← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 158

Sashe 107

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gaskiya ƙarya kakeyi, Halimar dana sani b zata zageka ba balle har ta kama ka da kokawa" ta sake faɗa, ya marairaice fuska ya ce

"Amma Anty kin san dai ƙarya ba hali na bace kuma ke macece akan lamarin kishi kin san ba abinda ba zaku iya yi ba. Ni kaina wlh idan wani ya ce mun Halima zata aikata hakan zan ƙaryata amma ya faru na san kuma ba lallai duk wanda zan faɗawa ya yarda ba shiyasa kawai nayi shiru na bar maganar ina so mu sasanta a tsakaninmu amma kuma hakan yana nema ya faskara. Wlh ina son matata kuma ni bana so ace Zulaiha ta tare bata nan balle hakan ya buɗe hanyar da zata fara rainata shiyasa ma nayi shiru ko Nasir ban faɗawa ba balle maganar ta fita har taje kunnen yan uwan Zulaihan".

Hararar sa Anty Amina tayi ta ce
"Na nawa kuma? Kaf dangi da yan unguwa wanene bai san bata gidanka ba?"

"Ai dai su can basu sani ba" ya bata amsa, kafin tayi magana ya ruƙo hannunta ya sake cewa
"Na san ina da laifuka a gurinta amma yanzu a shirye nake da na gyara komai ba iya alaƙata da Halima ba da kowa ma duk wasu kuskure nawa ina so na gyarasu amma dawowarta rayuwata shi zai jagoranci komai dan Allah Anty ki taimaka mun".

Yanda yayi sai da ta ji zuciyarta ta sosu amma ta dake bata nuna masa ba ta ce
"Ni dai na gaya maka ba zan shiga ba dan yarinyar nan na ganin mutunchi na haka kawai ban ma san gaskiya ka faɗa ko ƙarya ba a xe ma gaskiya ne in shiga ta haƙura ta dawo ka cigaba daga inda ka tsaya ai kaga nima ka mayar da ni mutuniyar banza a idonta"

"Yanzu baki yarda nayi nadama dagaske ba?" Ya faɗa kamar zai fasa kuka. Tayi gajeran tsaki ta ce

"Zan maka abu ɗaya, zan kira Yaya Aminu na faɗa masa, ko zata dawo gara ayi komai da shaidu ta yanda ko ka cigaba da halinka ka san shi ba sa'an wasan ka bane".

"Yanzu ba zamu iya sirri tsakaninmu ba sai an sako wani a ciki?" Ya faɗa ta ce

"Shi Yaya Aminun ne wani? Lallai baka canza ba Bilal yaudara ta kawai kake so kayi"

"Haba kin san ba haka nake nufi ba kawai ina tunanin Hajja ne idan ta ji kin san dai ta hana saka su cikin sabgogin mu" ya sake faɗa. Taso masa tayi da masifa ta ce

"Fitar mun daga mota mutumin banza kawai, dama na san ba zaka taɓa canzawa ba. To ai sai kaje Hajjan ta dawo maka da Halimar kar ka sake sakoni a shirmenka wlh tunda ba zakayi hankali ba". Duk yanda ya so ya shawo kanta ta ƙi sauraro, fata fata ta masa ya fita daga motar kamar zai fashe da kuka ya samu gefen titi ya zauna ya dafe kai. Yafi minti ashirin a gurin yana jin wayarsa nata ringing amma bai ɗaga ba sai da ya gaji ya zama kafin ya tashi ya tare Adaidaita ya wuce.

Hankalin sa ya ɗan kwanta da yaga duk missed calls ɗin Hajja ne da na Zulaiha Jalilah bata kira shi ba, sai da ya siyo mata abincin kafin ya wuce gida ya tarar da ita a falo da kayanta cikin shiri tana waya sai da ta gama fuska a sake ta kalle shi ta ce

"Yanzu Abdul ya kirani ƙarfe uku zamu tashi"
"Ƙarfe uku kuma?" Ya faɗa yana zaro wayarsa da kira ya shigo, ta ɗauki takeaway ɗin ta buɗe tana cewa

"Haka ya ce, zaka ajiye ni ko na yi order bolt?"

Ɗaki ya shiga bayan da ya ce zai kaita airport ɗin duk ya sha jinin jikinsa a ransa ya ringa raya anya ba wani sharrin ta sake ƙulla masa ba yanda ta ware tamkar babua abinda ya faru ɗazu.

Yanda ka san wanda ya ɗakko gawa haka ya ringa zare ido yana haɗa zufa sanda suka fita sai da ya hau babban titi kafin hankalinsa ya ɗan kwanta. Bai zauna ba yana sauketa ya wuce dan suna hanya yaji tana waya da Hafiz akan zasu haɗu a airport ɗin dan haka a parking lot suka rabu itama kuma bata matsa da ya tsaya ɗin ba sukayi sallama ta shige.

Sai lokacin ya ji kamar an zare masa ƙaya a maƙoshi, guri ya samu ya tsaya yayi wa Zulaiha transfer na sauran kuɗin da ya mata alƙawari dan ta masa kira ya fi ashirin daga sanda ya kunna wayarsa zuwa yanzu wayar da sukayi ɗazu ma cikin fushi take har tana cewa idan ya san ba zai bata ba ya faɗa mata ta cire rai ba wai ya ringa raina mata wayau ba.

Halin da yake ciki ya saka bai mayar da hankali akan maganar tata ba, jiya jiya fa ya bata 2m amma ko 24hrs ba'a yi ba ta addabe shi da waya akan cikon kuɗi.

Shi yanzu lamarin Halima ne ya tsaya masa a rai sam ya kasa samun ƙwarin guiwar kiranta balle ya taka ya bita to mai zai ce mata? Duk wata ƙarya da zaiyi dan ya kare kansa na zai fita ba da ace ita kaɗai ce ma da sauƙi ƙila ya iya manipulating nata amma yanzu wannan shegen ƙanin nata da dama can ba ƙaunar sa yakeyi ba shi kaɗai ya isa ya lalata komai.

Gashi Anty Aminar da yayi tunanin zata iya taimaka masa itama ta botsare, tada motar yayi ya nufi gidan Nasir. Yayi mamakin yanda ko da wasa bai masa zancen Halima ba dukda ya san Nasir ɗin yana sane da basa tare amma bai san dalilin da ya saka ya masa shiru ba.

Sunyi saɓani dan yana zuwa matarsa tace yanzun nan shi kuma ya fita ya kira wayarsa bata shiga ba dole ya tafi a ransa yana raya Nasir ɗin ne kaɗai yake jin zai iya gayawa gaskiyar abinda ya faru dan ya san zai rufa masa asiri. Wata zuciyar ta ce ya gayawa Hafiz mana,

Halima na ganin girmansa ya san idan ya saka baki zata haƙura amma kuma ko giyar wake ya sha ba zai taɓa faɗawa Hafiz gaskiyar abinda ya haɗa su ba; ko da ace ba da Jalilah bane domin a duk sanda zasu zauna lokuta ɗai ɗai ne baya tunasar dashi akan duk rintsi kada ya yarda shaiɗan ya kwaɗaita masa biye biyen mata har ya kan ji kamar Hafiz ɗin na da masaniya akan alaƙar sa da Jalilah.

Yanzu mai zai ce masa ya haɗa shi da Halima ya yarda? Dan dai ya san duk ƙaryar da zai masa zai gane gaskiya ce kaɗai zata ƙwace shi a hannun Hafiz ɗin.

Haka ya ƙarar da yinin ranar daga nan yayi can kansa cike da tunanin ta ina zai fara tunkarar Halima? Suna ƙare magana da Jalilah bayan sun sauka take yayi blocking nata a duk wata hanya da zata iya samun sa ya kuma saka duka numbobinta a blacklist. Ya gama da shafinta ya haƙura da zancen shago da kayan da zata zuba, tunda takardun gurin suna hannun sa hakan ma ya ishe shi zai siyar da gurin kamar yanda ya siyar da gidanta idan ya so ya haɗa kuɗin ya kama wani business ɗin.

HALIMA

Farkawa nayi na tsinci kaina a gadon asibiti; cikin abinda bai gaza seconds uku ba kuma komai ya dawo mun na abinda yayi silar zuwana asibitin. Na sake runtse ido na hotunan su suna gilmamun, ban lura da mutane a ɗakin ba sai da na ji muryar Mama Fauziyya ta na cewa

"Wai yanzu haka za'a zubawa yarinyar nan ido ta salwantar da rayuwarta akan wani banza da bai san darajarta ba?". Mama ta ja tsakin da naji har tsakiyar kaina ta ce

"To Anty ya za'a mata? Halima dai ba yarinya bace da za'a kama a doka; iya bakin ƙoƙari lallami da nasiha har ma da faɗan an mata tunda abinda ta zaɓa kenan ai sai mu zuba mata ido kawai. Ni wlh na gaji, na ma faɗawa Abbansu daga nan gidanta zata wuce taje can tunda dama ba wani ya ce ta taho ba haka kawai ba zata kasheni da fargaba kafin lokaci na yayi ba".

"Ke kika so ai; tuntuni na ce ki tattara lamarinta ki aje a gefe kiyi rayuwarki amma kika ƙi sai kace ita kaɗai kika haifa. Ni fa shiyasa tuntuni na kama bakina, ga labari yana ta ci na a zuci amma sanin idan na faɗa ƙarshe tare zaku raba jinyar ya saka nayi shiru".

Haɗa baki Mama da Mama Fauziyya sukayi gurin cewa "labarin me?"

A jikina naji ta kalle ni dan ta tabbatar da har lokacin bacci nake kafin ta ce
"Auren da mijinta ya ƙara mana". Suka sake haɗe baki gurin cewa
"Me? Wane irin aure kuma? Yaushe?"

Ji naji kamar ta soka mun mashi a zuciya, na sake runtse ido hawaye masu zafi suka ziraro ta gefen ido na amma nayi ƙoƙarin saita kaina gudun yin motsin da zai ankarar dasu. Ina buƙatar jin ƙarshen zancen ko babu komai zan samu amsar wacece na tarar a ɗakin Mijina tareda shi cikin yanayin da nake fatan in manta saboda abinda tuna shi yake haifar mun a gangar jiki da zuciyata.

Ƙasa da murya tayi ta ce
"Ranar da kuka zo duba Inaayah har kika ganshi ai gurin yarinyar zai je, a nan ƙasan layinmu suke kusa da gidan Zinaru mai yi mun kitso basu ma daɗe da tarewa ba dan basu shekara ba shi ya siya musu gida a gurin.

Tunda ya fara zuwa Zinaru ta faɗa mun tana ganin Mijin Halima a gidan ni farko ma na ɗauka ko yan uwansu ne amma da naji Haliman ba tayi zancen ba sai kuma Zinaru ta faɗa mun ai yarinyar gidan yake so, mun kuma sha haɗuwa yanda yakeyi bai ganni ba nima in ɗauke kai to kuma sai ji mukayi an ɗaura aure".

Ajiyar zuciya Mama ta sauke kafin ta ce
"Ai dama duk wanda ya siyi rariya ya san zata zubda ruwa, to waya sani ko zancen auren ta ji yanzun?"
Chapter 107 · 0% Book details