← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 158

Sashe 70

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Satin farko na dawowar mu zan saka shi a jere ranakun jin daɗi da kuma farin ciki a rayuwar aure na. Irin tarairaya da soyayyar da Bilal ya gwada mun ba ta nan kusa ba ce na kuma yarda da gasken da ya ce yayi kewata haka ne, ban san dalilin sa na ɓoye hakan a wancan zuwan da yayi ba amma dai duk wani haushin sa da nake ƙunshe da shi daga wancen lokacin sai da ya saka klin da hypo ya wanke fushin tas.

Kamar yanda aka ce yau da gobe bata bar komai ba tabbas haka ne domin kuwa yau na wayi gari babu ko ƙwayar hatsin da zan sarrafa mu ci a safiyar Talata. Tun dawowar mu nake tsammanin Bilal tun da ya san cewar komai na mu yayi ƙasa zaiyi ƙoƙarin ya siyo, kusan miya da soyayyen naman da na taho da su daga gida ne ma suka ɗan ja mu sati ɗayan ba tare da na buƙaci cefane na dole dole ba. Ruwan shayi na tafasa ma zuwa a flask nayi wanke wanke na gyara kitchen ɗin, indomie guda ɗaya da ta rage na tafasa na ci dan yunwa nake ji dagaske ba zan iya jira har sai ya tashi daga bacci kafin ya ƙaro wata na dafa mana ba dan dama na ɗauka guda biyu ce shiyasa ko da ya dawo jiya da dare bai shigo da komai ba ban wani damu ba.

Ina cikin shirya Al'amin Bilal ya shigo ɗakin yana hamma haɗi da shafa cikin sa, yanda yake yi ko bai yi magana ba na san yunwa nake ji, ya jefe ni da harar da ban tantance ta wasa ba ce ko ta gaske kafin ya ce
"Dariya ma kike yi mun ko?"
"Ni na isa? Ba dariya nake yi ba ka san dai haka fuska ta take dama" na faɗa ina miƙa masa Al'amin da na gama shiryawa. Ya karɓe shi ya zauna tare da shi a gefen gado ni kuma na wuce gaban wardrobe dan ciro kayan da zan saka.

"Badai baki ɗora abin karyawa ba?" Ya faɗa yana bi na da kallo. Sai da na ware doguwar rigar atamfar da na ciro kafin na kalle shi na ce
"Na dafa ruwan tea kai nake jira ka tashi ka siyo Madara da Milo tun da da sauran cake ɗin can sai a sha da shi dan na san babu lallai a samu burodi tun da rana ta fara yi goma yanzu".

"Ban gane na siyo Madara da Milo ba, kina nufin babu kayan shayi a gidan ko me?" Ya faɗa kusan cikin ɓacin rai, na dakata daga zuge zip ɗin rigar da nakeyi na ce
"Amma dai kai ne ƙarshen amfani da su jiya da dare tun kuma da zaka sha shayin sai da na gaya maka sauran kenan na juye a container baka kula ni ba".

"Kada ki gaya mun maganar banza Malama, kina nufin saboda na sha shayi da dare dan haka na sha rabo na ma safe ko me?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Hannu biyu na ɗaga na ce
"Mai da wuƙar ni ba haka nake nufi ba amma dai kayan tea sun ƙare, ni da wannan sutun ma da taimakawa kayi ka siyo dan yunwa nake ji sosai Indomin da na ci babu in da ta je mun".

Fita yayi ba tare da ya sake cewa komai ba, na cigaba da shiri na ina mitar yanzu kuma kayan shayi ne zasu haɗa husuma da safiyar Allah, shi dai baya raina abin magana dama.

Madara biyu Milo biyu ya siyo na sachet sai burodi babba guda ɗaya, na ringa kallon kayan sai dai gudun jan fitina ya sa ban ce komai ba na ɗora komai a try, sai da na ɗakko container sugar na ga shima ashe ya ƙare burbuɗi ne a ciki na tattara na kai masa falo in da yake zaune yana jira. Har muka gama karyawa babu wanda ya ce ƙala, yana gamawa ya wuce can part ɗin sa, ƙamshin turaren sa da na jiyo har cikin falo na ya sa na gane wanka ya yi zai fita, ina nan ina sauraren ya shigo na ji yanda za'ayi da girkin rana sai jin ƙarar rufe get na yi. Na tashi na fita da sauri amma ko ƙurarsa ban tarar ba sai ƙamshin sa da ya baza tsakar gidan.

Komawa na yi na ɗauki waya ta na shiga kiran sa, kira uku bai amsa ba haka na haƙura na ƙyale shi. Shiru shiru har sha biyu bai biyo kiran ba ga yunwa ta fara kawomun farmako dan Al'amin tsotso ne da shi ba na wasa ba, sha ɗaya idan ya yi sai na samu wani abun na cike gurbi. A can gidan Anty Labiba da yake ba na aikin komai sai dai na ci abinci na kwanta shi ya sa na cika na yi dam kamar ba jego nake yi ba yanzu kuwa daga dawowar mu sati guda har na fara jin ƙashin wuya na ya bayyana.

Ganin tunanin da tsammanin dawowar Bilal ba zasu kaini ko ina ba ya sa na zura Hijabi na na fita neman yaron da zan aika. Babu kowa a layin kasancewar rana ta take haka ta taka har bakin titi na yo cefane na da kaina. Sai bayan la'asar ya dawo na ringa kallon sa kawai yanda ya shigo babu ko tsinke a hannun sa sai fuska da ya haɗe kamar hadari amma da ya shiga kitchen ya fito sai naga ya ɗan saki fuskar ba kamar sanda ya shigo ba. Sai a lokacin ya ke ce mun wai ya ga missed calls ɗina me ya faru?

Takaici yanda ka san na rufe shi da duka kuma kamar wadda aka kullewa baki na kasa amayar masa da abinda ke cikin zuciya ta. Ban jinjinawa rashin ta idon sa na sai da ya tambaye ni ina abinci, haka na wuce na haɗa na kawo masa ya zauna ya hau ci na ringa kallon sa kawai har sai da ya gaji ya ce mun

"Wai kallon me kike mun haka ne ko so kike yi ki saka na ƙware?"

"Babu komai" na faɗa ina cigaba da kallon sa. Ya bata rai ya cigaba da cin abincin. Wayar sa da ya ajiye akan dining lokacin da zai shiga kitchen ta ɗauki ƙara, ban motsa na har sai da ya ce na miƙo masa ita kafin na tashi. Na ringa kallon sunan da ke yawo akan screen ɗin 'JALILA ABJ'.

A iya sani na Bilal ba shi da wata yar uwa ta kusa ko ta nesa mai irin wannan sunan, amma ko wanda baya son sa in har zai bayar da shaida akan sa kowa ya sani Bilal bashi da kule kulen yammata kuma nima zan shaidi hakan domin wayar sa ko password babu akai tun ina ɗauka na masa bincike ba tare da ya sani ba har na saki zuciya ta na yarda ni kaɗai nake da dashi dan haka ko yanzun abinda na bawa zuciya tabbaci akai shi ne Abokiyar aikin sa ce ba wata Mace daban ba.
[2/26, 11:11 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 29*

Kafin na kai masa wayar ta yanke dan haka da na bashi ajiye ta ya yi ya cigaba da cin abincin ba tare da ya duba wanene ya kira ba. Duk yanda na so na mayar da hankali na kan Al'amin dake ƙananun rigima sai na kasa ƙarshe kawai na goya shi na yi tsaye ina kallon Bilal da ke cin abinci wayar sa na ƙara alamar shigowar wani kiran amma be amsa ba. Kamar me tsoron magana na ce masa
"Ana kiran ka a waya fa" ya ɗago ya kalle ni kafin ya ɗaga wayar ya karata a kunnen sa lokaci ɗaya yana miƙewa tsaye.

"Ranki ya daɗe Hajjaju na" ya furta kalmar da naji ta dirar mun a ƙwaƙwalwa tamkar saukar aradu, ya gota ni ya shige kitchen yana murmushi ko na ce dariya ƙasa ƙasa. Ina nan tsaye kamar mutum mutumi ya fito fuskar nan kamar an masa bushara ya sake wuce ni ya koma kan kujera ua zauna ya cigaba da amsa wayar sa.

Gashi dai ina gurin kuma kallon sa nake yi amma ba zan iya cewa ga abinda yake faɗa ba dukda ba wai a hankali yake wayar ta yanda ba zan ji me yake cewa ɗin ba, Aa, gaba ɗaya kunnuwa nane suka toshe ko kuma ƙwaƙwalwa ta ce ta dena fassara saƙon murya oho, kiran suna na da ya yi da ƙarfi ya maido da ni hayyaci na. Na sauke ajiyar zuciya kafin a hankali na matsa kusa da shi ganin ya miƙo mun wayar sa.

Screen ɗin na fara kallo Jalila ɗin ce dai suke magana kuma har tsayin minti goma kenan minti na goma da yin mutuwar tsaye.
"Ina wuni Maman Al'amin" ta faɗa bayan da na yi sallama cikin muryar da banyi zaton ta ji ni ba. Na amsa da "lafiya lau". Da "Eh, A'a " na ringa amsa mata tambayoyin da ban ma san me take cewa ba har ta gaji ta mun sallama ta kashe wayar ba tare da na maidawa Bilal ba.
"A can head quarter ta ke tare muka yi workshop ɗin da na je da ita, ta damu kullum muka yi waya sai ta tambaye ni ke yau dai kun gaisa na huta" ya faɗa bayan da na miƙa masa wayar.
Chapter 70 · 0% Book details