← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 158

Sashe 85

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A tsakar gida ya tarar dasu Fadila tsaye da akwatinta tana ganin sa tace
"Yawwa gashi nan ma yazo ai" Hajja tace
"Kai kuwa ina ka jefa wayarka tun asuba nake kira baka amsa ba ko ka manta sammako zatayi? Shiyasa fa tuntuni nace ka bata kuɗin motar ta a hannu saboda irin haka yanzu da ƙyar idan zata samu motar farko sai tayi jira wata ta cika".

Cikin falo ya shige ba tareda ya amsa ta ba ya zauna kan kujera haɗi da dafe kansa da hannu biyu, Hajja ta shiga tana cewa
"Au ina magana shine zaka shige ɗaki ko ka amsa ni?"

"Ai tafiyar tata ba zata yuwu ba ma Hajja" ya faɗa yana gyara zama, sai ta zauna itama tana cewa
"Saboda me?"
"Mun ɗan samu matsala ne da Halima ta tafi gida, kinga kuma idan ta tafi ai ba zai yuwu ki zauna ke kaɗai ba tunda har yanzu jikin ki da saura" ya bata amsa. Sai kuwa ta zabura tace

"Kaji yar abu ta kazan uba au saboda zanzo gidan shine tayi yaji?"

"Bafa dalilin zuwanki bane" yayi saurin katseta, Fadila tayi tsugul tace
"Wlh saboda haka ne dama ai na gaya miki wlh da wahala ta yarda ki zauna a gidan nan dan ji take kamar na ubanta bata so kowa ya shiga sai ita da danginta".

"Ke, waya sako bakinki ko sa'anninki ne suke magana?" Ya faɗa yana ballawa Fadilan harara, Hajja ta taso masa itama tana cewa
"Ko ba'a sako da ita ba ai gaskiya ta faɗa, to kuwa bata isa ta hanani zuwa gidan ka ba billahilazi tunda haka ta zaɓa to kuwa ta tafi kenan sai ka tafa mata resit ka bita dashi kaga sai tayi zama mai lasisi kai kuma ka samu sarari ka auro mutuniyar kirki da suka gaji arziƙi ka saka ina dama duk ita ta kanainaye komai da anyi magana kace Halima to yanzu ta tafi Kuma in dai da yarda ne kar ta sake dawowa cikin gidanka ya isa kuma haka a canza sheƙa".

Shiru yayi kansa a ƙasa, ya za'ayi Hajja tace ya saki Halima? Sannan kuma tayaya zai gaya mata shi fa ko aure zaiyi ba Jalila zai aura ba ko dan bata san ainihin alaƙar dake tsakaninsa a Jalila bane?

Miƙewa yayi a a sanyaye yana cewa
"Idan ta huce dai na san zata dawo"
"Ta dawo ina? Ai wlh kaji ma na rantse ta tafi kenan. Ba dai dama ni na dage sai ka aureta ba na ɗauka dangin arziƙi ne ashe duk shigo shigo ba zurfi suka mana, tunda kuwa yanzu ta saka ƙafarta ta tafi to kuwa ba zata dawo ba kama cireta maza daga ranka ka tattara hankalinka kan wannan yarinya Jalila ayi maza ayi komai ita kuma can su ƙarata Allah sauki tsiya lafiya".

Da wata sabuwar damuwar ya fito daga gidan Hajja, can gefen hanya ya gangare ya kashe mota ya kife kansa jikin sitiyari ya tafi tunanin haɗuwar sa da Jalila.
[4/7, 9:01 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 36*

Ƙaddara da kwaɗayi haɗi da son zuciya irin nasa ya janyo masa faɗawa tarkon nadama. Dukda dai tsohon halin sa ne, a baya lokacin samartaka ya kan kwatanta domin rage zafi kamar yanda hakan yake ɗabi'ar dayawan Samari a wannan zamanin. Sun ɗauki hakan a matsayin wayo ko dabara a ganin su ai basu aikata Zina a zahiri ba sai dai suna mantawa da hanin ubangiji da yace kada a kusanci Zina ba wai kada a aikatata ba Aa kwata kwata kada a kusanci duk wani abu da yake da jiɓi da ita. Da yawan su sun ɗauki hakan a matsayin ƙaramin zunubi domin wasu basu ma yarda cewa dasu da wanda ya keta haddin macen da ba halalinsa basu da banbancin zunubi. Su kan manta ita kanta Zina ta kasu kashi da yawa, a ciki akwai Zinar idanu da kuma ta baki da kunnuwa wadda suke aikatawa domin kuwa suna kallon haram, su saurari haram su kuma furta haram da bakunan su wanda illolin hakan dai dai suke da wanda yayi fasiƙanci da mace a zahiri.

Ko farkon haɗuwar sa da Halima ya so ya gabatar mata da irin wannan soyayyar sai dai bata bashi fuskar hakan ba shima kuma bai takura mata ba daga baya ma kuma ya tuba ya bari har zuwa lokacin da sukayi aure kafin lokaci ɗaya Jalila ta faɗo rayuwarsa ta wargaza komai ta sake jansa ruwa har ta kaishi da aikata abubawan da suka zarce waɗanda yake aikatawa a baya.

Silar Hafiz ya haɗu da Jalila, ita ɗin tsohuwar budurwar Hafiz ce tare sukayi karatu a London dan har an saka musu ranar aure ya rage saura watanni aka fasa sakamakon ganinta da mahaifinsa yayi tareda wani abokinsa a France sunje wani taron kasuwanci ita kuma tayiwa Abokin nasa rakiya wanda ya kasance Sugar Dadynta.

Hafiz bai taɓa sanin baɗinin Jalila ba, dukda ya san macece me rawar kai dan shi yake tsawatar mata abubuwa da yawa saboda son da take masa kuma take ragewa kuma da yake shi ɗin bai zo mata da fuskar da zasuyi irin rayuwar da takeyi a bayan idonsa ba sai ta ɓoye masa zahirinta, ko da wasa bai taɓa sanin irin rashin jin da takeyi ba sai bayan da mahaifin ya kirashi ya gaya masa babu maganar aure a tsakaninsa da ita ya nemo wata matar yar gidan mutunchi tunda wuri. Koda Dady ya sanar masa sa abinda idon sa ya gani ma da farko har ransa bai yarda ba dukda ya san babu wani dalili da zai saka Dady ya masa ƙarya ko ya hanshi aurenta. Sai sa ya ringa bibiyar takunta a hankali komai ya fito ya gane zahirin wacece ita ya mata kaca kaca suka raba hanya a lokacin har kusan rataye kanta tayi saboda yanda take masifar Son sa, tayi rantsuwa da yi masa alƙawarin zata daina duk wani abu da takeyi in har zai aureta amma yace la la, in taga dama ta tuba saboda Allah amma ba dan shi ba domin ba zai taɓa aurenta ba bayan yasan wacece ita.

Haka nan tayi naci, Tun tana bibiyarsa harta haƙura ta ƙyale shi tana ji tana gani ya fara soyayya da Yasmin har suka yi aure daga ƙarshe ma ya bar Abuja ya dawo aiki a Kano. A hankali bayan wani lokaci da naci da bin binin da take masa ya fara sauraronta suna gaisawa a matsayin abokai kamar yanda suka faro tun asali kafin soyayya ta shiga tsakanin su, har ranta tana fatan a hankali ta shawo ya amince ko a ta biyun ne ya aure ta bata damu ba dan tana tsananin son Hafiz sai dai shi clearly ya gaya mata kada ta yaudari kanta domin ba zai taɓa aurenta ba. Ko da ya ke sauraronta a yanzu ma saboda yaga alamun ta kintsune saboda ya rage mata raɗaɗin takunkumin da iyayenta suka saka mata tun bayanfallasar asirinta da fasa aurensu yake yake sauraronta yana Kuma ƙara yi mata nasiha da nusar da ita gaskiya.

Jalila bata rasa komai ba domin mahaifinta hamshaƙin mai kuɗi ne haka mahaifiyar ta data kasance Balarabiya itama mai kuɗin kanta ce. Babu abinda suka rageta dashi a rayuwa kusan ma gatan da ya mata yawa yana da nasaba da silar lalacewarta. Tun tana secondary school take riƙe manyan kuɗaɗen da suka shallake shekarunta tafiyarta Turai karatu kuma ya sake bata yanci a nan ta haɗu da ƙawayen da suka buɗe mata ido da maza, da kuɗin ta take amfani ta mallaki duk saurayin da yayi mata idan ta gama yayinsa ta sallame shi ta ɗakko wani kusan Abokin Dadyn Hafiz shi kaɗai ne saurayin da ta taɓa yi babba kuma mai kuɗin kansa wanda shima wayewar sa da yanda ya iya soyayya irin wacce take so ta jata harta biye masa suke fita ƙasashe tare har hakan ya zamo silar tonuwar asirinta.

Yanda suka haɗu da Bilal kuwa lokuta da dama musamman idan zata tafi Umarah yawanci ta Kano take tashi dan haka a duk sanda ta shigo Kanon Hafiz take nema idan tana buƙatar wani abu, a irin haka wani lokaci ta dawo daga Saudiyya lokacin Matar Hafiz ɗin ta haihu suna tare da Bilal ta kirashi akan yazo Airport zai karɓi saƙo wa Baby a lokacin har yace ba zaije ba sai dai kuma ya canza shawara da yayi tunani ko babu komai bai kamata ya wulaƙanta ta ba tunda ya san bashi ya ɗora mata sonsa ba daga Allah ne duk kuma irin cin kashi da tijarar daya mata a baya bata saka ta fita a sabgarsa ba shiya kawai yake jurewa yana biye mata lokutan.
Chapter 85 · 0% Book details