← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 158

Sashe 120

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuska a sake kamar babu wani abu tsakani Hafiz ɗin ya tarbeshi, Suhaila ce dai ya karanci canjin fuska a gurinta hakan kuma ya saka ya zargi ko dai Halima ce ta kai masa ƙarar sa shine yar taya ɓera ɓuruntu take tayata fushi da shi.

"Baka kyauta ba, ko me Halima tayi maka bai kamata ace zaka turata gida saboda ka samu wata ba" Hafiz ɗin ya faɗa masa dalilin kiran, ya wani yi kinini da fuska ya ce

"Gaskiya ni ban fiya son ana tsoma mun baki cikin sabgar gida na da iyalina ba shiyasa ko iyayena bana kaiwa ƙara balle wasu mutane can bare".

Hafiz dai jijjiga kai yake yana kallon sa yan kuma sauraron abinda yake cewa, wato shine baren? Ko da yake tuni lamarin Bilal ɗin ai ya gama bashi mamaki ko mai zaiyi yanzu sai dai ya kalle shi da ido kawai.

Bilal ya cigaba da cewa
"Ni bani da lokacin da wani zai ajiyeni yanzu ya ringa gaya mun abinda ya kamata nayi da wanda ba zanyi ba, ita bata san dama haƙuri kawai nake ina zama da ita ba dan da ita namiji banbancinsu kaɗan ne a guri na. Saboda kuna na ce zan auro wacce nake so shine zata tada fitina, tace na saketa tun ba'aje ko ina ba shine zata fara bibiyar neman sulhu? Toh wlh ko zan mayar da ita sai ta ji a jikinta ta yanda ko wani ya sakw zugata ta mun abinda tayi a baya ba zata kuskura ta ji ba".

Mamakin jin wai ya saketa ya hana Hafiz sake ce masa komai sai kallonsa kawai da ya ringayi, daƙyar ya ce
"Ai bata gaya mun ba, toh Allah ya sa hakan shi ya fi alkhairi a tsakaninku amma gaskiya kamar kayi ganganci"

"Ba wani ganganci ni nake zaune da ita ni na san halinta ku kawai daga nesa kuke mata kallon ta ƙwarai amma yarinyar nan bata da mutunchi, kawai dan ni ba mai tona sirrikan mutane bane amma dai shikenan" ya sake faɗa kafin yaja farantin kayan ciye ciyen da sai da Hafiz yayi magana kafin Suhaila ta saka mai aiki ta kai masa.

Shi dai Hafiz kallon sa kawai yakeyi bakin sa na so ya furzar da maganganun da suka cika shi taf amma ya danne domin komai yana da lokaci. A hankali ya ce masa

"To ita wacce ka aura ɗin yanzu ka san halinta ne?"
"Yarinyar da na shafe sama da shekara goma da ita kake tambaya na san halinta? Kamar yanda na san kaina kuwa" ya bashi amsa, Hafiz ya sakeyin shiru sannan ya ce

"Allah ya sanya alkhairi toh, ni na ɗauka ma yar gida za'ayi da uwarɗakin naka dukda kana ɓoye mun, ashe kai da Target ɗin ka a gefe".

Dukda Hafiz bai ambaci sunanta ba amma ya gane wa yake nufi cewar da yayi kuma wai dukda suna ɓoye masa ta saka lokaci ɗaya tashin hankali ya rufto masa har sai da ya ƙware da lemon da yake sha ya shiga tuttula tari shi dai Hafiz sannu yake masa a ransa yana dariyar wautar Bilal ɗin. Shi fa duk a zatonsa ya fi kowa wayo ne ko me yake nufi oho?

Sai da tarin ya lafa masa kafin ya ce
"Wacece uwar ɗaki na?" Yana kallon Hafiz ɗin ƙasa ƙasa shi kuma ya gyara zama ya ce
"Jalilah mana. Ai ta gaya mun soyayya kukeyi a yanda ta ce nan da yan satittika ma za'a fara maganar aurenku, amma na san bata da labarin auren da kayi ko? Dan na santa da baƙin kishi gaskiya da taji da yanzu ta tayar da hankalinta musamman da na fahimci tayi nisa a soyayyarka kuma da gaske take. Amma wai yaushe duk hakan ta faru bani da labari?"

Bilal dai yanda kasan wanda za'a rataye haka ya tsure, fuskarsa kaɗai zaka kalla ka hangi tsantsar tashin hankalin da kalaman Hafiz suka jefa shi a ciki.

Tunani yakeyi, me da me Hafiz ɗin ya sani? Iya kacin zancen soyayyar su? Ko kuwa harda ɓoyayyiyar alaƙar da take tsakaninsu? Kai ko ma dai Halima ta faɗa masa komai kawai wasa yake masa da hankali ne?"

Ya akayi ne duk ka wani firgice daga zancen Jalilah kar dai kaima tsoronta kakeyi?" Hafi ya faɗa cikin wasa kafin ya cigaba da cewa

"Allah ne ya kamata dan na tabbatar yaudararka kawai takeyi amma Jalilah ta fi ƙarfin matasa irinmu yanzu ai ta yuwu sai dai kawai kaji tayi aure dan akwai ƙishin ƙishin ɗin da naji kan wani Senator da yake sonta kamar har an kai gaisuwa ma"

Sai ya ji kamar an tsundumashi a ruwan ƙanƙara har ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke Hafiz kuwa canza akalar hirar tasu yayi zuwa zancen office wanda shi ya bar gurin yanzu ya koma jagorancin ɗaya daga kamfanonin mahaifinsa dama shi ya nace akan aikin gomnati amma Babansa baya so yanzu kuma da kansa ya saki, farin ciki ya mamaye Bilal, bai wani damu da ce masa da yayi gaskiya idan bai yi wasa ba za'a iya sallamarsa daga aiki saboda sunce sun gaji da abinda yakeyi gashi dama anyi sabon DG a ministry akwai shirye shiryen kora da ɗibar sababbin ma'aikata kuma yanda Ogansu na nan yake ƙorafi akansa yana tsoron kada abun ya rutsa da shi.

Ko a jikinsa domin ko an koreshi ya san zai samu in da zai lafe a kamfanin Hafiz ɗin. A gidan ya kusan wuni suka sha hirar yaushe gamo har ya tallatawa Hafiz shagunan gurin Jalilah wanda ya ce na wani yayan abokinsa ne saboda waɗancan mutanen da aka ce suna so yaga alamar wasa a lamarin su yana kwatantawa Hafiz ɗin in da suke kuwa ya nuna sha'awa har ya ce bari rana tayi sanyi sai suje su duba dan dama yana neman shaguna zai siya.

HALIMA

Sosai naji daɗin sallar da nayi, har gabannin asuba kafin bacci ya fara fizgata amma na daure sai da nayi sallahr asuba sannan na kwanta. Gurin ƙarfe takwas Anty Labiba ta tashe ni, na kalleta ganinta cikin shiri da key ɗin mota a hannu.
"Zan fita, ga abin kari nan a dining, ki tashi da wuri dan Allah kiyi lunch kin san za'a kaiwa yara makaranta idan akwai abinda kike buƙata a taho miki dashi daga gidan Mama kuma ki kirani anjima dan kar in manta" ta faɗa tana kallona. Na yamutsa fuska, abinda ya faru jiya ya shiga dawo mun sai nayi narai da ido na ce

"Nima ai gidan zan tafi"
"Yana falon sa kije ki gaya masa" ta bani amsa tana nufar ƙofa, sai na miƙe ina cewa

"Ni dai wlh gidanmu zan tafi in dai na son a takurawa rayuwar mutun ba ta yaya za'a ce ya zauna a nan gidan?"

Bata ko kalleni ba tayi ficewarta dan haka na haɗiye kukan da na so in fasa mata na koma na kwanta tunda ta ce Uncle Saleh yana nan amma da zarar ya fita zan kama gabana dan ba zan zauna a gidansu ba wlh.

Bacci na so ta koma amma na gagara yi sai kawai na tashi nayi wanka na shirya kafin na fita na karya. Bayan na gama na ɗauki wayarta a shiga latsawa dan babu wani aiki da zan mata a gidan sun gama komai, fitowar Uncle Saleh ta saka na shiga taitayina na sauka ƙasa na shiga gaishe shi sai ya dakata ya samu guri ya zauna, nasiha ya shiga mun amma da yake muryar tasa kullum a kaurare take fuska kuma babu fara'a sai na ringa jin maganganun nasa kamar faɗa. Ya gama ya fita kaina na ƙasa sai da na ji ya rufe ƙofa kafin na kona kan kujera na zauna ina sauke numfashi.

Ni kaina ba kamar yanda na kwanta jiya ba yau ɗin da na tashi na jini sakayau kamar an sauke mun wani nauyi a jikina, tabbatas sallolin da nayi sun taimaka mun matuƙa gurin samun nutsuwa amma dukda haka isanyna tuna wai Bilal ya sakeni sai hawaye sun tarar mun a ido ban dai basu damar zubowa bane na daure.

Kan wayata na koma na lalubo number Hansa'u dan ina tura mata text dan ta nan kaɗai nake samunta yanzu shima sai taga sama ne take maido mun da amsa, ido na ya sauka kan sabon saƙo daga Bilal wanda naga time tun biyar bata gama cika ba aka turo, maganganu dai marasa kan gado ya aika mun yana sake jaddada mun sai nayi nadamar rabuwa da shi. Sai naji abun ya bani dariya ma, a fili na ce

"Allah ba dan halina ba ka yaye mun jarabtar son bawan Allah ka bani ikon nuna masa ni ba banza bace yanda yake kallona". Hawaye suka shiga silmiyo mun, Bilal kallon ballagaza yake mun akansa dukda ba laifinsa bane ni na nuna masa hakan nake a soyayyarsa amma yanzu idan Allah ya yarda zanwa kaina faɗa, ko da ace akwai rabon sauran zama a tsakanin mu zai nemawa kaina mutunchi.

"Ashe baki haƙura ba kenan?" Zuciyata ta tuhumeni ban bata amsa ba na kawar da zancen ta hanyar rubutawa Hansa'u saƙo "Bilal ya sake ni, dan Allah idan kina gari ki zo idan ma bakya nan muyi waya dan ina tsaka mai wuya ina buƙata shawara" abinda na aika mata kenan ko minti biyu cikakku kuwa ba'ayi ba sai ga shi ta kira, sai da ta gama ihun murna da hamdala kamar kafin muka shiga magana ta nutsuwa kuma ta fahimta. Yinin ranar sur maganganunta na ringa tisawa wanda zallar gaskiya ce a cikinsu na kuma samu ƙwarin guiwa domin yana daga dalilin da ya saka nake son Hansa'u, za muyi faɗa ta zageni amma kuma ba ta gajiyawa zata faɗa mun gaskiya ta sigar data san zan fahimta saɓanin Anty Labiba da take ganin faɗa da masifarta ne zasu saka na gane abinda take haska mun.
Chapter 120 · 0% Book details