← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 158

Sashe 17

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanda Allah yayi maka bakayi zato ba wata rana shima zeyi masa, a aure nagartar ma'auri ita ce abu ta farko da ake dubawa. Yaron nan bashi da laifi an san shi an san iyayen sa ubansa mutumin kirki ne har ya faɗi ya mutu ban taɓa jin an ce ga wani halin sa mara kyau ba badan ma mutuwa me tonon asiri ba ta yaya za'ayi ace kamar ɗan Alhaji Mansur ya rasa muhallin da ze shiga ya zauna da iyalansa? Kasan sanda ya rasu basu tasa sosai ba yan uwansu suka hau kan komai suka bar musu abin da suka ga dama shi da ƙannen sa da suke ciki ɗaya, yayyen sa na sama uku duk mata ne shi ɗin dai shi ya tashi yake ta fafutuka da nemo abin da ze rufawa uwarsa da yan uwansa asiri yanda ka gan ka ɗin nan hake yake me zumunchi abin sa na yan uwan sa ne har irin wannan Mijin ne za'a ce ba za'a bashi aure ba?

Karka kuskura ka biyewa mutane dan idan abun kuka ya same ka dariya zasu maka idan na farin ciki kuma yazo se sun san yanda suka yi suka ture ko shi Salahun da yake wannan maganar naga Maryam haka ya aurar da ita ba lefen yanzu ka gaya mun duk cikin yayan dangi wa cece take jin daɗi a gidan aure kamarta? Ka ci gaba da addu'a kawai ka barwa Allah komai shi yasan sirrin daya lulluɓe a cikin auran nan dama kuma duk wani abun alkhairi ai baya samuwa ta daɗi mu ci gaba da addu'a kawai tun da dai yarinya tana son sa babu abin da za'a fasa in Allah ya yarda za'a yi komai arziƙin kenan, ubangiji ya hore maka ka kira shi kaji, idan har aikin gidan nasa ba me yawa bane da za'a iya ƙarasa wa a masa in ma kuma baze gamu ba a nemi haya ko ka basu gida su zauna arziƙin kenan amma zancen a fasa aure be taso ba sharrin da za'a bibiye mu dashi kaɗai ma se ka rasa in da zaka tsoma ranka to ina dalili tun da dai Allah be hana yanda za'ayi ba" maganganun da Inna Salamatu ta faɗa masa kenan da suka bar shi cikin kogin tuna ni zuciyar sa ta kasu biyu.
*******************
Se yamma lis na koma gidan Anty Labiba, ko da naje gidan su Hansa'u dama ban gaya mata komai ba data tambaye ni me ya same ni fuskata ta kumbura se kawai nace mata kuka nayi yan uwan Abba ne suka zo yi mun nasihar aure ta ringa tsokana ta daga nan muka ɗan taɓa zancen biki ƙawayen mu nata ƙorafin ba'a gani na naƙi nazo a fara shirye shirye nace mata gobe tazo muyi maganar a gidan Anty Labiba kawai. Ban iya runtsawa ba cikin dare, Bilal be kira ni ba na kira shi kuma wayar sa a kashe ga Abba ma nayi zaton yanda baya son damuwata kafin wucewar yinin ranar ze aiwatar da abinda ya kamata ya share mun hawaye na se dai har dare shiru wannan ya ɗaga mun hankali na ringa tunanin ko dai su Baba Salahu sun zuge shi ne tun da naga alamar daga shi har Baba Hashim ɗin ba son auren suke ba wannan tunanin ya ninka tashin hankali na tsabar damuwa har ji na ringayi numfashi na yana sarƙewa, rabuwa ta da Bilal is the last thing i could ever imagine in my life. Ina son Bilal irin wanda ban san adadin sa ba ba kuma na fatan ace wani abu ya shiga tsaka ni na dashi.

Washe gari da wani irin ciwon kai na farka bana ko iya buɗe ido na da kyau ga ciki na daya ɗauki ciwo shima dan rabo na da abinci tun na safiyar jiya haka na wuni na kwana. Daƙyar na iya fita kitchen ina dafa bango na haɗa shayi, a ƙasan kitchen ɗin na zauna na shanye kafin na jingina jikin bango ma rufe ido na ina jin kaina na bugawa kamar me. Anty Labiba ta shiga, kallo ɗaya ta mun ta wuce yin abin da ya kai ta kitchen ɗin se da ta gama zaryar fitar musu da abin karyawa ganin har sannan ban motsa ba kafin tace mun
"Ki tashi ki mun wanke wanke yau wadda zata miki gyaran jiki zata fara zuwa, kalli yanda kikayi firkai firkai dake a banza zaki kashe kanki saboda wani banza da be san mutunchin ki ba". Se da ta maimaita sau biyu ban amsa ba a fusa ce tayo kaina tasa ƙafa ta haure ni, ina jin duk abun da take faɗa se dai bani da ƙarfin amsa mata a zaunen da nake jiki na ya saki gaba ɗaya duniyar ma juyawa takeyi a ido na. Haurin da ta mun yasa na zame daga bangon dana jingina na sulale a ƙasa ganin haka yasa ta fasa ihu babu shiri daga nan kuma ban sake tuna komai ba kawai na farka na ganni a gadon Asibiti Bilal na zaune a gefe na.

[12/22/2024, 9:09 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 8*
"Sannu Halims, kin tashi" Bilal ya faɗa yana nufo ni se dai shigowar Anty Labiba ɗakin ta katse masa hanzari se ya ja gefe yana shafa kansa ita kuma ta balla masa harara kafin ta nufo ni ta kamani ganin ina ƙoƙarin tashi zaune.
"Sannu" ta faɗa tana gyara mun ɗankwali na daya zame. Bilal ne ya fita ya kira wo likita suka dawo ɗakin tare da Abba. Bin su kawai nakeyi da kallo har likitan ya gama dubani yace babu komai jiki na ya dai dai ta amma a barni na sake hutawa. Abba yayi mana sallama akan ze je wani guri Bilal na rakuɓe a bango kamar wani maraya a idon sa na hango tarin damuwa wadda nasan tana da nasaba da halin da nake ciki se dai wanzuwar Anty Labiba tsakanin mu tasa ya kasa yin motsi me ƙarfi balle yayi mun magana.

Ita ta kai ni toilet da nace mata ina jin fitsari se kawai taci na daure nayi wanka gaba ɗaya ko zan ji daɗin jiki na. Tana cuɗa mun baya na tambaye ta me ya same ni? Kuma tun yaushe nake asibitin? Ta mun banza bata amsa ba har muka gama ta ruƙo ni se kuma ta dakata tace na jira ta fita, ina jiyo muryar ta ta cewa Bilal ya bamu guri, se da ta rufo ƙofa kafin ta dawo ta fito dani cikin kaya na da na gani a ƙaramar jaka na shirya, bana jin ciwon komai ban da kaina da yayi mun nauyi se jiki na da babu ƙwari dan haka a zaune nayi sallolin da Anty Labiban tace sun same ni a kwance. Ina idarwa ta miƙa mun cup data haɗa tea na girgiza mata kai ina cewa
"Bana jin yunwa Anty". Se ta mayar ta ajiye akan drawer ta nemi guri ta zauna tare da ciro wayar ta daga aljihun rigar ta ta shiga dannawa. Kusan minti goma muka yi shiru, so nake yi na tambaye ta ko Bilal ya tafi ne amma yanda ta tsare gida yasa na ji shakkar yi mata magana da dai naji bazan iya jurewa ba se kawai nayi shahada cikin murya ta data ƙara laushi nace
"Anty Bilal ya tafi ne?"
Yanda kasan tana jira na kuwa tayo kai na tana cewa
"Ki kiyaye ni Halima, ni zaki tambaya Bilal ya tafi ko yana nan ajiyar sa kika bani ko yaya akayi?. Badai bakya tausayin kanki ba da kananun shekarun ki zaki jawa kanki ciwo saboda namiji. Se ki zuba ruwa a ƙasa kisha zaki auri Bilal autan maza. Badai namiji kika ɗaukaka har kike neman halaka kanki saboda shi ba Halima? Allah ya bada sa'a" se ta miƙe fuuu tayi waje tana ci gaba da maganganu.

Da kallo na rakata har ta fice ina jin babu daɗi a raina. Na rasa wace irin ƙiyayya Anty Labiba take yiwa Bilal. Ban san me ya tsare mata da bata iya ɓoye tsanar da tayi masa a zahiri ba.

A can waje kuwa cike da damuwa Bilal yake zauna, yana so ya koma cikin ɗakin yaga halin da Halima take ciki amma rashin ganin fuska a gurin Anty Labiba yasa yake zaune a gurin. Da daren jiya Mu'azzam ya kira shi ya sanar masa da Halima bata da lafiya an kwantar da ita a asibiti a yanda yace tana ta kiran sunan sa ne shine Abban su yace a kira shi yazo. Sanda yaje ɗin ya tarar da ita anyi mata allurar bacci a hirar su ya tsinci wani abu a dalilin rashin lafiyar tata. Duk se yaji ya tsani kansa, yasan Halima tana son sa shima kuma yana son ta amma kuma ya rasa yanda ze yi dole ya fito ya gaya mata gaskiya. Be yi zaton zata saka abun haka a ranta har ya kwantar da ita ba se dai da ya ci gaba da jan ta yana ɓoye mata har se an kai gaɓar da gaskiya zata fito da kanta a ganin sa gara ta sani su taru su nemawa kansu mafita.
Chapter 17 · 0% Book details