← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 158

Sashe 64

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da izinin uban wa kika ɗauki abinci na kika basu?" Ya faɗa dai dai ina fitowa daga ɗaki. Shiru kawai na yi ina kallon sa dan ban san me ya kamata na ce masa ba, hakan ya sake harzuƙa shi kamar zai rufe ni da duka ya sake cewa
"Ina miki magana wato ga mahaukaci shi ne zaki mun shiru ko? Saboda baki da hankali baki san dai dai ba, nan yan uwa na jini na suka zo gidan nan ku ka hana su abinci amma yanzu wasu kattin banza ba dangin iya babu na Baba sun zo jikin ki na rawa kin ɗebo ruwa da lemo kin basu, bai ishe ki ba kin sake kawo musu nama sannan abincin baki ko bari ma na ga kalar abin da kika girka ba kin kawo musu tsabar kin mayar da ni banza shashasha sauran da suka rage zaki zuba ki kawo mun. Sai ki zo ki kwashe tsiyar ki dan ni ba mahaukaci ba ne da zaki bani sauran arna na ci. Wace tsiyar kika ga sun kawo mana balle ki ɗauki abinci na ki basu?"

Kallon sa kawai na ke yi yanda ya fitittike yana masifa sai kace wanda na aikatawa wani zunubi, daga na karrama baƙin sa shikenan cibi ya zama ƙari? Maganar sa ta ƙarshe ta saka na fahimci ainihin dalilin faɗan na sa, mamakin sa ya nunku a raina. Ban tsammaci a fili na furta
"Yanzu saboda basu kawo komai ba ne ya saka kake wannan masifar ashe" sai kuwa ya yo kaina yana cewa

"Kika zage ni sai na naɗa miki duka a cikin gidan nan Halima daga ni sai ke babu mai ƙwatar ki a hannu na". Da sauri na ja baya zuciya ta na bugawa da sauri. Da gaske na tsorata da yana yin sa, lokaci ɗaya idanun sa suka rikiɗa suka yi jaa. Ya nuna kan sa yana cewa
"Saboda ba su kawo ɗin ba ne, ai ni ba ɗan iska ba ne da zasu zo su cinye mun abinci su tashi ko kuwa kin ga gida na yayi miki kama da sansanin gajiyayyu da zan ringa ciyar da mutane kyauta?
Wannan ya zama karo na farko kuma na ƙarshe da wani ɗan iska ko yar iska zasu sake zuwa gidan nan ki ɗauki wani abu ki basu ba tare da izini ni na ba, idan kuma kin cika ke bakya jin magana ki sake" ya faɗa yana kaɗa yatsunsa biyu a fuskata.

Motsin da Al'amin ya yi ya sa na yi firgigit na kama jiki na guri ɗaya a tsorace kafin na fahimci shi ne na nutsu ina sauke ajiyar zuciya. Na kasa yarda lafiyar Bilal ƙalau, abin da ya faru yanzu ya saka mun kokwanto a zuciya ta, an ya kuwa Bilal baya shaye shaye? Gaskiya akwai abin da yake afawa a ɓoye da yake gotar masa da saitin kan sa dan dai abubuwa da yawa da yake yi basa kama da na wanda yake fully oriented.

Ban da ma sharrin ƙwaya, na ga daga abincin da yake masifar akai har zuwa naman da ruwan da lemon babu wanda aka siya da sisin kobon sa. Cikin kuɗin da na samu na suna na yiwo cefane na, gishiri ne kawai ban siyo ba amma hatta mai da maggi sai da na siya. Komai na mu ya ƙare Macaroni ce leda shida da Taliya biyu sai shinkafa da nake zaton ba zata haura kwano ɗaya da wani abu ba shikenan abun da ya yi mana saura. Niyya ta idan ya dawo ya ci abinci muka nutsu na yi masa zancen kayan abincin ga kuma a yanda ya dawo gidan.

Ina so na je na bashi haƙuri na tambaye shi ko na dafa masa indomie ya ci kuma ina tsoron kar na je bai gama hucewa ba na sake tada wani ballin daga ƙarshe dole na haƙura na bari sai da safe zuwa lokacin duk ma abin da ya sha ya sake shi, sai da na wanke kwanukan da suka ɓata. Har na yi shirin bacci amma zuciya ta ta gagara nutsuwa, ko da ace wani abun ya sha da gaske bai kamata na barshi shi kaɗai ba. Irin fushin da na gani tattare da shi kar ya je ma ya yiwa kansa wani abun ina zaune ban sani ba. Wannan tunanin da na yi ya saka na zabura na tashi na goya Al'amin na saka Hijab na tafi ɗakin sa.

Ta window na hango shi ɗai ɗai akan kujera da waya kare a kunnen sa, duk da ya bani baya ne amma daga yanayin gefen fuskar sa na fahimci dariya ya ke yi. Wannan ya bani ƙwarin guiwar ƙarasawa na murza hannun ƙofar sai na ji ta a rufe, ƙwanƙwasawa na yi a hankali tun da ya na kusa na san zai ji amma bai amsa ba, na sake bugawa karo na biyu still yana zaune ko motsi bai yi ba hakan ya saka na ƙara ƙarfin bugun ko wayar da ya ke yi ce ta ɗauke masa hankali sai kuwa ga shi ya taso, na ɗauka buɗe mun zai yi ga mamaki na sai gani na yi ya kashe fitilun falon dan switch ɗin a kusa da ƙofar suke sannan ya koma ya yi kwanciyar sa akan kujerar.

La shakka na san ya san da tsayuwa ta hakan da ya yi kuma yana nufin kar ma dame shi ne ko kuma baya buƙata ta a gurin kenan. Na rasa me zan yi, haushi ya kamata na ji ko kuma dariya zan yi oho, haka nan na ja ƙafafu na na koma ɗaki, ina sauke Al'amin Bismillahi ya ce dawa Allah ya haɗa mu. Ashe kukan da ya yi jiya nafila ne. Yanda kasan wanda ake yankar naman jikin sa haka ya ringa zuga kuka, duk yanda zan yi na lallashe shi na yi abu ya ci tura daga ƙarshe na kwantar da shi kawai nima na fashe da kukan yana yi ina yi. Idan na tuna Bilal ya na cikin gidan yake tsala kukan da na tabbatar har maƙwafta suna jiyo shi amma bai leƙo ya tambayi ba'asi ba sai na ji duniyar ta sake yi mun zafi.

Daƙyar ya yi shiru guraren ƙarfe ɗaya bacci ya ɗauke shi, ina durƙushe gaban gadon nima a haka baccin ya ɗauke ni bana jin an yi ko minti goma cikakke ya sake farkawa da kukan da ya fi na farko.

Bani da wani zaɓi da ya wuce na ɗauki waya na kira Mama a lokacin tun da in sake komawa gurin Bilal ma ɓata lokaci ne tun da ai shi ɗin ba kurma bane balle na ce bai ji duk kukan da yake yu ba ne. Kira uku na yiwa Mama har wayar ta gama ringing bata amsa, ita kaɗai ce bata kashe wayar ta a gidan idan zata kwanta sai ni saboda raba dare da muke yi muna waya da Bilal lokacin da nake gida amma har Abba kashe ta sa yake yi su ɗin dai su zan nema su iya kawo mun agaji a kowanne irin yanayi a kuma kowanne lokaci gashi ban same su ba haka nan na aje wayar na ɗauke shi, sai na ji jikin sa ya yi zafi alamar zazzaɓi na san azababben kukan da yake yi ne ya haifar masa da shi.

Muna da paracetamol wanda aka rubuta masa a asibiti na ɗauka na bashi, haka na ringa jele da shi kamar jiya sai da sanyin asuba ya fara busawa kafin bacci ya sake ɗaukar sa. Ina zaune dan baccin ma yaƙi zuwar mun saboda gajiyar da na yi na jiyo motsin buɗe ƙofar Bilal, ban kawo zai shigo gurin mu ba, to me zai yi mana? Kwatsam kuma na ji an buɗe ƙofar falon ban motsa daga in da na ke ba har ya shigo ɗakin. Na ɗaga kai na dake mun ciwo kamar me na kalle shi, shi ɗin ma ni yake kallo fuska ba yabo babu fallasa. Mayar da kai na na yi ƙasa cikin taushin da ban tsammaci ji daga muryar sa ba ya ce

"Mai ya samu Al'amin ya yi ta kuka cikin dare?"
Ɗaga kai na yi na zuba masa idanuwa na da suka ƙanƙance saboda kuka da rashin bacci. Da zan iya da na kwarara masa ashar kafin na ce masa uban sa ne ya same shi ya ke kukan, amma harshe na ya yi mun nauyi, ba zan iya zagin miji na ba, mijin ma kuma Bilal abin ƙaunata. Sake mayar da kai na nayi ba tare da na ce masa komai ba. Ina jin sa ya matso in da na ke ya dafa ni yana cewa
"Mai ya samu idon ki haka Halima?" Baƙin ciki da takaici suka tsaya mun a wuya ban san lokacin da na fashe da kuka ba.
"Dan girman Allah ka fita, idan ka tashe shi wlh Allah sai ya saka mun" na faɗa cikin kuka ina nuna masa ƙofa.

Shiru ya yi yana kallo na kafin ya ce
"Allah ya isa kika yi mun Halima?"
"Ko ban yi maka Allah ya isa ba haƙƙin kukan da ɗan ka ya ringa yi kana jin sa kayi biris ba ze barka ba. Ka fita Bilal ka fita bana son ganin ka" na sake faɗa cikin ɗaga sauti.

Kallo na ya sake yi na kusan minti ɗaya dai dai lokacin kuma aka fara tayar da Iƙama a masallaci, ina jin sa ya sauke numfashi ya ce
"Na faɗa miki zan tafi wani aiki Abuja, Jirgin ƙarfe bakwai zan bi, idan zaki iya ki sama mun abin da zan ci kafin na fita" yana gama faɗar haka ya fita daga ɗakin na rakashi da kallo idanuwa na na tsiyayar da hawaye. Wai duk waɗanda suka auri Mazan da suke so haka suke kwasar baƙin ciki kullum ko kuwa ni ce ban yi dace ba?
Chapter 64 · 0% Book details