yayi magana tsabar yanda ya shiga shock, suna raye a duniya wace irin damuwa ce haka Halima take da ita da har take barazana ga rayuwarta amma basu sani ba?

Dr ne ya ringa kwantar masa da hankalin ganin yanda jikin sa yayi laƙwas ya kasa cewa komai sai ajiyar numfashi kawai yakeyi. Haka nan ya shanye maganar a cikin sa duk yanda Mama ta ringa nacin ya faɗa mata yanda sukayi da likitan amma yace mata babu komai, ta kaɗa ta raya tayi kukan duk a banza yaƙi faɗa mata domin ya san damuwar da take ciki a yanzu kaɗan ce akan ya sanar mata da ainihin halin da Haliman take ciki.

Buɗe ƙofar da akayi ya sake ya dawo daga dogon tunanin daya tafi, Alh Saleh mijin Anty Labiba ya tsaya daga bakin ƙofar yana cewa
"Dan Allah Alhaji kazo kayi mata magana ko kai zata saurareka" sai ya miƙe yana cewa
"Wacece"
"Labiba mana, gata nan wai gidansu Mijin Halima zata tafi" ya bashi amsa jin haka ya saka Abba ya fita da sauri dan dama tunda ya dawo ya tarar da rigimar Anty Labiba taje har can gidan Bilal bata same shi ba ranar da aka kai Haliman asibiti taji ba'asin me yayi mata shine yanzun ma ta tada bala'i kamar zata hau iskokai Mama da Mama Fauziyya na riƙeta tana fizgewa wai gidansu Bilal zata tafi idan ma bata same shi ba sai ta saka an ɗaure Hajja ai dole ya fito duk ma inda ya shiga ya musu bayanin abinda yayiwa Halima.

Tsawa Abba ya daka mata ganin yanda ake riƙeta tana fizgewa duk ta tara mutane sun tsaya suna kallonsu, ta fashe da kuka tace
"Na rantse da girman Allah bai isa ya kasheta yaci banza ba har in wani abu ya samu Halima wlh sai na ɗaukar mata fansa akansa". Cikin faɗa Abba yace

"Bana son shashanci Labiba da girman ki zaki ringa abu kamar wata ƙaramar yarinya shikenan Allah ba zai jarabci bawa da lalura ba sai wani ya zama sila? Kada na sake ji, ku tashi ma ku wuce gida kawai tunda hayaniya zaki tayarwa da mutane". Haka ya tattarasu duka da sauran yan dubiyar da suka zo dukda babu wanda ake bari yana ganinta bayan su amma dangi kamar masu jira ana cewa bata da lafiya suke ta tururuwar zuwa dubiya, gashi dai babu wanda ya san takamaiman abinda yake damunta haka nan duk wanda yazo ya tafi zai haɗa nasa kalar labarin da ciwon da zai ɗora mata, amma dai maganar data fi ƙarfi ta kuma fi shahara a gari ita ce Guba ta ci saboda Bilal zai ƙara aure kamar yanda wacce ta fara kai labari Galadanci can gidan kakannita tace daga majiya mai ƙarfi ta samo bayanin gurin ɗaya daga cikin ƙannen Bilal.

BILAL

Bayan daya sauke su kai tsaye gidan Hajja ya nufa, tuƙi kawai yake amma bashi da nutsuwa a tattare dashi. Tsakanin sa Allah tun waccen ranar da Halima ta bankaɗo sirrinsa yake jinsa tamkar tsirara yake yawo, kamar kowa ma yasan abinda yake aikatawa a ɓoye. Koda da yake nuna tamkar komai ba komai bane kawai yana yi ne saboda ya ceci kansa amma shi kaɗai yasan kalar kunya da nadamar da yake ciki a yanzu. Tsautsayi da ƙaddara ya saka koda ya lura ya bar wayarsa a gida bai koma ya ɗakko ba saboda yasan Halima bata da ɗabi'ar bibiyar masa waya ko lokacin da baya saka password babu ruwanta da wayar sa balle yanzu daya kulleta ya kuma san babu ta yanda za'ayi ta iya buɗewa koda ace ma tayi niyyar hakan.
Chapter 84 · 0% Book details