Sashe 6
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaf muka gama kwalliyar mu, munyi kyau sosai aka mana hotuna kafin muka fita inda motar da ango ya turo ta ɗauki amarya ke jira. Saurayin Baby ya iso dan haka ta shiga motarsa Zulaiha ma saurayinta ne yazo ɗaukar ta se ni da Hansa'u ne muka shiga motar amarya muka tafi. Bayan an sauke mu kowacce seda saurayinta ya bata kuɗin da zatayi liƙi dashi har Hansa'u muna hanya da Alhaji Bala ya kirata seda yayo mata transfer kuɗi masu nauyi kan tayi kwalliya da liƙi haka akayi kamu aka tashi suna ta wanke amarya ni dai dana liƙa abinda na tanada dama na koma gefe na zauna seda aka tashi zamu tafi gida kafin har raina naji babu daɗi ganin still kowacce saurayinta ne ze maida gida suna ta zuzutun kwalliyar su. Kira uku nawa Bilal yace mun ze zo amma gashi har aka tashi shiru dana sake kiransa ma naji wayar a kashe. Wannan ya ɓata mun rai ban ko tsaya jira a gama watsewa ba nabi yan unguwar mu a Adaidaita muka tafi.
A ƙofar gida na tarar da Bilal tareda abokinsa Nura, duk da naji haushin ƙin zuwan da yayi gurin bikin amma ganin dana masa se naji zuciyata tayi sanyi. Light blue ɗin shadda ya saka data dace da atamfar ankon da mukayi me ruwan dark blue da ratsin fari da light blue ɗin. Na isa inda suke Ina haɗe fuska a son na nuna masa ɓacin raina amma na kasa musamman da Nura ya fara zolayarmu wai munyi too match dama mun haɗa baki ne amma gamu nan tamkar ranar auran mu. Haka na lalace a tsaye yana tsarani har seda Abba ya dawo kafin na wuce ciki su kuma suka tafi bayan sun gaisa dashi.
Ina tsaka da sallar magriba da isha'i da suka haɗe mun Amirah ta shiga ɗakin tana faɗin nazo inji Abba. Bayan na shafa addu'a na fita falo, Abba ma zaune yana kallon labaran ƙarfe tara. Seda aka tafi hutun rabin lokaci kafin ya juya kaina yana murmushi yace
"Hali dubu" haka yake tsokanata. Sunan babbar yayarsa ne kuma mafi soyuwa a gare shi cikin yan uwansa. Kwanana uku a duniya ta rasu seya haɗa soyayyar ta data kasancewata yar da ya fara samu duk yake mun.
Murmushi nayi kaina yana ƙasa na gaishe shi yana amsa yana tambayata biki kafin ya ɗora da cewa
"Yaya Salahu ya gaya mun sunyi magana da kawun Bilal yace ze kirashi duk yanda ake ciki ɗazu yake sake ce mun kimanin sati biyu kenan har yanzu beji daga gare su ba". Sena rasa abinda zance masa, ina ji yaci gaba da cewa
"Ɗazun har zan tsaya nayi masa magana da kaina se kuma sai nace bari na fara jin ta bakinki ko dai saƙon be iske shi ne". Daƙyar nace
"Eh Abba ya gaya masa. Dama maganar albashinsa da be fara samu bace ta dakatar dashi" se Abba yace
"Aa, har yanzu dama wannan matsalar bata kau ba? Na zata dana haɗashi da Malam Mansur yace mun an gyara komai tun last two or three months kenan da mukayi maganar.
"Eh Abba an gyara amma salaryn ne wai se wannan watan sannan suka sa masa na wata uku" na faɗa masa iya abinda na sani, se yayi shiru kafin yace
"Ikon Allah, to barka tunda an gyata ɗin. Yanzu ina kuka tsaya kenan a maganar?"
"Yace zuwa ƙarshen watan nan zasu zo" na faɗa ya amsa mun da
"Toh Allah ya nuna mana. Yaya Salahu ya damu, kin san fa babu sanda zamu haɗu ba tareda yayi mun mitar ƙin aurar dake ba. Kullum se yace ga Bishira nan da yaya biyu bayan rana ɗaya aka haife ku"
"To ita Abba ai muna gama secondary aka mata aure bata cigaba da karatu ba" na faɗa cikin shagwaɓa yayi dariya yace
"Haka ne amma dai da kema anyi miki ta tatan da yanzu kin fara tara mana masu samu bari bari a gidan nan ai". Sena rufe fuska ta da hijabi ina cewa
"Haba Abba ni yar yarinya dani ai dama ban isa aure ba har yanzu"
"Baki isa aure ba amma kin iya dafawa gardi abinci" Mu'azzam daya shigo falon ya faɗa, na galla masa harara ina cewa
"Abba ka mana tsakani dashi"
"Se dai in ce ya dena tsokanarki amma babu batun na miki tsakani da ɗan uwanki" Abban ya faɗa nace
"To ka gaya masa ya fita daga sabgata"
"Gaskiya ce bakya so kuma se an faɗa, har gulmarki ake a unguwa da anga yara da kula za'a ce daga gidan nan ne" Mu'azzam ɗin ya sake faɗa kafin nace wani abu Abba yace
"Arziƙi ne ai kai baka san ladan ciyarwa ba ko?"
"Ciyar da mabuƙata ba. Kai kake bin bayanta Alhaji shiyasa kullum take sake shiga daji maimakon ta dawo hanya" Umma data fito daga ɗakinta ta faɗa sena miƙe na sulalae ɗaki na barsu inaji Abban na kareni yana faɗin ai ba laifi bane idan na bashi da babu ai ba za'a masa ba.
Washe gari akayi ɗaurin auran Zainab a ranar kuma muka rakata gidanta mw kyau acan sabuwar gandu. Mijinta matashin ɗan kasuwa ne yayi ƙoƙari sosai a gininsa iyayenta ma sunyi namijin ƙoƙari gurin yi mata kaya da suka sake ƙawata gidan muka fito munata santi da yiwa juna shaƙiyancin wacece next. Duk su uku da ranar su ni kaɗai ce amma dukda haka a jikina inajin sena rigasu amarcewa domin dai nasu samarin a yanda suke ko yau akace a fito ayi aure kowanne yana da abin yin auren amma sun tsaya suna jan lokaci har da Hansa'u da zataje a ta huɗu.
Kusan sati uku da suka biyo baya ina ta juya yanda zan sake ma Bilal magana ganin bamu daɗe dayi ba kuma ha uzurin daya bani se naji dama Abban ya amsa maganar da kansa kawai dan harga Allah yanzu dana gama makaranta bana komai hankalina ya fara komawa akan nima nayi aure na tafi nawa gidan. Safiyar litinin Anty Labiba ta haihu, ina bacci Mama ta tashe ni wai zamuje asibiti daga can kuma bayan an sallameta muka wuce gida Mama tace in zauna mata kwana biyu, ban so ba amma babu yanda na iya haka na tafi gida na haɗo kayan da zanyi amfani dasu na kira Bilal ya mayar dani.
Seda nayi mata sati biyu, dake morata takeyi bata damu da zaryar da Bilal ya ringayi ba kullum se yaje anan zeci abincin dare ko kuma yazo da yamma idan ya taso daga aiki mu ɗanyi hira ya karɓi abinci ya tafi, duk zuwan da yakeyi kuma sau ɗaya ya samu ya shiga ya yiwa Anty Labiba barka dan kusan duk sanda zezo tana da baƙi yan barka dake ta kwana biyu bata haihu ba tsakanin Amir da Inayah shekara ɗaya da rabi ita kuma ta bawa Sadis shekara biyu tun nan kuma seda ta shekara bakwai yanzu ta haifi Amina takwarar Mama. Ba ƙaramar kunya naji ba sanda Bilal ya gama zamansa a falon Antyn ya tafi ba tareda ya bada ko sisin kwabo da sunan barka ba. Dama tun kafin suna dana ke masa hirar me ya kamata mu siya na takwarar da akawa Mama ya fara kawo zancen wata yazo ƙarshe har yanzu ba'a fara salary, a zato na ze bada wani abu amma se gashi ya tashi ko asi dukda uban naman suna da abincin da na jibga masa har yan gidansu seda suka ci.
Kwananta goma sha shida da haihuwa na koma gida saboda wata ƙanwar Mijinta bazawara data zo daga zaria, sena fake da zanje na maida kaya na na ɗebo wasu daga nan na fece ba komai ya saka hakan ba kuma illah Munir dake neman takura rayuwata yana kuma haɗa ni faɗa da Bilal. Ranar talata na koma gida Bilal baya gari yaje Jos mijin ƙanwar Hajjan su ne ya rasu babban mutum ne sosai shine duk suka tafi. Ranar alhamis zasu dawo tunda suka tafi kullum mukayi waya kwana uku kacal amma ya ringa mitar yayi missing Kano yayi missing abincin Kano ze kace wanda ya tafi wata ƙasar ta daban. Ran da ze dawo tun safe na tashi da shirin yi masa girki, na yi da ɗan yawa tunda duka tare da Hajja da yayyensa mata biyu da ƙaninsa ɗaya suka tafi se matar wansa nasna kuma duka a gidan Hajjan zasu sauka kan kowa ta tafi gidansu. Ina aikin Mama namun tsiyar da sakani tayi se nayi ƙorafin abincin yayi yawa amma dake na Bilal ne na zage inayi sedai kawai nayi murmushi har na gama na shirya komai nayi wanka a Adaidaita na ɗauki Amirah muka tafi gidan bayan munyi waya ya gaya mun sun dawo.
Ba wannan ne zuwa na na farko gidansu Bilal ba, badan ma Mama ta kafta mun warning ba da haka nan ko faɗa mukayi na kirashi a waya be amsa ba zan zari jiki in tafi, tun Hansa'u na rakani har ta dena yanzun ko nasan ko giyar wake nasha bazan cw tazo muje ba shiyasa ma naja Amirah ko Maman ce mata nayi Aliyu me Adaidaita zan bawa ya kai musu ni kuma zan wuce gidan kitso badan ba nasan ba zata bari in kai abincin da kaina ba. A kuyance muka gaisa da yan gidan nasu suna ta nan nan dani kamar su goyani ban wani jima ba nayi musu sallama muka fita se da muka fito waje kafin naga Bilal dan sanda muka je ance yana ɗakinsa yana wanka. Se naga kamar ya rame a kwana ukun da ban ganshi ba, ya jingina jikin bango yana kashe ni da kallon so yace
"Ashe dagaske kike zaki zo"
"Oh da ka ɗauka da wasa nakeyi? Ai na gaya maka zanzo nawa Hajja gaisuwa dama" na bashi amsa seta miƙe tsaye sosai yana cewa
"Kin kyauta, kuma naji daɗi sosai". Ya shafa cikinsa yace
"Kin san ruwan tea kaɗai nasha muka kamo hanya, ina kwanukan kuma na ganki ke kaɗai?"
"Suna cikin gida na bashi amsa" se ya wani kalleni yace
"Cikin gida kuma? Abincin nawa kika kai mun cikin gida Halims? Maimakon ki buga mun ƙofa ki ajiye a nan kafin ki shiga?"