← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 158

Sashe 154

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka ya shafe sati biyu a kurkuku cikin yanayin da shi kaɗai zai iya fasaltawa. Sai ya kwana ya yini bai saka komai a cikinsa ba dan hatta da ruwan gurin baya iya sha. Shopping sosai Zulaiha tayi masa harda miya da soyayyen nama ta kai masa amma yana shiga ciki wasu suka ƙwace bai kuma iya yin ko tari ba domin fuskokinsu kaɗai daya kalla ya san babu abinda suke jin tsoro, zasu iya yi masa komai tunda dama ba barin gidan zasuyi ba da yawansu ɗaurin rai da rai aka yi musu. Haka ya shafe kwanakin cikin wahala da ciwo, ga zazzaɓi ga damuwa da tashin hankali kafin cikar lokacin idan ka ganshi sai ka ɗauka shekara goma yayi ba wai sati biyu ba.

Yayi baƙiƙƙirin, tunda yaje sau uku yayi wanka shima ba soso ba sabulu haka kayan jikinsa sai da wani da suke cell ɗaya ya taimaka ya wanke masa. Abu ne ya haɗu da mai son jiki wanda bai saba da wahala ba shiyasa abin ya masa yawa, yan uwansa babu wanda bai zubar da hawaye ba lokacin da aka kawoshi za'a shiga dashi kotun.

Hajja data dage sai an je da ita haka ta kware baki ta fashe da kuka tana cewa
"Sai kace wanda yayi kisan kai kalli yanda suka mayar mun dashi?"

"Koma menene shi ya janyowa kan sa ai Hajja, kuma babu wanda ya masa komai, Abubakar ya ce baya cin abinci baya wanka ai dole ki ga ya zama haka. Kawai kici gaba da addu'a Allah yasa shari'ar ta zo a yanda muke fata kawai" Anty Ladidi ta faɗa mata.

Sai da akayi Shari'a biyu kafin aka zo tasu, bayan maganganu daga kowanne ɓangare, Lawyer Alhaji Lawan ya tabbatarwa da kotu an mayarwa da Client ɗinsa kuɗaɗen daya bayar na siyan gida ciff ba tareda ko naira biyar tayi ciwon kai ba. Shima lawyer Jalilah ya faɗi an mayar musu da wani kaso na daga jumullar kuɗin kayan da aka ɗiba, kuma client ɗinsa ta amince da roƙon da yan uwan wanda ake ƙara sukayi na cewa za'a ringa biyanta kuɗin a hankali har a warware. Abinda yayi saura tsakaninsa da kotu ne domin jin matsayin laifukan daya aikata a matakin dokar ƙasa.

Alƙali Yakubu Bechi daya gama sauraron jawabi daga bakin lawyoyi yayi rubuce rubuce kafin ya fara karanto hukunci kamar haka.
"Bayan sauraron kowanne ɓangare, an gabatar da hujjoji masu ƙarfi da suka tabbatar da cewa Bilal Saleh ya fasa store da Jalilah Muhammad ta ajiye kaya in da ya ɗebi kayan da kuɗinsu ya kai kimanin naira miliyan talatin (₦30,000,000)."

A firgice Bilal ya ɗaga kai ya kalli inda Jalilah take zaune, ta kuwa sakar masa murmushi harda kashe masa ido ɗaya. A ina ya ɗebi kayan miliyan talatin? Amma ya zaiyi? Bai isa ya musa ba ko na miliyan dubu tace ya ɗiba haka nan zai amsa tunda shi ya jawa kansa.

Mayar da kai yayi ya cigaba da sauraron Alƙali dake cewa
"An samu shaidar hoto mai motsi daga CCTV camera da kuma shaidu na gani da ido wanda suka ga lokacin da aka fita da kayan.
Haka kuma, an tabbatar da cewa ka damfari Alhaji Lawan Isiyaku in da ka siyar masa da gidan da Jalilah Muhammad ta baka kake kula mata dashi bayan ka gabatar da bogi, ka karɓi naira miliyan hamsin da biyar (₦55,000,000)".

Alƙali Yakubu yaja fasali kafin ya ci gaba da cewa
"Duk da haka, kotu ta lura da wasu abubuwa masu muhimmanci:
Ka amsa laifinka tun farko ba tare da wasa da hankalin kotu ba. Sannan kotu ta samu tabbaci da shaidar mayarwa da Alhaji Lawan kuɗinsa da kuma wani ɓangare na kuɗin kayan Jalilah Muhammad bayan kotu ta fara sauraren shari’ar.

Sannan, a zamanka a kurkuku ka nuna cikakkiyar nadama da bayyanannen yunkurin gyara ta hanyar ayyukanka waɗanda ma'aikata suke lura da shi.
Wannan kotu ba ta tsaya kan hukunci ba kawai, tana kuma la'akari da gyara da dama haɗi da niyyar shiriyar wanda ya aikata laifi. Saboda haka, kotu ta yanke hukunci kamar haka:

1-A kan laifin fasa store da sata, kotu ta yanke maka hukuncin shekara biyar (5) a gidan gyaran hali, amma za a dakatar da aiwatar da hukuncin zuwa nan gaba idan aka sake samunka da aikata wani laifin (suspended sentence) a tsawon shekara biyu.

2-A kan laifin damfara, kotu ta yanke maka hukuncin shekara bakwai (7), sai dai saboda ka mayar da kuɗin da kuma nadamar da ka nuna, kotu ta sauya hukuncin zuwa shekara uku (3) ko kuma tarar naira miliyan goma a matsayin diyya ga wanda aka damfara, sannan da aikin taimakon al'umma (community service) na tsayin shekara ɗaya a ƙarƙashin kulawar hukumar gyaran hali. Sannan ba zaka tsaya takarar siyasa ko samun wani promotion na aiki ba a tsakanin shekaru biyar masu zuwa.

3-Zaka biya gomnati tarar naira miliyan 5 diyya ga gwamnati a matsayin horo da kuma darasi akan laifukan daka aikata. Karya ɗaya daga cikin Sharuɗa ko saɓawa doka yana nufin kotu zata dawo da cikakken hukunci haɗi da ƙari a kai.Ina fatan hakan ya zame maka darasi a rayuwarka da sauran masu aikata laifuka irin naka." Daga haka ya buga guduma wacce take nuna tabbatuwar kammala hukunci.

Bilal dake jingine da katakon box ɗin da yake ciki ya ɗago idanuwansa cike da hawaye, tsananin nauyi da kunyar da yakeji ta saka ya kasa ɗaga ido ya kalli ɓangaren da masu sauraron Shari'a suke. Yana jin nauyin idanuwa akansa amma bashi da ƙarfin guiwar da zai iya haɗa ido da kowa a yanzu. A hankali ya zame a gurin, ya fashe da kukan da bai shirya yin sa ba.
Bai san inda aka shiga aka fita har aka nema masa yanci, sau ɗaya lawyer da aka ɗaukar masa yaje gurinsa a prison shima basu wani yi magana mai tsayi ba ƙorafi yayi masa akan amsa laifinsa da yayi a kotu bayan ya tsara masa duk abinda zai faɗa idan anje.

Abubakar da Nasir ne a duk sanda sukaje suke bashi tabbacin ya kwantar da hankalinsa Insha Allahu komai zai dai-daita. Koma dai mai akayi ya godewa Allah ya kuma godewa ɗanuwansa da Amininsa Nasir da basu dubi halinsa sun wofantar dashi ba.

Kamar an ce ya sake ɗaga kansa karaf suka haɗa ido da Halima dake zaune a row ɗin dake kusa da ƙofa. Ji yayi gabansa ya faɗi, tayi masa wani irin kwarjini, kallon da takeyi masa daya fassara na baƙin ciki da jin kunyar abinda ya aikata. Kasa daina kallonta yayi kamar yanda itama take kallonsa kafin ta miƙe a hankali ta fice daga ɗakin kotun wani wanda bai san ko wanene ba da sai lokacin ya lura dashi ya bi bayanta riƙe da jakarta data bari akan table.

Sam bai ji maganar da ɗansandan dake kusa dashi yakeyi masa ba sai da Barr Sajid ya ƙaraso gurin yana murmushi da yi masa barka. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yana amsawa dukda hankalinsa gaba ɗaya yana kan Halima da tunaninsa ya tafi akan sanin wanene wancan daya bi bayanta?

A wajen kotun bayan murna da jaje daga yan uwa, Hajja dake riƙe da hannunsa kamar wani zai ƙwaceshi ta kalli Barr Sajid da yace zasu tafi da Bilal ɗin a ƙarasa cike takardu. Kamar zata fashe da wani kukan tace
"Ɗannan ba an sallame shi ba?"
"An sallame shi Hajiya, amma dole sai munje anyi cike-ciken takardu tukunna. Ganin harda Abubakar suka tafi ya saka hankalinta ya ɗan kwanta suka wuce gida tareda su Anty Amina da sauran yan uwa da suka halarci zaman kotun.

Dab da magriba su Bilal suka isa gidan Hajja a motar Nasir shi da Nasir ɗin sai Abubakar. Yanda yake jin jikinsa tamkar wanda aka haƙo daga rami ya so ace kai tsaye gida suka fara kai shi yayi wanka tukunna ko Asibiti ma dan shi kaɗai ya san abinda yake ji amma dai yayi shiru har suka isa gidan Hajjan. Nasir ya musu sallama da addu'ar Allah ya ƙara kiyayewa. Abubakar na kallon Bilal ya ce

"Yaya Nasir yayi maka ƙoƙari, duk tarin abokananka shi kaɗai ya tsaya da jikinsa da aljihunsa har Allah ya ƙwatoka. Ka gode masa kuma kada kayi wasa da abotarku dan shi ɗin mai sonka tsakani da Allah ne"

"Haba Abubakar ai babu zancen godiya tsakaninmu duk abinda nayi saboda Allah ne ba dan a gode mun ko wani abu ba. Ni dai fatana ya kiyaye Allah kuma ya sake tsare mu baki ɗaya" Nasir ya faɗa daga haka yaja motarsa ya wuce su kuma suka shige ciki ganin unguwa da yara sun fara taruwa suna kallonsu.

Falon Hajjan cike da yayanta da yan uwanta da suke jiran dawowarsu, gida ya sakw cika da murna da kuma jaje. A ƙofar ɗakin da Abubakar yake ya hangi Zulaiha tsaye yana masa murmushi, bai ganta ɗazu a kotu ba, ko kuma bai lura bane oho haka dai suka shige falon Hajja bayan ya ɗaga mata hannu. Abubakar ne yace yaje ya huta suma matan kowa ta wuce gidanta haka kuma abun ya isa.

A tsakar gida ya kalli Abubakar ya ce
"Ka samo mana Adaidaita na gaji wlh kamar zan faɗi nakeji"

"Ga ruwa can ai naga ta kai maka ka samu kayi wanka bari naje na samo maka abu mai ɗan ruwa ko yoghurt ne, ga magungunan da Yaya Nasir ya taho maka dasu yace idan kasha zaka samu sauƙin ciwon jikin kafin safiya sai muje Asibiti" Abubakar ya bashi amsa yana nuna masa Zulaiha dake tsaye ƙofar banɗakin tsakar gida, ya kalleta ya kalli Abubakar ɗin, bai dai yi magana ba ya wuce ɗakin da ta shiga zuciyarsa cike da tambayoyi.
Chapter 154 · 0% Book details