← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 158

Sashe 108

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dagaske kenan dama saboda zaiyi aure tayo yaji ashe?" Mama Fauziyya ta faɗa, Mama ta girgiza kai Anty Labiba kuma ta ce
"Ita ta sani, idan ma dan hakan ne dai ba abinda ya canza tunda gashi yayi auren sa in da kuma yana sonta yana son zama da ita ko bai fasa aurenba ba zai mata wannan wulaƙancin ba. To ba ji take ba balle ka ɓata lokacin ka ka mata magana ni shiyasa na sallamata bana iya kayan takaici ba".

Maganar suka cigaba da tattaunawa, na samu na gyara kwanciya cikin dabara na basu baya dan in samu damar yin kuka dakyau, ita bata san abinda ke damuna ya zarce maganar auren Bilal ba wannan ai tsohon zance ne tuntuni na samu labari. Sai da aka kira la'asar suka fita duk su ukun kafin na tashi zaune sosai na fashe da kuka harda shassheƙa.

Ina tsaka da kukan wata Nurse ta shigo dubani, babbace dan ta haifeni ai kuwa ta rufeni da faɗa yanda kasan zata dokeni tana cewa wai ni muguwa ce bani da imani na san a halin da iyayena suka kawoni kuwa shine zan tashi na cigaba da kuka saboda na ƙara tayar musu da hankali?

A daren aka bani sallama Dr ya ce ba abinda zasu mun kawai na koma gida na cigaba da shan magunguna na. Sai na ringaji na kamar marainiya wacce bata da sauran gata da muka koma gida a falo aka barni kamar baƙuwa kowa ya kama sabgarsa saida na gaji da zama dan kaina na lallaɓa na shige ɗaki na kwanta na shiga tunani.

Idan wacce Bilal ya aura yar unguwar su Anty Labiba ce kenan tana nufin gidan da ya kaini nayi musu gaisuwa; in kuwa haka ne ba Jalilah da na tarar a ɗaki na ya aura ba, wancan mugun abunda na gani suna aikatawa a waya ne ya cigaba har ta kai ya ɗakkota ya kawota gida shi tafiyata yanci ya samu mai lasisi na kawo mata.

Na haɗa kai da guiwa ina hawayen tausayin kaina. Sam ba wannan ne Bilal ɗin da na faɗa soyayyar sa ba, Bilal ɗina ba haka yake ba. Amma wai a yaushe ya canza Ina tareda shi ban taɓa fahimtar komai ba? Ya akayi na bari soyayya ta rufe mun ido har na kasa fahimtar canzawarsa ina zaune da manemin mata amma yardar da nayi dashi ko da wasa ban taɓa hasaso zai kasance haka ba.

Tabbas Bilal ya cuceni kuma ya yaudareni sannan ya ci amanar ƙauna. Wlh da ace Zulaihan ita ce na kama shi yana chat da ita ba Jalilah ba zan iya yafe masa ko dan aurenta da yayi zai shafe komai amma ƙazantar tayi yawa, Allah kaɗai ya san bayan ita mata nawa yake mu'amala da su ko ita Zulaihan ma ta sani ko kuma itama ninketa yayi yanda ya mun? Allah kaɗai ya sani.

Haka na kwana cikin alhini, tausayin kaina da yayana musamman Sharifa ya cika mun zuciya. Da naga kuka da tunani ba zasu kawo mun mafita ba sai na miƙe na ɗauro alwala na shiga jera nafiloli na mayar da hankali akan addu'ar kar Allah ya kama ni ko yayana akan laifin Bilal.

Allah shaida ban rage shi da komai da har zai fita ya nema a waje ba idan ma ban ishe shi ba bai taɓa faɗa mun ba na san Allah ba zai kamani da laifin haka ba.

Kafin wayewar gari na sake zugewa sai k ɗauka kwana nayi ina zawo tsabar yanda na zabge lokaci ɗaya.

Da Asuba bayan na idar da sallah ina zaune ina lazumi Mu'azzam ya shigo ɗakin, sai da gabana ya faɗi na ringa kallonsa har ya zaune gefen gado shima yana kallo na ya ce

"Abba ya tambayeni mai ya sameki bayan mun fita" cikin firgici na ce
"Sai ka ce masa me? Amma baka faɗa masa ba ko?"

Ya taɓe baki ya ce
"Ban faɗa masa ba, na ce masa ne zaki faɗa masa da kanki saboda kin san ni ban iya ƙarya ba idan na buɗe baki zan gaya masa gaskiya be kawai".

Tashin hankali na ya nunku ban san sanda na fashe da kuka ba na ce
"Amma baka kyauta mun ba akan me zaka haɗa ni da shi? Ba sai kawai ka ce masa babu komai ba kawai jini na ne yayi ƙasa?"

"Ke idan ya kiraki sai ki gaya masa" ya faɗa kafin ya sake cewa
"Ni ba wannan nw ya kawo ni yanzu ba, an jima ki shirya zamuje asibiti ayi miki test".

Ban kalle shi ba na ce
"Test ɗin me bayan likitan ya ce ba abinda zasu mun?"

"HIV test da na sauran STDs". Yanda kasan kiɗan mandiri haka zuciyata tayi wani diri, na kafe shi da ido, tsabar yanda abun ya dakeni na kasa cewa komai daƙyar na haɗa kalmomi na ce

"HIV kuma?"
"Eh, kin san sai ba'a raba yan bariki da ita dan haka tun da wuri gara a miki gwaji ki san makomarki" yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin.

Ji na ringayi kamar na hau rollercoaster, daƙyar na lallaɓa na koma kan gado na rufa da bargo saboda wani sanyi da naji yana shigata kamar zazzaɓi zai rufeni. Na ringa nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a zuci har ta fito fili, tsoro mai tsanani ya lulluɓe ni.

Duk tunanin da ya taho mun sai in kore shi na idan ta kasance aka mun test ya zama positive ya zanyi? Ban iya cin komai ba har ƙarfe goma ina kwance a ɗakin kafin Amirah da suka gama Exams jiya ta shigo ta ce wai Mu'azzam yana jirana. Haka na fita yanda kasan zautacciya, fuska jeme jeme baki a bushe Kai ba iya bakina ba komai na jikina ma ya bushe kamar wata tsohuwa haka na dawo a dare ɗaya.

Babu wanda ya tambayi ina zamuje muka kama hanya muka fita, can wani babban lab muka je, ikon Allah ne kawai ya kaini har aka gama running test ɗin result ya fito ban mutu a gurin ba saboda tsoro. A gurin ya buɗe ya gama dubawa kafin ya miƙo mun takardar ban karɓa ba na girgiza masa kai daƙyar na ce

"Akwai ko babu?"
"Babu" ya bani amsa, sai na ji kamar an kwarara mun ruwan ƙanƙara tun daga tsakiyar kaina har tafin ƙafata. Na ringa jera ajiyar zuciya tamkar jaririn da ya wuni ba tareda mahaifiyar sa ba, a hanya muna tafe babu mai cewa kowa komai sai da muka kusa isa gida ba tareda ya kalleni ba ya ce

"Wannan ba shi yake nufin shima bashi da wani ciwo ba, ta yuwu baki da haƙƙin sa shiyasa Allah ya tsare bai shafa miki ba dan haka ruwanki ki godewa Allah ruwanki ki butulce masa zaɓi ya rage naki yanzu.

Baƙuwar motar da na gani ya saka na fahimci anyi baƙi, bani da tabbacin gurin Abba aka zo tunda yana gida ko gurin Mama koma su waye bana buƙatar haɗuwa da su dan haka na shiga ta ƙofar kitchen na shige ɗaki ba tareda na bi ta falon ba. Wanka na farayi na ɗauro alwala na fito ina ji na kamar iska zata kwashe ni saboda rashin nauyi. Ina zama Amirah ta shigo wai na zo nayi baƙi,

"Ban santa ba" ta bani amsa bayan da na tambaye ta su waye baƙin? Suhaila ce ta zo mun, na ɓata rai a zuciyata ina cewa zuwan da mijinta yayi bai isa ba shine ya sake turota?

Ban fita ba bayan na shirya kwanciyata nayi sai da Zainab ta sake zuwa ta kirani kafin na yafa ƙaramin mayafin abayar da na saka na fita, ba yabo ba fallasa na ƙarasa na zauna a ƙasa na shiga gaisheta, ta amsa a sanyaye tana ƙare mun kallo, na sace kallon Mama dake danna wayarta kafin na mayar da kaina ƙasa ina juya zoben hannuna.

"Ashe kuma abinda ya faru kenan Halima? Dan Allah kuyi haƙuri, wlh ban sani ba sai da aka daɗe tukunna nauyi da kunya kuma suka hana in zo ko na kiraki saboda na san duk dalilin da zai saka ki baro ɗakinki ba ƙarami bane duba da tarin ƙaunar da kikewa Bilal.

Na yiwa Mamanku duk bayanin da yayi mun, na san bai zama lallai abinda ya faɗa mun gaskiya bane amma koma menene tone tone bashi da daɗi ayi haƙuri har idan da yuwuwar komawa kiyi haƙuri ki koma, amma idan kinga cewa da cutuwa a lamarin zamanku wlh bana goyon bayan kici gaba da haƙuri kiyi abinda kike ganin ya fi kwanta miki a zuciya" Anty Aminan ta faɗa.

Mama na sake kallo naga ta taɓe baki kafin ta miƙe ta bamu guri. Nayi shiru sai Anty Aminan ta sake cewa
"Na san kina haƙuri da shi harma da mu da mahaifiyarmu baki ɗaya amma ki sani Halima babu wani gidan aure da bashi da nasa kalar ƙalubalen kawai na wani ne ya fi wani da kuma yanda ma'auratan suka iya riƙe sirrin su shine banbanci amma duk inda aka zaga hakan take shiyasa zakiji hausawa suna cewa da sabon gini gara yaɓe".

Kai na girgiza hawaye ya kawo ido na na ce
"Bana zaton zan iya zake zaman aure da Bilal dukda ina son sa".

Kuji tsoron Allah masu fitar mun da littafi babu lallai na yafe haƙƙina wlh
[5/9, 4:36 PM] Zainab Madawaki Dahiru: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 46*

"Kar kice haka mana Halima. Ke da na san ki jaruma shine zaki bari daga sama wata ta zo ta ƙwace miki miji kuma ki sakar mata? Haba mana dan Allah karki bani kunya.
Chapter 108 · 0% Book details