← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 158

Sashe 109

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na san abinda ya aikata miki dole kiji zafi ba ke ba hatta Hajja dake goyon bayansa a ko da yaushe a wannan karon tana adawa da auren nan dan wlh ba dan mun tausheta ba rantsuwa tayi akan sai ya saki yarinyar ba zata tare ba. Mu muka yi ta bata haƙuri saboda a ganina bai kamata ace a gyara ɓarna da ɓarna ba, ubangiji ya rigada ya ƙaddara matar sa ce sai ayi haƙuri baki ɗaya a karɓi hakan ta yuwu silar auren sai ki ga kina zaune ubangiji ya fitar miki da haƙƙin ki ya wanke ki a idon duk mai ganin laifinki" Anty Amina ta faɗa cikin tausasawa.

Murmushin takaici nayi ina share hawayen da suka ɓalle mun, kowa ɗauka yake saboda Bilal zai ƙara aure ne muka samu saɓani amma nayi mamakin yanda da ta tashi tahowa bikon bai faɗa mata gaskiya ba ta yanda zata fi sanin hanyar da zata bi gurin shawo kaina idan ma hakan mai yuwuwa ne. Ina jin ta ta cigaba da cewa

"Kiyi haƙuri Halima, kishiya da ciwo amma sau tari mace bata sanin matsayin ta a gurin namiji idan tana ita kaɗai sai ranar da ya kawo mata abokiyar zama a lokacin shi kansa zai banbance tsakanin aya da tsakuwa.

Balle Bilal Allah na tuba ni da ke mun san idan ba ke ɗin ba babu wata mace da zata iya jure halinsa suyi dogon zango yanda kikayi,

ni da ace kinyi shawara dani tun farko zan ce miki ki danne zuciyarki ka bashi lokaci kawai ki kuma zuba ido ki sha kallo zakiga zuwan da dawowar amma yanzun ma bata ɓaci ba hakan za'a yi kiyi haƙuri ki koma ɗakin ki tun kafin amarya ta tare balle ta samu lagonki ta fahimci kina kishi da ita".

Girgiza mata kai nayi na ce
"Ko da ina son Bilal ina kuma tsananin kishin sa hakan ba zai saka na bijirewa umarnin ubangiji na so kaina ba.

Ban ce banji zafin ƙarin auren sa ba amma wannan bai ko kama ƙafar abinda ya aikata mun da ya saka na nisance shi ba. Kuma zuwan ki da maganganunki sun sake tabbatar mun da bai yi nadama ba, ba kuma shi ya turo ki ba zuwan kanki ne kawai domin da ace yana buƙatar cigaba da zama dani ba zai rufe miki ainihin abinda ya haɗa mu ba ya faɗa miki ƙarya" na ƙarasa cikin kukan da ya ƙwace mun.

Tayi shiru jiki a sanyaye tana kallona kafin tayi ƙarfin halin cewa
"Menene gaskiyar abinda ya shiga tsakanin ku Halima? Ni dama jiki na ya bani ba gaskiya ya faɗa mun ba, na yarda da shi ne kawai saboda rantsuwar da ya mun ban kuma yi zaton lalacewar ta sa har ta kai ya ringa rantsuwa akan ƙarya ba".

Na miƙe tsaye ina goge fuskata na ce
"Kiyi haƙuri amma ba zan iya furta miki komai ba domin bai zama lallai ki yarda da ni ba ƙarshe ma zaku iya cewa sharri nayi wa ɗan uwanku". Miƙewar itama tayi ta ruƙo hannuna ta ce

"Ashe har yanzu kina kallo na kamar sauran Halima?" Na girgiza mata kai na ce

"Ko da ace kamar su kike kin mun alkhairin da ko me zaki mun zan ɗaga miki ƙafa. Maganar Bilal kuma mu barta kawai kiyi haƙuri, idan zuwan kanki ne ba zan iya sake koma masa ba, Idan ma kuma shi ya aiko ki ki faɗa masa; ko da ƙaddara ta kasance akwai sauran zama a tsakani na da shi ba zan koma ba har sai shi da bakinsa ya faɗa muku abinda ya aikata mun" daga haka na wuce ɗaki na barta a tsaye da alama ta rasa da kalmar da zata tsayar da ni.

Kan gado na faɗa na fashe da kuka bayan shigata ɗaki, Amirah dake shafa mai a gaban mirror ta waigo ta kalle ni ta ce
"Wai Yaya Halima ba zaki dangana ki dena wannan koke koken banzan ba?"

"Ba zan iya ba Amirah, duk yanda na so na bari tunanin dake cunkushe a ƙwaƙwalwata ba zasu barni ba. Ban taɓa zaton Bilal zai mun haka ba na kasa yarda mutumin da na so tamkar raina zai maida mun da irin sakayyar nan" na faɗa cikin kuka har raina kuma na ji wani sanyi na samun wanda zan tattauna yanda nake ji a zuciyata da shi.

Tunda Hansa'u ta fahimci ina shirin yafewa Bilal a faɗar ta shikenan ta fita a sabgata ta dena kirana kuma ko da ni na kirata ba zata amsa ba kamar ma blocking ɗina tayi dan baya bayan nan idan na kira kullum user busy ake ce mun. Mama da Abba kuwa sun zame mun kamar dodanni a yanzu, banda tsawa da hantara ba abinda yake shiga tsakaninmu, Anty Labiba da ta kasance abokiyar shawarata tun asali na ruguza alaƙar mu tunda na kafe akan auren Bilal, ita ɗin kuma bata da sauƙi ta kasa haƙuri ta rungume ni tamkar yanda sauran sukayi kafin yanzu komai ya lalace.

Tasowa tayi ta dawo kusa da ni ta zauna ta ce
"Kin aure shi cikin rashin sanin ainihin wanene shi, a yanzu da komai ya fito miki; idan kika sake biyewa So ba kuskure bane bane abinda zakiyi ganganci ne, kin kuma san duk abinda aka aikata shi bisa ganganci, idan aka samu akasi sakamakon sa ya kan zarce na kuskure.

Ya hanaki abinci kin ɗauke ido, ya zageki kin ɗauke ido, ya doke ki duka kin shanye saboda kina son sa kina kuma son kiyi zaman aure sannan bakya so waɗanda suka ce kar ki aure shi suyi miki dariya shiyasa kika haƙura kika zauna amma Yaya Halima har zuwa wane lokaci zuciyarki zata iya jurewa bayan kin san mijinki yana da wata alaƙa a waje irin wacce take tsakaninku ma'aurata?"

Da firgici haɗi da mamaki na kalleta, ta gyaɗa mun kai cikin tabbatarwa kafin na buɗe baki ta ce
"Kar ma ki ɓata lokaci gurin tambayata a ina na sani, kowa kallonki kawai yakeyi suga iya tsayin lokacin da zaki ɗauka kina rufa masa asiri.

Ba Jalilah sunanta ba? Har gidan da ta siya masa a Kano suke zuwa suna sheƙe ayar su a ciki an sani, mota da kuɗaɗe duk da yake facaka da su zuwa yanzu kowa ya san karuwanci yakeyi tana biyansa.

Ke ce kike ta nuƙu nuƙu da abu a rai yana neman kashe ki a zatonki kin ɓoye sirrinsa bakya so mutunchinsa ya zube bayan shi tuni ya daɗe da barbaɗar da mutunchi hotel hotel a gari, dan haka tun wuri idan ma zaki saki ranki ki saki, idan kin ce zaki koma masa babu mai miki dole ki rabu da shi amma kiwa kanki faɗa tun kafin duniya ta miki.

Kinga test ɗin da kuka je ɗazu? Toh Abba ne ya saka ya kaiki dan ina ji yana gayawa Mama idan kika dage sai kin koma to fa duk abinda ya je ya dawo ki kuka da kanki, waya sani ko an gaya masa yarinyar da yake neman bata da lafiya ne? Ke dai kawai ki godewa Allah bai shafa miki ciwo ba kuma kiyi ta kanki in kuma kin na ce toh sai in ce miki Allah ya bada sa'a".

Yanda kasan wata uwar mata haka Amiran ta zauna tana tsara zance, duk maganganun nata ba wani fahimtarta nayi ba hankali na ya tafi kan cewa da tayi kowa ya san abinda Bilal yake aikatawa. A hankali na ce mata

"Mu'azzam ne ya faɗa muku ko?"

"Babu ruwan Yaya Mu'azzam, ita magana ai kamar tusa take in dai an yita a sannu zata isa ko ina. In miki mai gaba ɗaya, to hatta da cewa da Abba yayi kije ki ɗakko Uniform ɗin ki a gidan jiya yana sane yayi haka ne saboda ki tarar da abinda idan kina da hankali ba zaki ko sake kallon in da Bilal ya gifta ba, amma kika sake gwada masa ke ɗin fa kinyi nisa bakya jin kira.

To wlh tun wuri ki wa kanki faɗa dan Abba ya gama kaiwa bango da lamarinki, Sai kinji yanda ya yiwa yayansa tas tas duk da ya ce shi bai san komai ba.

Ita kuma wannan Anty Aminar raina miki wayau kawai tazo tayi dan na tabbata su dai sun san komai" Amiran ta sake faɗa daga haka ta tashi ta fara saka kayanta tana sake jaddada mun wai in wa kaina faɗa na san inda yake mun ciwo sai kace wata uwata.

Jiki na yayi laƙwas da jin maganarta. Ashe ni duk bonono nake wai rufe ƙofa da ɓarawo, ina nan ina fama da abu a ciki na ashe na bar baya ba zani kowa kallona kawai yakeyi. Yanzu ashe iyaye na sun ma san abinda ni ban sani ashe su har sun san yana kai mata gida kenan.

Kuma mai ciwo na sake fashewa da shi, na rasa gane wace irin ƙaddara ce take yawo da ni haka, ina jin zuciyata tamkar zata fashe saboda ƙunci da baƙin cikin halin da na tsinci Bilal a ciki amma kuma a wani ɓangare babu ko ɗigo na soyayyar sa daya ragu, ji nakeyi ma tamkar ana sake rura mun wutar ƙaunar sa a zuciyata. A fili na furta

"Ko sonka zai zama ajalina na haƙura da kai Bilal in sha Allahu na barka har abadah" na sake faɗawa kan gado na cigaba da kukan da babu abinda yake rage mun saik ƙarin zafin zuciya da yake saka mun. Ina tsaka da kukan Al'amin ya shigo, motsin buɗe ƙofar ya saka na ɗago muna haɗa ido wani sabon kukan tausayinsu ya ɓalle mun. Ganin ina kuka ya saka ya taho da gudu ya faɗa jikina yana cewa

"Mami menene? Momy ta ce baki da lafiya dubaki muka zo yi ko naje na kirata ina ne yake miki ciwo?"

Rungume shi na yi na cigaba da kuka, abinda nake gudu ya rigada ya faru. Bilal ya cuce ni ya cuci yarana ya ɓata musu suna ya kuma bar musu abin gori har duniya ta tashi. Sai da ya fara kukan shima kafin daƙyar na lallashi kaina nayi shiru, ina lallashin sa Anty Labiba ta shigo.
Chapter 109 · 0% Book details